YANA DAGA ZALUNCI MIJI AKAN MATARSA

YANA DAGA ZALUNCI MIJI AKAN MATARSA


1-Dayawan mutane a kasar hausa suna qin wadata iyalan su da abunci alhalin kuma yana dashi.

*_Hakan din haramunne annabi s.a.w yahana yakuma nunawa mata sa iya diban kayan abuncin a bayan idon maigida gwargwadon yadda zai isheki batare da almubazzaranciba ko ha inci_*
@Bukhari da Muslim 

2-Fita waje aci abunci me tsada da dandano me dadi alhalin abuncin gidansan yakasa gyarawa,wani shikadai inyatafi yakan kashe 500 a iya lokaci daya amma a gidansa kuwa baifi yabada 200 in anyi badadi yakici,itakuwa mace dole taci kar yunwa ta halakata yayantama haka zasuci wani har da ma haifiyarsa haka za aci .

*_Amma shikuwa yafi wata guda baici abuncin dare nagidan sa kullun yana teburin me indomi da da kwai, wanikuma zaici abuncin matartasa kadan daganan inyafita sai teburin me shayi anan zai cika kundunsa da me dadi."_*

*3-RASHIN YIWA MACE SUTTURA A KAI AKAI*

ALHALIN YANA SAMU kuma shi yana dinkawa kansa amma matarkuwa da salla sai sallah ko intahaihu.

*4 BARIN DAWAINIYAR YA MACE AHANUN MAHAIFIYARTA KAMAR SAYAMATA KAYAN KWALLIYA DA SUTTURA TA YAYI Koda yana da yadda zai'. 

5-fifita lafiyarsa akan ta matarsa kamar gazawarsa wajen sai mata magani,kin barinta awu ko kin tallafamata akan awun ,kinkaita asibiti dawuri.

DADAI SHAURAN MATSALOLIN WASU MAGIDANTAN


_*🕌SAUTUS SUNNAH*_
Post a Comment (0)