10 Years Challenge

#10YearChallenge

Maimakon sanya hoto biyu don bayyana yaya tsufa ta kama ka between (2009-2019) ina ganin zai fi wa mutum alhfanu ya tsaya yai karatun ta natsu.

Wane irin aiki ka yi cikin wadannan shekarun wanda zai amfani rayuwa da addininka da makomarka?

Wace irin alaqa ka kulla da Allah Ubangijinka?

Mece ce dangantakar ka da Al-Qur'ani da sunnar maaiki (SAW)?

Shin hankalinka da tunaninka da dattakunka karuwa suke ko raguwa?

Wane matakin ilimi ka taka tun daga lokacin zuwa yau?

Ko kana tunawa da mutanen da suka mutu a wadannan shekarun ballantana kai musu addua?

Wadanne laifuka da zunubai ne kai ta aikatawa a wadannan shekarun?

Me ka shirya wa mutuwa?

Wane irin tanadi kake yin don lahira?

Wace irin turba ka daura iyalenka?

Wace irin nadama kake yi akan asarar lokutan da ka yi cikin shekarun?

Allah mun tuba ka yaye mu.

Allah ka sa mu cika da imani
Post a Comment (0)