UKU-BALA'I 37

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA BAKWAI.


A hankali take taka benan har ta isa bakin kofar tana jin yarda gabanta ke dokawa ba ta san ya zai kalleta ba bata san ya zai karbeta ba ita dai ta san tana son sa so mai tsanani wanda tun da take a filin duniyarta bata taba jin son wani É—a namiji ba kamar Dr.Erena zuciyarta da ruhinta sun jima suna kai kawo akan son shi ta dalilin son sa ta zo aiki cikin Company sa saboda burinta ya cika take zaman aiki a company ba wai saboda kudi ba amma ta rasa ya zatayi ta rasa mai ya dace tayi a gareshi domin ya amince da ita har ya so ta sosai ta lura sam! baya kula duk yanayin da take nunawa don ya sota amma hakan sam ba ya wani tasiri akansa ba ta san ya za tayi ba abin da ya ke kara tayar mata da hankali yarda lokaci guda wata ta shigo cikin Company din take kokarin bata mata duk wani shirinta ta lura Dr.Erena son ta yake yi so kuwa mai tsanani abin da ta lura dashi ita Areefa ba son sa take yi ba shi yake kiÉ—in sa yana rawar sa ga inda ake son sa amma ya kwashi jiki ya tafi in da ba a son sa.
Ita dama tun da Areefa ta shigo cikin Company nan gabadaya taji bata kwanta mata ba sosai take ji a ranta akwai abin da zai faru don ta lura ita ma Areefa ba wai aiki ne kawai ya kawo mata ba har da wani KUDIRI nata na daban.
Tsaki taja kadan kafin ta gyara zaman rolling din da tayi wa dan kwallin jallabiyar dake jikinta sosai ta gyara zaman glass din dake fuskarta kallo daya kayi mata ka san ita ma ba baya b wajan kyau da kirar jiki fara ce amma ba can sosai ba.
A hankali ta turo kofar Office din ta shiga zuciyarta na bugaawa da halin tsoro don bata san abin da zai je ya dawo ba bata san yarda Dr.Erena zai karbeta ba ta san ya zai anshi abin da za taje masa dashi ba.
"...Bobby karka sake ka bata min rai kayi kawai abin da nace da kai ba wai ka kai shi can in da ba a dawowa ba a,a kawai so nake yi yaji a jikinsa ya san har yanzu Dr.Erena yana nan a yarda ya sanshi ba wai canzawa yayi ba".
Tana kokarin buÉ—e baki tayi sallama ta tsinkayi muryar Dr.Erena ya na fadin haka ai mutuwar tsaye tayi idanuwanta a warwaje lokaci guda jikinta ya shiga É“ari kamar wacce akayi wa wankan ruwa mai tsanani sanyi gumi ya shiga tsantsafo mata a jiki lokaci guda duk taji jikinta ya shiga narkewa da duk wani kudiri da buri da ta zo don cimmawa a hankali ta shiga jan numfashi tana mamakin kalaman Dr.Erena bata taba zaton haka yake ba bata taba zaton akwai rashin imani har haka ba a ransa.
A hankali ta shiga kokarin juyawa don ficewa amma zuciyarta tana hanata akan kudirin da ta zo dashi sosai taji komai ya fara canzawa tsoro da fargabar da take yi ya ragu sosai zuciyarta na kara mata jarumta akan kawai taje ai mai nema ba ya rasawa ita fa abin da ta zo yi daban maganar da yake yi bai shafe ta ba kuma ba ta san abin da yasa yace haka ba.
Da wannan tunanin ta shiga saita kanta gabanta na faduwa kadan kadan.
Sallama tayi tana mai cusa kanta cikin Office din tsaye ta hangeshi yana kai kawo fuskarsa da murmushi wanda daka kallashi zaka gane na mugunta juyowa yayi jin sallamar da kayi dubanta yake yi cikin wani irin yanayi kafin ya kau da kan sa.
"Sannu Sir".
Ta fadi da kokarin dauko jarumta ta azawa kanta ansawa yayi a ciki kafin ya dube ta ba yabo ba falla sa.
"Lafiya me ke faruwa ne Mufeeda?".
Sosai taga yayi mata kwarjini a idanunta gabanta taji yana bugawa wata irin burgewa take jin lokaci guda tana karuwa akan Dr.Erena juya idanunta ta shiga yi tana faman yak'e kamar wacce bata da gaskiya.
Dubanta ya shiga yi da wani irin yanayi na tuhuma kafi ya tako inda take tsaye.
"Akwai wani abu ne?".
Ya fadi yana kureta da kallo da ya kusan narkar mata zuciya da gangar jiki. A hankali ta shiga motsa baki zuciyarta na tsallen tsoro akan yarda zai anshi lamarin.
"Sir, dama akan maganar Areefa ce".
Dan yatsine fuska yayi kafun yace.
"Me ya faru da Areefa din wani abu tayi miki ne?".
Girgiza kai tayi kafun ta ja numfashi mai tauri tana jin yarda wani abu da ya tokare mata kirjiya ya sauka.
"Gaskiya Sir. Ban yarda da ita ba jikina sam! Bai kwanta da ita ba tun da ta zo Company din nan sosai nake ji ajiki kamar ba alheri bace a gareka da ma mu kafatanin ma'aikatanka...".
Hautsine wa fuskarsa ta shiga yi da wani irin bacin rai idanuwansa suka shiga kaÉ—awa da tsananin haushi kafin ya dube ta sosai da sosai yana faman hirji kamar wani kumurci.
"Me kike cewa Mufeeda Areefa din ce ba alheri ba Areefa ce kike jifa da wadannan kalaman naki kina da hankali kuwa anya ba wani abu kika sha ba wanda ya rabaki da duniyar hankali gaskiya bana zaton kina cikin hayyacinki na lura ke ma kin fara yan kurɓe-kurɓen nan na yan matan wannan zamani in ba haka ba ina ruwan ki da ita mai ya shafe ki da ita rayuwarki daban ta ta daban don haka tun wuri tun muna kallo juna a mutunce ki fice mani daga Office tun kafin na keta miki rashin mutunci.".
"Am...amma Sir. Daka tsaya ka fuskance ni gaskiya ce fa nake sanar da kai...".
Wani kallo ya watsa mata kafun ya shiga nuna ta da hannu.
"I Say Get Out! tun kafin nayi miki abin da baki taba zato ba".
ware idanu tayi sosai jin furucinsa ya taba mata zuciya amma sai taki barin haka yayi tasiri a zahirancen cikin jarumta ta sake dubansa murya alankwashe.
"Sosai na fuskat kamar akwai wata alaka a tsakanin kai da ita Sir hakan kuma bai dace ba sam ya kamata ace ka nemi mace mai daraja mutunci a matsayinka na mutum mai daraja da mutunci mutane da yawa yanzu kallon wani daban suke yi kamata ganin alakarka da Areefa...".
"Mufeeda! Which can of nonsense kike kokarin gaya mini me kike nufi dani me kike so ki ce da nine akan Areefa ya kamata tun wuri ki gyara kalaman ki kuma ki sani indai akan Areefa ce kika zo kina yi mani wannan haukar wallahi tallahi gaf! kike da barin Company din nan".
Gwalo idanu tayi waje sosai zuciyarta na wani irin raÉ—aÉ—i da zafi komai take ji na jikinta yana canzawa sosai take jin komai nata kamar ba nata ba kalaman Dr.Erena ba karamin taba mata zuciya sukayi ba ji take kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu bata san ya zatayi ba bata san me zatayi Dr.Erena ya kalle ta a mutunce ba bata san hanyar da za ta bi ba domin ya kulata ya anshi tayin da take masa ya sota kamar yarda ta kamu da son sa a filin duniyar zuciyarta sosai take son sa so bana wasa ba tana kishinsa ba ta son duk wata mace ta ga tana kusantarsa sosai tashiga tashin hankali lokacin da ta ga Areefa ta fado rayuwarsa.
Wasu kwalla taji suna neman zuba mata da sauri ta dauke su ba tare da Dr.Erena ya gani ba amma sai dai tayi shuka a idon makwarwa domin kuwa duk motsinta akan idonsa take yi da mamaki yake dubanta sosai hawaye da ta shafe ya kara sanya shi a mamaki sosai sakanni ya dauka yana kallonta kafun ya ce da ita cikin muryar tuhuma.
"Hawaye Kuma me yayi zafi shi ba wuta ba Mufeeda me yake damun ki wani abu akayi miki ne Pleaae Leave my Office ba zan dauki wannan haukar taki ba kin ji ko I need to be alone ba na son abin da zai kawo mani ciwon kai don ba dauka zan yi ba".
Murmushi tayi wanda ya fi kuka ciwo sosai take jin bakin ciki da takaici na rashin darajawa da Dr.Erena yake nunawa akanta sosai take ganin rawar kanta da gangacin da zuciya tayi mata na son wani wanda bai son tana yi ba ga ta yanzu a gaban shi amma yana nuna ita da banza duk daya bata san mai ya sa haka ba ta san dai SONE SILA wanda bai yi mata adalci ba bai dace ace yayi mata haka ba bai kamata ace AKAN SO tana kuka ba kukan ma akan wanda ba tayi tsammanin zuciyart za ta so shi ba ko a mafarkin ta ba ta taba zaton zuciyarta zata dauko mata son Dr.Erena ba ta kawo mata tun da ta fara aiki a Company tun ranar da ta daura idanuwanta akan sa taji ta kamu da son sa amma bata san ta yaya zata bayyanar son da take masa ba a gareshi domin sosai da sosai yake mata girma da kwarjini a idanunta.
Ba ta zaton za ta iya barin nan batare da ta amayar masa da abin da take ji game dashi ba bata zaton zata iya daukar gangar jikinta ta fice daga cikin Office din nan batare da ta bayyana son da take masa ba ko da kuwa hakan zai sanya ya kore ta daga Company din nan. Ba za ta iya cigaba da dakon son sa ba tana bukata zuciyarta ta sarara mata da tashin hankali da take samun kanta kullum a ciki runtse idanuwanta tayi kirjinta cike fargaba da tashin hankali mara musaltuwa tana jin yarda kirjinta ke bugawa da sauri-sauri motsa laɓɓanta ta shiga yi kanta take ji yana juyawa amma haka ta kinkimo jarumtar duniya ta daurawa kanta.
"Dr.Erena...".
Ta fadi tana jan wani numfashi mai tauri gaske shi kuwa dubanta yake yi da mamaki cike da fuska jin a RANA DAYA Mufeeda ta kira sunansa abin da bata tabayi ba tsayin lokacin da ta fara aiki sosai ya natsu yana dubanta kafin ya ja kujera ya zauna.
"Na jima a duniyarka ina shawagin son ka amma sam baka lura da haka ba, na jima ina jiyar zuciyata da tayi gangancin daukar sonka ta azawa kanta, na jima ina kwaɓarta amma ta ki ji tayi nisa a sonka, na jima ina sanar da ita cewa ba mu dace ba amma bata ga hakan ba ta nuna min so ba ruwansa da haka, Dr.Erena naji ma ina son ka so mai tsanani sosai nayi zaton za ka gane in da na dosa amma ina sam hankalin ka bai kai nan ba maganar gaskiya ina son ka kai ne namiji na farko a filin duniyar nan da zuciya ta tayi amanna dashi a fannin so ban san ya zan kwatanta maka ba amma ka sani ina son ka so mai ansa suna so".
Zabura yayi daga kan kujerar da yake zaune idanuwansa cike da tulin mamakin maganganun Mufeeda hannu ya shiga nuna ta dashi yana jan numfashi kafun ya saki wata dariya wacce ta kaÉ—a 'yan hanjin Mufeeda sosai lokaci guda taji gabanta ya yanke ya fadi runtse idanu tayi wasu hawaye suka zubo ta kasar Glass din da ke fuskarta kafin ta shiga haÉ—e hannayenta waje daya tana Rolling din su.
"You Love Me? For God Sake! Mufeeda kina cikin hayyacin ki kuwa kin san waye Dr.Erena kuwa da kike daukar wa kan ki wahalar son sa to maganar gaskiya ba zan boye miki ba bana tunanin zan iya zama nayi soyayya dake bake ba ma hatta WATA MACE daban bayan Areefa bana zaton ko kallon arzuki zan iya yi mataa ya kamata ki san wani abu mace bata gabana mace daya na taba so kuma nake burin zama da ita ita ce Areefa ita ma ban san ya akayi zuciyata ta kamu da son ta ba a RANA DAYA ba zato ba tsammani naji KIBIYAR AJALI ta son ta ta cakar min zuciya wanda har zuwa wannan lokaci na kasa zareta sai kara lumewa take yi cikin zuciyata da duk wani gurbi na cikin ta".
Dubansa take yi da duk idanuwanta da suka kaÉ—a sukayi jajir fuskarta har tana canza kala izuwa ja sosai take jin duniyar nayi juya mata da duk wasu kalaman Dr.Erena da take jin su kamar saukar garwashin wuta.
Numfashi take ja da take jin sa kamar ta na jan barkono izuwa kanta dama cikin ta sosai take jin duk wani sashi na jikinta na narkewa kamar zata watse a kasa dan yatsanta daya ta kai baki tana cizawa domin tabbatar da abin da yake faruwa da ita gaskiyane ba a mafarki bane yau ta kara tabbatar wa da maganar hausawa na cewa SON MASO WANI koshin wahala ne ta tabbatar da yau Dr.Erena baya tare da ita At All baya gayyatarta a filin duniyarsa bai ma san tana yi ba.
"Na lura da abin da kika zo dashi akan Areefa duk kishi ne kina tunanin son da nake yi mata zai bari na dauki abin da ki ka zo mani dashi a gaske to ko da kuwa gaske ne ba zan dauka ba Areefa mace ce da nake so so mai garman gaske wanda bana zaton a filin duniyar nan akwai macen da zan iya yiwa ko da kwatar son ne don haka fice mani daga cikin Office".
Ya fadi yana mai yi mata nuni da hannu fuskarsa a murtuke kamar bakin hadarin da ya gangamo yake kokarin zubda ruwa.
"Dr.Erena MENE NE LAIFIN ZUCIYA don ta nuna so da kulawa akan abin da take so bana zaton son da nake yi maka zaka yi masa fatan KARKON KIFI ka sani so nake yi maka son da ban taba yi wa wani É—a namiji ba a filin duniyar nan ya kamata ace ka girmama son da nake yi maka ka dauke shi da daraja ka killace shi a zuciyarka a wani fili ko ya ya ne...".
"Are U At Of Your Sense Mufeeda kina da hankali kuwa wacce irin magana ce haka kike fadi wani irin hauka ne haka ina so dole ne nace bana yi na ce bana sonki leave alone mana".
Murmushi ta saki mai ciwo kafun ta zare Glass din dake fuskarta idanuwanta da suke rine suka bayyana sosai take duban Dr.Erena da yake mata kallon wulakanci da raini laɓɓanta ta ciza.
"Karka yi tunanin don na furta kalmar so a gareka zai baka lasisin wulakanta ni, karka yi tunanin don buɗe baki na sauke aji na da daraja ta ta 'ya mace za ka wulakanta ni ka sani ba aibu bane san nan ba zubda mutunci bane don mace ta buɗe bakinta ta fadiwa ɗa namiji tana son sa ba san nan haka ba yana baiwa ɗa namiji dama bane don ya wulaƙanta 'ya mace don ta nuna tana ta son sa ba duk macen da zata iya buɗe baki tana cewa namiji tana son sa ba abin kunya bane kuma ba abin a wulakanta ta bane domin tayani don ceto kanta da halin da zata fada ka san wannan Dr.Erena karka yi tunanin son da na nuna ina yi akan ka zai baka damar tozartani ka wulakanta ni daraja da martaba ta tana nan ba abin da ya ragu sannan ko a duniyar masoya na san nayi abin kwarai wanda da yawan mata ba sa yi sannan kuma kamar yarda mata suke tsoro halin da ka nuna min da tozarci da wulakanci don kawai na nuna ina son ka ba laifi na bane laifin zuciya tane wacce ba ƙashi gareta ba".
Dubanta ya sake yi a wulakance domin sosai zuciyarsa tayi zafi da kalamanta motsa baki ya shiga yi yana kokarin magana ta daga masa hanni.
"Ba sai ka daka min tsawa koka koreni kamar wata mara 'yanci kai ba yanzu zan bar maka Office din ka".
Tana fadin haka tayi hanyar fita daga Office har ta rike Handle din ta juyo ta dube shi sosai kafun ta kau da kai tare da ficewa daga cikin office din tana kokari hau benen da zai kai ta kasa ita kuma Areefa na sako kai saura kadan suyi gware nan suka shiga kallon kallo a tsakanin juna su fuskar Mufeeda cike da kunci da bakin ciki kallon Areefa take yi da wani irin yanayi kafun ta kau da kai gami da jan tsaki ta wuce ita dai Areefa bin ta take yi da kallo ganin yanayin da take ciki kamar akwai abin da take damun ta musamman idanuwanta da suka kaÉ—a sukayi jajir kafaÉ—arta ta daga cikin nuna halin ko in kula kafin ta isa ta tura kofar cikin Office din.
Tsaye ta same shi yana kai kawo hannayensa goye a bayan sa motsin shigowar tane ya sanya shi tsayawa yana jan numfashi fuskarsa a daure kamar hadari.
A hankali ta isa ta zauna tana mai daura kafa daya kan daya bakinta dauke da cingum tana faman taunawa idanuwanta akan Dr.Erena kallon sa take yi da wani irin yanayi mai haifar mata da ɗaci a zuciyarta sosai take dubansa da damuwar da take fuskarsa a ranta take fata dama ya dauwama a haka yaƙe ta saki kafun ta kaɗa idanuwanta.
"Me ke faruwa ne Dr.Erena?".
Sai a lokacin yaja numfashi mai girma ya na huci gami da runtse idanuwansa dubanta yayi kafun ya ja kujera ya zauna.
"Wannan mai kalar haukar ne za tayi mani akunyanci bata san na fita da duk tashencin ta ba".
Cikin rashin fahimta ta yatsine fuska cikin son karin bayani.
"Wai fa zuwa tayi tana sakin wasu banzayen kalamai kafun daga karshe ta dire da cewa wai ni take so ki ji fa wata wauta da kalar hauka".
Fakare tayi tana kallonsa tana karantar yanayin sa mamaki ya cikata ta yarda Mufeeda ta iya jefa kanta son wannan mugun mutumin mara tausayi da imani ita kam bata ga abin so a jikinsa ba bata ga abin burgewa a gareshi ba har da Mufeeda zata zo tana fada masa tana son sa har ya samu damar ci mata mutunci ya wulakanta ta ko da yake kila kudin da yake dashi ya ruÉ—eta in kuwa haka ne Mufeeda bata yi wa kanta adalci ba da tayi sake ta fada motar kwadayi ta dire a tashar wulakanci da cin mutunci.
"Ni ban ga abin ta da jijiyoyin wuya ba don tace tana son ka ai ta dace ace kai ma ka anshi son da take yi maka duk macen da zata iya zuwa ta ce tana son ka ai bata cancanci wulakanci da tozaryawa ba duk da dai ku mafiyawancin maza haka kuke in har kuka ga mace ta mutu akan son ku shikenan kun samu hanyar wulakanta ta da cin zarafin ta iri-iri".
Murmushi yayi lokaci guda kafun ya motsa laɓɓansa.
"Bana tunani haka zata kasance tsakani na da ke Areefa so daya nake yi kuma akan ki yake bana zaton akwai wata mace da zan so bayan ki akan ki na fara so kuma akan ki zan gama so ki san wannan".
"Uhmm haka dai kace aiku dama haka kuke maza akan mace akwai iya dadin baki musamman in duniya na yi muku biyayya ba abin da ba za kuyi wa mace ba".
"Areefa na lura kamar kina goyon bayan Mufeeda da ne ko baki jidadin abin da nayi mata ba".
"Ko daya wallahi amma dai ka sani mace mace ce ko min lalacewarta don haka ka kula mace ba yar wulakanci bane ita mai daraja ce da kima duk da dai wasun mazan ba su dauki mace a bakin komai ba sun mai da ita kamar riga lokacin da suke ra'ayin ta za su saka ta da sun gama kuma su cire su ajje ita da banza duk daya".
Mikewa tayi tana mai daukar jakarta ta dubi Dr.Erena da ya saki baki yana ta faman murmushi idanuwansa akanta kafun ya mike shima.
"Ya haka Areefa ina zaki daga zuwanki kuma Please ki zauna mana akwai maganar da nake so muyi dake mai muhimmanci ce".
"At this Time bana tunanin zan iya zama kuma ina da abin yi gaskiya".
"Please mana Areefa".
Juya idanu tayi kafun ta dube shi cikin gyaÉ—a kai ganin haka ya sanya shi komawa ya zauna yana mata nuni da ta zauna ita ma ba musu ta zauna yana ma kallonta kallo na sosai da sosai kafun ya ja mumfashi.
"Areefa maganar gaskiya ya kamata ace kin ce wani abu akan alakar dake tsakaninmu ya kamata ace kin motsa motsawarki kawai nake buƙata a yanzu".
Ci rashi bawa zancen nashi muhimmanci ta dubeshi kafun ta motsa laɓɓanta cikin ɗacin zuciya.
"Ina jin ka me kake nufi?".
Sai da ya sosai ƙeyarsa kafun ya saki murmushi na sosai da sosai.
"Maganar aure mana ya kamata ace mun tsayar da magana a wannan lokacin...".
Da sauri ta daga masa hannu tana mikewa kan kafafuwanta zuciyarta take ji tayi wani bugawa da tashin hankali mai girman gaske jin zantukan nashi take yi kamar saukar aradu ƙwanyarta taji tana juya a hankali ta dube shi.
"Please ka bari za muyi waya in na koma gida kaji komai zai yi settling a cikin kan kanin lokaci".
Tana gama fadin haka ta fice daga Office din cikin sauri kamar wacce zata kifa haka take ji komai taji lokaci guda ya canza mata da tashin hankali mai girma kunnuwanta take ji ba za su iya daukar kalamansa ba masu dauke da kunci da bakin ciki tafiya take yi har ta sauka kasa ta isa in da sashin ta yake komai ta kammala a hanzari ta zare key din motarta ta fice daga cikin reception din tun kafin ta isa in da motar ta take tayi mata key ta buÉ—e baya ta isa ta shige ta haÉ—e kanta da sitiyari tana mai da numfashi a hankali kanta take ji yana sarawa da karfin tsiya kamar zai rabe gida biyu sai da ta shafe lokaci mai tsayi kafin ta yiwa mota key ta fizge ta cilla ta saman titi ta shiga zabga gudu kamar wacce zata tashi sama burin ta kawai ta ganta a gida ko ta samu tayi saita kanta sosai take jin tashin hankali na tunkaro ta sosai take jin ranta na kara baci duk lokacin da suka hadu da Dr.Erena don dole kawai take zama dashi da umarnin Hajiya Layla.
*********
Tun da ya doso Muhabbir Coffee yake jin gabansa na yankewa yana faduwa lokaci lokaci hakan na karuwa sosai yaji a jikinsa akwai abin da ke kokarin faruwa dashi.
Parking yayi bayan yashiga wajan yayi oda din duk abin da yake bukata ka kawo masa a hankali yake kai Coffee bakin sa yana kurba har zuwa lokacin jikinsa bai daina sanar dashi wani abu dake kokarin faruwa dashi ba tun yana daukar lamarin da sauki har yaji zuciyarsa tana kara azalzalarsa da yabar wajan A hankali ya mike ya dauki wayarsa da key din sa bayan ya biya kudin abin da yayi oda ya doshi in da motarsa take ajje ya bude ya shiga ya zauna bayan kulle yana kokarin yi mata key yaji an dorasa masa bakin bindiga ta bayan kansa zare idanu yayi a firgice yana kallon mutane biyun da suke bayansa zaune ta glass din gaban motar.
"ja motar muje".
Daya daga cikin su yace dashi murya a buÉ—e gabadaya kamar saukar markaÉ—e.
Jikin rawa ya shiga yi jin abin da suka ce dashi ware ido yayi yana kokarin juyawa ya dube su laɓɓansa na motsi daya daga cikinsu ya daka masa tsawa cak! ya tsaya da maganar da yake kokarin yi jikin sa na ƙyarma sai faman ambaton sunan Allah yakeyi.
A hankali yayi wa motarki bayan ya yi ribas ya fice daga cikin wajan. In ba wai kasan abin da yake faru a cikin motar ba ba zaka iya cewa komai ba dubin gabadaya glass din motar mai duhu kuma a zuge yake.
Suna fita daga cikin wajan suka shiga nuna masa hanyar da zai bi a hankali a hankali suke tafiyar har suka fara ficewa daga cikin gari nan Alhaji Abdulwahaab ya kara ruÉ—ewa ganin suna tun karar daji da sauri yayi kokarin taka burki amma jin bindiga a keyarsa ya sanya shi kara wuta cikin hanzari jikinsa na rawa domin ya tabbatar wadannan mutanan barayi ne ko kuma yan satar mutane.
Daji sosai suka yanka sai da yashiga cikinsa sosai sannan suka ce yayi parking a hanzarce yayi sannan ya juya yana kokarin kallon su daya daga cikin su ya buga masa kan bingida a gefen fuska wanda hakan ya sanya shi sakin kara gami da yin lif! jikin kujera kamar wani mara lafiya wajan da suka dokar masa lokaci daya ya fara fiddo jini.
Gabadayan suka buÉ—e suka fito dayan su ya ja kofar gaban ya buÉ—e ya fizgo Alhaji Abdulwahaab zuwa waje ya baje akasa kansa na buguwa da gefen motar wata irin kara ya saki gami da ambaton sunan Allah numfashi kawai yake ja a hankali gabadaya ya gama shiga tashin hankali mai tsanani dagowa yayi cikin matsanancin yanayi yana duban su ganin su yake yi suna kasuwa bibbiyu idanuwansa suna lumshewa a hankali yana buÉ—e su bai ankaraba ya sake ji an kai masa wani wawan naushi a fuska an daki goshinsa da kan bindiga nan ya baje a sume bai sake sanin in da kan sa yake ba.
Duban juna sukayi suna masu sakin wata mahaukaciyar dariya kafin su tafa hannayensu a hankali suka fara tafiya suna ficewa daga wajan shikuwa Alhaji Abdulwahaab bai ma san in da kan sa yake ba.
Ya dauki lokaci mai tsayi can wajan magrib sanyin yamma ya kaɗashi ya farka a wahale yana kokarin buɗe idanuwansa amma jin su yake yi kamar ba a jikinsa suke ba dafe kan sa yayi sosai yana mai kara runtse idanuwansa lokaci daya ya buɗe su duhun daren da ya fara shigowa shi ya an karar dashi da sauri ya tashi zaune ya juya yaga motarsa hannu ya saka ciki Aljihu wayarsa yaji da sauri ya zaro yana dubawa 6:50pm shida da minti hamsin ya gani a hankali ya shiga kokarin tashi amma tsamin da jikinsa yayi ya hana shi kokarin da yake yi rarrafawa yayi har ya isa wajan motar ya dafata sannan ya mike yana faman cizon laɓɓansa buɗe motar yayi ya shiga a hankali yana faman numfarfashi yakeyi zama yayi sosai yana jin yarda bayansa ke amsawa da ciwo mai tsanani cikin dauriya yayi wa motar key Allah ya taimake shi ta ta shi ajiyar numfashi yayi mai karfi a hankali ya shiga yin ribas har ya juya hanyar da zata fiddo shi daga cikin daji.
Sosai ya fita daga cikin daji ya shiga gari daidai wani Super-Market ya tsaya ya daga kansa sama daidai wani shago da yake zaton clinic ne haka kuwa akayi KAMALA CLINIC ya ga an rubuta da dan hanzarin sa ya buÉ—e ya fito ya doshi wajan bayan yayi sallama ya shiga nan ya yi musu bayanin abin dake faruwa wani daga cikin ma'aikatar wajan ne ya zo yayi masa komai da ya dace har da allurai sai daya sha
Kafun ya fito ya dauki hanya zuwa gida zuciyarsa cunkushe da godiyar Allah da lamarin ya tsaya a haka ba tare da sunyi masa wata illa sosai ba.


*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
Post a Comment (0)