UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TALATIN DA SHIDA.
Juyi kawai yake yi saman faffaɗar gadonsa da ya kusan cinye rabin dakin numfashi yake ja a hankali zuciyarsa na wani irin kartawa.
A hankali ya mike yana kai kawo a tsakiyar dakin gumi mai tsananin zafi sai tsantsafo masa yake yi a goshi lokaci-lokaci yake runtse idanuwansa ba abin da yake hangowa sai Huzaif da ya rike hannun Mariya sosai yaji zuciyarsa na zafi da zugi wani katon abu mai nauyi yaji ya zo masa zuciya ya tsaya cak!.
Bai san abin dake damun sa ba a daidai wannan lokacin zuciyarsa sosai take son firgita masa tunani game da Mariya sosai yake jin wani fili mai girma ya buɗe a zuciyarsa ba abin dake yada zango a cikin sa sai lamarin Mariya sosai yake hangowa a ranar da ya fara ganinta bayan shekaru hudu da suka shuɗe ba tare da ya sanyata a idanuwansa ba.
Runtse idanuwansa ya sake yi a karo na ba adadi kafin ya shiga taka kafafuwansa a hankali yana mai isa toilet din sa ruwa ya watsa domin ko zai samu sa'ida a zuciyarsa dama gangar jikinsa gabadaya.
Yana cikin goge sumar kansa da shawul wayarsa dake yashe gefen gadonsa ta dau Ringing ya tsine fuska yayi kafin ya dubi wayar cikin halin-ko-in-kula yana mai jan guntun tsaki sai da wayar ta tsinke sau biyu kafin a na uku ya kokarta zuwa ya dauka new number ga ni kuma bata najeriya bace shiru yayi yana tunanin inda number din ta fito amma ya kasa cankowa yayi kamar zai katse sai wata zuciyarsa ta bashi damar dagawa a hankali ya latsa madannin yana kaiwa kunnansa mai makon ya rike da hannunsa sai ya ƙi sai ya makale ta a kafaɗarsa.
"Dr.Karami".
Yaji muryar ta doki dodon kunnuwansa da sauri ya yarda shawul din dake hannunsa ya dago wayar daga kunnansa yana duba number din sosai mamakin murya da yaji yake yi sosai gabansa ya buga kadan don yasan shi mai laifi ne sau ba adadi yana kiransa yana kin dauka wanda bai san dalilin ba a hankali ya ciji laɓɓansa yana mai da wayar kunnansa.
"Uhmm!".
Ya fadi da dan sauti a muryarsa.
"Ka kyauta kaji Dr.Karami...".
Runtse idanu yayi kafun ya motsa laɓɓansa.
"Please Sorry My Dr.Vijay kasan dai ba haka kawai zan shan yaka ba dole sai da dalili".
"Ban yarda ba kawai kace mani wulakanci ne ya tashi ko abin da ba halayyakar baka...wai shin ma me ya zaunar da kai ki dawo wa aiki ne har yanzu 3weeks left fa haba mana ya kamata ace duk abin da kake yi izuwa wannan lokaci ka kammala shi ka dawo".
Runtse idanu Dr.Karami yayi yana jin yarda zuciyarsa ke sake hautsinewa da wani irin yanayi mai girman gaske na tashin hankali ba ya zaton zai koma aiki ba tare da komai ya daidai ta ba, ba ya zaton zai koma Delhi a yanayin da yake a yanzu ko yace zai koma to tabbas karya yayi domin kuwa ko yaje din ganga jikinsa ne kawai zata je can din amma zuciyarsa da ruhinsa suna nan nisawa yayi kafin ya fesar da huci mai zafi.
"Ina cikin wani yanayi ne mai matukar girma Dr.Vijay a halin da ake ciki yanzu ban san ranar dawowa ta aiki ba in har ba wai komai ya zama Normal bane".
"What?!. Me kake kokarin cewa dani Dr.Karami anya kana hayyacin ka kuwa aikin naka kake mai dawa haka kana masa halin ko in kula meye ya same ka har da kake wannan ikirarin haka ya kamata gaskiya ka sauya tunani tun wuri kuma ya kamata ace ka dawo aiki at this time domin ana bukata ka".
"Ba zan iya ba".
"Kan wani dalilin?".
"Kawai dai ba zan iya dawowa a yanzu ba domin akwai abu mai girma da nake so ya zama normal in har ba wai ya zama normal din bane to gaskiya bana tunanin ko na dawo zan iya wani abun kirki".
"Shikenan Allah ya kyauta".
Abin da Dr.Vijay ya fadi kenan da damuwa a muryarsa shi kansa Dr.Karami ya lura da haka sai dai ba yarda zai yi a matakin da yake a yanzu ba ya tunanin zai iya komawa Delhi sauke wayar yayi bayan sun yi Sallama jiki a mace ya zube bakin gadon kamar wani kayan wanki hannunsa ya saka ya dafe kansa da yake jin yana yi masa wata irin sarawa kamar zai rabe gida biyu runtse idanuwansa yayi kafin ya buɗe su a hankali.
Sosai yake jin zuciyarsa na sonta sosai yake ji duk jikinsa na aiki ne da sosai yake jin zuciyarsa nayi mata ya jima yana karyata kansa akan cewa son ta yake yi ya jima yana jin zuciyarsa na sanar dashi amma ya ki ansar lamarin sosai yayi kunnan uwar shegu da komai ba tun yau ba lokaci mai tsayi da ya shuɗe zuciyarsa tana kawo masa abubuwa masu matukar girma a game da ita amma bai yi AMANNA ba.
Bai san ya zai yi ba bai san ya zai fuskance ta da wannan lamarin ba sosai yake jin wani iri a zuciyarsa sosai yake hango rashin nasara baya tunanin in ya tunkare ta da wannan lamarin zata ansheshi har ta bashi fili a zuciyarta.
Fushi take yi dashi fushi na sosai da sosai bai san mai yasa ba ya sani har da laifin sa laifin sa mai girma ne a gareta wanda bai san ya zai wanke kansa ba a idanuwanta ta ki yarda dashi taki bashi lokacin ta su zanta gudun sa take yi sosai ta ke kin haɗa ko da hanya dashi ne sosai yake bibiyarta amma bata bashi lokaci yayi iya yin sa saboda ita ya baro aikin sa saboda ita ya zauna har tsayin wannan lokacin tun da ya fara aiki bai taba zuwa ya zauna a kasar nan ba mai tsayi sai a dalilinta a dalilinta komai nashi yake canzawa wanda bai yi zato ko tsammani ba zuciyarsa ta dade da narkewa da duk wani lamarinta ruhinsa ya jima da daskarewa da duk wani abu nata kwanyarsa ta jima da buɗe fili mai girma na tunaninta.
A tunaninsa ba ta kai matsayin da zai so taba, a tunaninsa ba ta kai matsayin da zai tsaya ya nuna yana son taba, a shekarunsa gani yake yi kamar ba su dace ba, gani yake yi kamar sun bambanta a wajaje da dama sai dai wani abu da yake kokarin ruguza duk wani tunaninsa a lokaci kankani ganin yarda ta canza komai na ta ya sauya ta koma masa mace mai ansa sunanta mace ta ko wani fanni sosai yake ji a ransa yayi wauta a can baya tunaninsa bai yi masa adalci ba da ya tunano masa rashin dacewa tsakaninsa da ita sai yau ya kara tabbatar wa SO SHU'UMI NE so ba ruwansa da girma ko yarinta a ko wata zuciya zai iya sauka ya buɗe filinsa yayi yarda yake so da zuciyar.
Numfashi ya ja mai tauri kafin ya fesar da huci mai zafi a hankali ya mike ya shiga shiryawa cikin riga da wando rigar mai dogon hanni Milk-colour sai blue din wando mai haske kayan sun yi matukar ansarsa suka kara fito da tsarin halittarsa ta mazantaka kallo daya zakayi masa ka gane Allah yayi halittar ɗa namiji a wajan mai ji da kansa ta ko wani fanni.
Sosai ya feshe cikin sa da turare mai dadin kamshi dakin kansa sai da ya dauki kamshi na ban mamaki kamar anyi barinsa.
Bayan ya kammala ya dauki Key din motarsa da wayarsa ya fice can parking Space ya nufa ya fiddo motarsa sai da ya gama kare mata kallo kafin ya buɗe ya shiga yayi mata key a hankali ya ja ta ya fice daga harabar gidan ya cilla titi.
London Streat unguwar ya nufa in da gidan mahaifiyarsa yake tuki yake yi a hankali a jikinsa yake ji kamar bashi da lafiya sosai yake jin ko wani sashi na jikinsa kamar an doddoke masa cikin wannan yanayin ya isa gidan Horn yayi mai gadi ya buɗe masa Get Babban gida ne sosai kallo daya zaka yi masa kasan masu gidan akwai farcen susa ko wani sashi ka kalla tsaf yake Parking yayi ya fito bayan sun gaisa da Malam Audu mai gadi sannan ya nufa hanyar Falo din da sallama a bakin sa ya tura ya shiga ba kowa a falon sai Tv dake ta faman aiki yawatawa ya shiga yi da idanuwansa cikin falon da yake ta faman tashin kamshin turaren wuta a hankali ya ja numfashi yana mai sakin yak'e kamar wanda akayi wa dole da sauri yayi hanyar dakin mahaifiyar tasa don ya tabbata tana ciki.
Zaune ya tadda ita bayan yayi mata sallama ta ansa shi fuskarta da murmushi mai girma kallo daya zakayi mata ka tabbatar da ita ce mahaifiyar tasa suna kama sosai sai dai shi Dr.Karami ya fita hasken fata saboda hasken fatar mahaifinsa ya biyo kama ce dai ya dauko ta uwa sak!
A hankali ya isa gareta shi ma fuskarsa da murmushi kan salayar da take kai ya samu guri ya zauna ya na daura kansa a kafadarta shafar kansa tayi kafin ta rufe littafin Husnul-Muslim dake hannunta.
"My Son ya akayi ne?".
Margaya kai yayi kamar wani karamin yaro kafin ya dago kansa ya dubeta.
"Ba komai Mami kawai dai yau bana jin dadin jikin nawa ne sosai".
Zaro idanu waje tayi kafin ta furta.
"Yaa Allah da fatan dai ba wani abu bane yake damun ka".
Girgiza kai kawai yayi kafun ya mai da kan nasa jikin kafadarta.
Wani numfashi taja mai kwari kafin ta dubi Dr.Karami sosai fuskarta da wani irin yanayi mai girma na damuwa.
"Hisham".
Ta furta kamar bata so ba da hanzari ya mike yana dubanta jin ta ambaci sunansa sak! Wanda ya manta rabon da yaji ta kira shi da hakan sosai yake kallon ta jikinsa da wani irin yanayi gabansa ya ji yana bugawa a hankali.
Kau da kai tayi daga kallonsa.
"Na fara gajiya Hisham abin dai da baka so shi zan fadi ban san adadin lokutan da nake zaunar dakai muna irin wannan maganar ba ban san adadin lokacin da na dauka wannan lamarin na damuna ba abin ya fara shanlake tunani tun kafin rasuwar mahaifinka ake abu daya amma har yau babu wani lamari to maganar gaskiya in har ba so kake yi nima na mutu da wannan burin ba to ya kamata ace kayi wani abu akai ba wai takura maka nake yi ba abin da zai kuftar da kai daga fadawa halaka nake gujewa ba wai ina zargin ka bane da komai Hisham amma ya kamata ace a irin wannan shekarun naka yaci ace kana da mata har da 'ya'ya duk da dai komai na rayuwar nan sai Allah ya sa zai tabbata san nan yake tabbata".
Shiru yayi kansa na wani irin juya masa gabadaya yake jin komai na kara hargitse masa musamman yanayin da ya ga mahaifiyarsa a ciki a yau din nan ya san ta kai makura amma shi kam bai san ya zai yi akan maganar auren nan har yanzu bai jin akwai wacce zai iya zama da ita a filin duniyar nan a matsayin mata ba shi akaran kansa yana mamakin rashin aurensa bai san dalili ba bai san mai yasa sam a shekarun da ya kwashe na girman sa bai ji yana da muradin aure ba domin zuciyarsa har yau bai ji ta kamu da son wata 'ya mace ba...
Shiru yayi jin zuciyarsa na karyatashi da abin da yake fadi wanda ya tabbata a yanayin da yake ciki yanzu komai ya sauya komai ya canza sosai yake jin so a cikin zuciyarsa son ma akan wanda bai taba tsammani ba.
"Hisham kai kadai ne ɗan mu a duniyar nan kai kadai Allah ya ba mu duk da muna son 'ya'ya haka muka hakura da hukuncin Allah kai ya kamata ka share mana hawaye na 'ya'ya bila adadin amma kuma ya kamata ace kai a bangaren ka kayi aure ka hayayyafa domin Ubangiji yayi alfahari da kai nima nayi alfahari da kai mu ba muyi ba ya kamata ace kai kayi Hisham a maganar gaskiya shekarun sun kai matakin da ya dace ace ka ajje iyali in har ba so kake yi ka koma ga mahaliccin ka a haka ba ba abinda ka rasa kana da arzuki daidai gwargwado kana da aikin yi ba rashin muhalli kana da lafiyarka ko mace fiye da daya Hisham kana da halin riketa to don Allah ka duba Hisham ba wai takura maka nake yi ba a,a so nake yi kai ma ace ko ka bar duniya to ka bar wanda za a gani ace naka ne wanda hakan ba zai sa a manta da kai ba a lokaci kankani".
Dago kai yayi ya dube ta da damuwa kafin ya saki fara'a
"Mami na! Shikenan naji in Allah ya yarda ba zan baki kunya ba a wannan lokacin kin san mi ma kawai ki nemo min matar aure kawai...".
Wani kallo ta watsa masa.
"Ban yarda ba ai bani zan zauna maka da matar ba don haka da kanka zaka zaɓo matar auren ka don haka maza tashi ka bani waje na baka lokaci kayi abin da ya dace".
Kokarin kwanciya yake yi da dariya a fuskarsa ta dube shi.
"Me zakayi kasan Allah ba yarda za ayi kana katoto da kai ka karasa ni maza tafi gidan ka kaje can ka kwanta ba wai ka zo nan ka isheni ba...wai shin sai yaushe zaka koma wajan aikin ka ne Hisham lokaci fa naja kuma nasan za su ne meka ban son abin da zai zo ana dana sani".
"Na kusan komawa".
Ya fadi yana mai mikewa domin a halin da yake yanzu sam bai so ayi masa maganar kin nan nasa sam ba ya gabansa wannan tashin hankalin da yake ciki ya ishe shi Sallama yayi wa Mahaifiyar tasa yayi tafiyarsa ita kanta ta lura da sauyin ɗan nata a lokaci guda sai dai fatan ta Allah yasa lafiya littafin Husnul Muslmin din ta dauƙa ta cigaba da dubawa.
*******
Ya tsine fuska ta shiga yi ganin wanda yake kiranta sai da ta gama kare masa kallo kafun ta isa gareshi shikuwa sai faman yashe baki yake yi kamar wanda aka ce an bashi ita kyauta.
Gaidashi tayi ba tare da nuna masa komai ba ta lura da Dr.Aqeel sosai yake son bata matsala a duk lamarinta sosai yake so yake haifar mata da tashin hankali lokaci da yawa yana zuwa amma sai yaji labarin Dr.Karami ya zo sannan zai fara mata zarya kamar wacce yake bi bashi a cikin satikan nan da Dr.Karami yayi Dr.Aqeel ya zo yafi a lissafa ta rasa mai yake nufi da haka sosai take hango kamar akwai wata manufa ta daban a zuciyarsa duk da ya nuna yana sonta din ta yarda amma ita halayensa ne ba su mata ba ya fiye zafin rai da mai da karamin abu babba ita kuma abin da ta ki jini a filin duniyarta zafin rai da sauri hassala...
"Mariya ban san ta ya ya zan billo miki ba iyakar bakin kokarina nayi amma abin har yanzu dai ba canji ya kamata izuwa wannan lokaci kin bani matsaya domin ni dai da gaske nake ba karya nake miki ba ni ba karamin yaro bane da za ai ta kai kawo akan abin da bai fi shan ruwa wuya ba".
In akwai abin da ta tsana a filin duniyar Dr.Aqeel to rashin iya kalamai sam magana yake yi kamar saukar markaɗe ga shi murya ba kadan ba gabadaya sai ta cika mata kai ba wai bata son sa bane a,a sosai take jin sa a ranta amma ba ta tunanin za ta iya zama dashi a inuwa daya.
"Kice wani abu mana".
Dago idanuwanta tayi ta dubeshi sosai Dr.Aqeel ba shi da makusa ko ta miskala zarratin amma bata san mai yasa zuciyarta har zuwa wannan lokaci ta kasa amanna dashi ba.
Horn din da ya doki kunnuwansu ya sanya su gabadaya suka juya kallo daya Mariya tayi wa motar ta gane wanene wani irin bugawa taji gabanta yayi da karfi idanuwanta suka yo waje wani matsanancin tsoro taji ya ziyarce ta nan ta shiga kallon kallo tsakanin Dr.Aqeel da Motar Dr.Karami yanayin da Dr.Aqeel ya ganta aciki ya tabbatar masa da akwai wani abu domin shidai bai gane waye ma a cikin motar ba.
Numfashi ta shiga ja a hankali ji take yi kamar ta kwasa da gudu sam bata so ace sun hadu da juna domin rabon dasu tsaya a tsakaninsu tun ranar da rigima ta kacame tsakanin Dr.Karami da Huzaif shikenan ta shiga wasan buya ko ya zo wajan ta sai ta san yarda tayi ta guje masa.
"Zan shiga gida Sai anjima".
Mariya ta fadi muryarta na rawa da sauri Dr.Aqeel ya dubeta cikin mamaki da tuhuma kafin ya motsa laɓɓansa yana cizansu.
"Idan kika yi mani haka kina tunanin kinyi mani Adalci kenan Mariya me yasa wai baki son tsayawa ki fuskanci in da na dosa ne mai yasa kullu yau min in na zo wajanki baki taba bani lokacin ki...".
Numfashi mai zafi ya fesar kafin ya sake kallon motar wacce har zuwa wannan lokacin ba alamun za a buɗe ta.
"Ina son ki Mariya so mai tsanani kuma na san ke ma kina sona ko baki so ni dan komai kin so ni taimako...".
Ware idanu tayi sosai tana duban Dr.Aqeel da take jin kalamansa na saukar mata kamar aradu aka jin in da ya dosa ya sanyata daga masa hannu.
"Ban yi zaton haka daga gareka ba ban taba tsammanin zan ji haka daga gareka b Dr.Aqeel me kake son ce mani kana nufin ba saboda Allah ka taimaka mani ba ko me kana nufin dama akwai wata manufa a tsakanin taimakon da kayi mani".
Lokaci guda idanuwansa sukayi ja bacin ranta ya bayyana sosai bakin ta na rawa ta sake dubansa kafin ta kau da kai.
"Kenan ba don Allah kake so na ba kenan dama can kana da wata manufa ta daban a haka kake so na so ka a haka kake so mu zauna inuwa daya da kai a haka kake son ko mun zama ma'aurata ba zaka mance taimakon da kayi mani ko da laifi nayi maka goranta min zaka din ga yi kaico!".
Ta fadi tana mai dauke kwallar da suka zubo mata a fuska a hankali ta shiga takawa tana barin wajan zuciyarta na wani zafi da raɗaɗi kirjinta take ji yana kartawa kwanyarta na hautsine wa.
Gabanta ya sha cikin matsanancin tashin hankali idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir.
"Mariya me kike nufi da haka mai yasa zaki yi saurin yanke min hukunci akan abin da ba haka bane mai yasa kike kokarin fuskantata a hagunce na rantse miki da...".
Da sauri ta daga masa hannu izuwa wannan lokacin idanuwanta sun kawo ruwa.
"Ba abin da zaka ce mani Dr.Aqeel ba maganar da zaka sake fadamin na yarda na sani ni talaka ce wacce bata dashi wacce ubanta ya kawo su asibiti ya gudu ya bar su ba tare da komai ba...".
Wani murmushi mai ciwo ta saki kafin ta dora da cewa.
"kana da damar fada min komai ko mai kace ban ga laifin ka ba ni ce mai laifi mu muka zo wajan ka mu muka nemi taimako zaka iya fada mana komai amma ka sani a duniyar nan hanyoyin da Allah ya buɗe su da yawa suke domin wani ya zo ya nemi wani abu a wajan dan'uwansa ka sani komai yake faruwa dani da sauran iyayena ba mu muka daurawa kan mu ba ka sani ALKALAMIN ƘADDARA ne ya zana mana kuma ka sani duk wani dangin rai a duniyar nan ba yarda ƙadddararsa bata zuwa masa domin kuwa ba komai bane bawa ke nema ya samu Dr.Aqeel...".
Runtse idanu tayi jin yarda zuciyarta ke zafi da raɗaɗi a duniyar nan in akwai abin da ta tsana shine ayi mata gori tana jin zafin hakan sosai a ranta shiyasa ta kullacin hakan a ranta cewa duk yarda zatayi rufawa kanta asiri zata yi domin ta lura a duniyar nan ba abin da yafi bakinciki da takaici shine ka nema wajan wani ya dizga ka ko kuma yayi maka bayan idonka ya zo yana zaginka ko yana goranta maka a duniyar nan ba abin da yafi kwanciyar hankali da gujewa wulakanci kamar DOGARO DA KAI.
"Mariya don Allah kiyi hakuri wallahi tallahi ba haka nake nufi".
"Don Allah Dr.Aqeel ka rabu dani in har ba so kake yi zuciya ta buga ba ka barni haka ka sani ban ga laifin ka ba don ka fadi haka maganar so kuma Dr.Aqeel ka sani ina son ka amma halayenka ne na tsana ba zan boye maka ba a yau na kara gasgata abin da zuciyata ta ɗade tana sanar dani bana tsammanin inuwa daya da kake kwadayin mi zauna a tare zai yuwu".
Ta karashe tana mai kaucewa tana wucewa da sauri ya shiga kokarin shan gabanta wani kallo tayi masa hakan ya sanyashi tsayawa cak! Yana dubanta har ta karasa cikin sauri-sauri gudu-gudu.
Zubewa ne kawai Dr.Aqeel bai yi ba a kasa domin zuciyarsa yake ji tana wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata faso kirji ta fito duniyar yaji tana juya masa bai san abin da ya kai shi yin wannan maganar ba bai san mai ya kai shi ba gashi yanzu bakin sa ya yanka masa wuya yankan da bai san ko zai warke ko ba zai warke ba yanayin da ya ga Mariya a ciki ba karamar kiɗima yayi ba a hankali ya fara taka kafafuwansa hannunsa rungume da kansa har isa wajan motarsa ya shiga kafun ya dago ya dubi Motar da tun dazu take tsaye ba tare da mai ita ya fito ba sosai yaji zuciyarsa tana azalzalarsa da ya tsaya ya ga kowa waye amma a halin da yake jin kansa a yanzu ba zai iya ba yana bukatar ya gansa a gida yana bukatar ya kebe kan sa waje daya domin yin tunani da samo mafita da za ta haifa masa da ɗa mai ido.
A hankali yayi wa motar key kafun yayi ribas ya fizge ta da gudu ya bar unguwar zuciyarsa a jagule.
Dr.Karami da zuciya ta kwasoshi tun dazu yana dannewa duk abin da ya wakana yana kallo ya dade yana zargin Dr.Aqeel akwai wani abu a tsakaninsa da Mariya bai gasgata ba sai yau da idanuwansa suka gane masa zuciyarsa yaji tana zafi da wani irin turiri sitiyarin motar ya buga tare da buɗe murfin motar ya fito sai faman huci yake yi kamar wani kumurci fuskarsa har ta canza launi saboda tsananin bacin rai ya shiga kai wa iska naushi kafin ya ja kakafuwansa zuwa cikin gidan da Sallama ya shiga ba kowa tsakar gida sai muryar Mu'azzam dake tashi cikin kuka sake sallamar yayi a lokacin Umma ta ansashi kafin ta bashi izini ya iso daga kofar dakin ya tsaya suka gaisa da Umma abin da bai saba yi ba yau yayi shi kansa sai da yaji wani bambara kwai wai namiji da suna Hajara ita kanta Umma sai da tayi mamaki amma ba ta nuna masa ba.
"Mariya na ciki Umma ce ina son ganinta".
Ya fadi murya a sake amma a zuciyarsa shi kadai ya san abin da yake ji
Mariya dake dunkule waje guda tun dazu dama take jiran tsammani da sauri ta mike ta zauna tana rarraba idanu alamun rashin gaskiya sosai Umma ta shiga dubanta tana karantar yanayinta kafin ta wurga mata harara lokaci guda.
"Tashi ki fice mani daga daki sakayya".
Rau-rau tayi da idanu kamar zatayi kuka don yarda Umma tayi maganar ya tabbatar zargin da take yi yiwa Dr.Karami laifi tayi shi shi haifar da komai.
"Tashi nace tun kafin na kwaɗe ki wallahi".
Zabura tayi tana mike tana tura baki gaba har sai da ta ga Umma ta mike sannan tayi saurin ficewa daga cikin dakin bata same shi a tsakar gida ba hakan ya tabbatar mata yana waje a hankali ta fara takawa gabanta na faduwa a har ta isa cikin soron gida tana kokarin ficewa daga cikin sa sam bata lura da mutumin da ta wuce ba sai ji tayi ya kira sunanta a firgice ta waigo tana kokarin kwasa da gudu ya sha gabanta saura kadan ta fada jikinsa runtse idanu tayi jikinta ya shiga rawa sosai ta firgita da yanayin sa a hankali taji yayi gyarar murya.
"Buɗe idanunki".
Ya fadi ba yabo ba fallasa jin abin da yace ya sanyata buɗe idonta daya tana kallonsa harararta yayi da sauri ta mai da ta rufe kafin ta bude su gabadaya a firgice.
"Ke kina tunanin wannan halin da kikeyi shine mafita a gareki ko a yarda kike a matsayinki na 'ya mace kina tunanin abin da kike yi mutuncin kine na lura Mariya gabadaya kin canza halayenki ba yarda na san ki a da ba wai har kece kullum baki wajan wannan saurayi ba ki wajan waccan kuna rigima a matsayinki na 'ya mace anya kuwa bana tunanin wacce ta san mutuncin kanta da darajar ta zata kasance a haka".
Wata katangar tashin hankali taji ta rikito mata lokaci guda kanta ya shiga sarawa lokaci guda idanuwanta suka kawo kwalla ta shiga dubansa shikuwa nuna wa yayi ko a jikinsa amma can kasar zuciyarsa ji yake yi kamar ana hura masa wuta.
"Duk mace mai daraja ba za ta taba kasancewa a haka ba Mariya kin bani mamaki kin canza mani ban yi tsammanin haka kika koma ba...ba ma wannan ba tun yaushe nake garin nan amma daidai da rana daya kin ki bani lokacin ki amma kin iya baiwa wanda zaku tsaya layi kuna rigima da su saboda ni bani da wata daraja a idanunki ban cancani ki tsaya dani ba shikenan na gode amma ki sani in har kikace haka za ki cigaba da rayuwa da samari kina da katon aiki a gabanki".
Yana gama fadin haka ya fice daga cikin soron zuciyarsa na suya sosai yaji ba dadi a ransa da maganar da ya gaya mata amma haka kawai yake ji a zuciyar tasa ita kadai hanyarsa ta samu sauki duk da dai bai san ya zata dauki lamarin ba.
Idanuwanta da suke zubda hawaye ta kure kofar da su tana jin wani tashin hankali mai girma yana wanzuwa gareta a hankali taji kafafuwanta na kokarin kasa daukarta zubewa tayi kan gwuiwowinta lokaci guda ta na sakin wani kuka mai ciwo da taba zuciya...
*_KAMALA MINNA_**😘😘😘