UKU-BALA'I 38

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA TAKWAS.



Ihu sukeyi gabadaya sun karaÉ—e wajan sai cukuikuye junansu sukeyi a waje daya cikin matsanancin tashin hankali kallo daya zakayi musu ka tabbatar suna cikin tsaka mai wuya gabadaya sun jeme sun yi baki kayan jikin su gabadaya sun gama fita hayyacin su wasun suma ko kallabi babu akan su.
Janta yake yi yana faman dukanta da bakin bindiga itakuwa sai turjewa take yi tana janyon yan'uwanta suma sunan janta kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin galabaitaccen yanayi idanuwanta gabadaya sun gama rufewa kawai fizgar ta yake yi har zuwa lokacin da ya fidda ita daga cikin wajan sai numfarfashi take yi can ciki tsakiyar rana yaja ta ya watsar da ita ga ranar ta kwala sosai kamar zata darkar da mutum.
A hankali ta shiga kokarin buɗe idanuwanta jin zafin ranar na dukanta ta ko ina gashi ba wata wadatacciyar suttura bace a jikinta wando ne dogo sai riga ita ma doguwa iyakar gwuiwa da guntun hannu amma yanayin da kayan su ka koma sai ka ka rantsee yagaggune daga bola aka tsinto su kanta kuwa ba kallabi wasu hawaye suka zuba daga cikin rufaffun idanuwanta kafin ta tashi zaune tana faman cizon laɓɓanta.
Wani irin murÉ—awa taji mararta tayi lokaci guda kamar yan hanjinta da mararta za su zazzage wata kara ta saki mai razanarwa kafin ta kai hannayentala duk biyun cikin galabaitaccen yanayi tana dafe wajan zubewa tayi gabadaya a kasa tashiga murkususu da shure-shure kamar kazar daka yanka take kokarin mutuwa cikin lokacin kankani ta fice daga hayyacinta ko motsi bata yi kafin can kuma jini ya balle ya shiga kwararowa ta kasanta mai dauke da gudaje-gudaje numfashi take ja jin komai na duniyar take kamar ba nata ba duniyar take ji tana canza mata da tashin hankali mai tsananin gaske zafin da take ji tun daga cikinta har zuwa mararta ya tabbatar mata da lokacin mutuwarta yayi sosai taji dumin da ke bin kafafuwanta hakan ya kara tsinkar mata da zuciya.
Tsaye yake kanta yana kallon duk abin da ke faruwa amma ko motsi bai yi ba sai faman murmushi yake yi kafin ya juya ya dubi gabadayan alkaryar tasu sannan ya juya ya dubi sauran yan'uwan nata da ke kargame ko wacce da sakar a hannayenta da wuyanta sai faman zubda kwalla suke yi suna gunjin kuka hannu suke miko mata amma ina bata san ma a ina take ba lokacin da suka lura da abin da ke faruwa da ita ba su san lokacin da suka kara sautin kukansu ba cikin matsanancin yanayi.
Bindigar da take hannunsa ya daga ya saita in da suke ji kake daram! ya sake nan take albushiri yayi fitar burgu ya sauka cikin wajan a saitin goshin daya daga cikin yan matan wani razanan nan ihu ta saki lokacin da kanta ya tarwatse kwanya ta watse duk ta bata yan uwanta kafin gangar jikinta ya zube kasa warwas.
Ganin abin da yake faruwa ya ka sanya su cikin matsanancin rikici lokaci guda duk su rikice suka shiga kai kawo cikin wajan ko wacce hannunta akanta suna faman kankame junansu.
Ihun da yake tashi ne a wajan yana ansa kuwwa ko ta isa ya sanya shi dago tambol din sa ya fito fuskarsa a murtuke kam! ya tsaya a tsaye yana faman bin filin wajan da kallo kafun ya sauke wajan yan matan da yake hangowa sun faman rusar ihu wata razananniya tsawa ya doka lokaci guda sautin tsawar ya karaɗe wajan ƙafin ya shiga takawa cikin matsanancin zafin rai idanuwansa da wani irin yanayi na tsananin rashin imani da tausayi idanuwansa na kan su sam bai lura da abin da yake gabansa ba sai da yaji yaci karo da mutum sannan ya tsaya yana duban wajan shame ya ganta ko alamun rai babu a jikinta da sauri ya daga kansa yana duban sa.
"Ita kuma wannan fa?".
Ya tambaya cikin yanayi na halin ko in kula kafun ya sake dubanta iya zuwa lokacin tana fidda numfashi a hankali hankali.
"Shiga nayi na bukace ta shine ta saka min hakora a jiki".
Ya fadi yana mai nannaÉ—e hannun rigarsa wani wawan cizo ne ya bayyana har fatar wajan ta dauke sosai.
Ji kake kau ya dauke shi da mari kafi ya tsartar masa da yawu cikin tsananin dacin rai.
"Mai ya hanaka rabata da filin duniyar nan tun da har zata yi maka taurin kai har haka".
Yana gama fadin haka ya zaro wata karamar bindiga fisto ya saita ta lokaci guda ya sakar mata albushiri a kai shurawa daya tayi daga shi bata sake yin wani ba.
"Wa ya fada maka ana jayayya da su ai duk wacce ta tsaya tsaiko a tsakanin ku kawai dauki ranta don ba su da wani amfani a gare mu".
Ya fadi yana mai tsartawa gawan dake yashe tana zubda jini daga kanta yawu kafun ya juya cikin takun isa yana mai juya bindigar dake hannunsa har ya isa garesu tun da suka ga ya tunkara garesu suka shiga haÉ—ewa waje daya suna cakume junansu numfashin su na fita da sauri-sauri cikin matsanancin faduwar gaba da tsoro mai tsanani jikin kofar ragar da aka rufe su da ita ya tsaya yana mai yawatawa da idanuwansa akan su kafin ya saki wata mahaukaciyar dariya mai matukar razana su ya shiga sakin albushirin bindiga wajan na ansa sautin fitar albushirun hakan ya kara firgitar da su kafin lokaci daya ya daka musu tsawa da ta sanya su yin shiru wasun su har da sakin fitsari.
A hankali ya shiga kaucewa daga wajan yana faman cilla bindigar sama yana caɓewa har ya isa ga tambol din sa can nesa ya hangota tana ta faman kyalaye amai kamar zata amayar da kayan cikinta gabadaya ta gama galabaita numfashi kawai take saki cikin tsananin zafi da raɗaɗi gabadaya jikinta take ji ya canza komai nata jin sa take yi kamar ba nata ba a hankali ta shiga kokarin tashi amma jirin da taji yana dibarta ya sanyata komawa tayi zaman daɓaro idanuwanta sai faman shatatar da hawaye sukeyi gabadaya ta gama figewa ta rame kamar ba ita ba idanuwa duk sun zurma ga wani mahaukacin duhu da tayi kamar wacce ta shekara ba ta ga ruwa ba.
A hankali ya tako ya iso gareta yana bin ta da kallo kafin ya dan ranƙwafa sosai ya tallabo haɓarta a dan razane ta dago kai ganin waye ya sanya ta buge hannunsa tana mai jan jikinta can nesa dashi zuciyarta na kara cushewa waje daya ta wani tarin bakinciki da takaici mai yawan gaske kallonsa take yi kallo na tsana da kiyayya fuskarta a murtuke sai faman huci take yi ji take kamar ta cafko shi ta shake shi ya mutu ko ta huta da wannan bakar izaya da ukuba da take ciki a filin duniyar nan bata san yarda zata kira wannan lamarin ba bai ta san mai zata ce da wannan al'amarin ba bata san ya zata kwatanta rayuwar kaskanci da take cika ba ta rashin yancin da mutunta kallon kanta take yi a wata banza wacce bata da saura galihu tun da ta fado filin duniyar azzalumin mara imani wanda ba abin da ya saka gaba sai daukar rai da bai ji bai gani ba.
Murɗawar da cikinta yayi ne ya sanyata dafewa tana runtse idanu hadi da tura laɓɓanta duka cikin baki tana cizawa wata irin azaba ce taji tana kartar mata ciki da bayanta ji take yi kamar zata mutu don azaba da take ji hawaye suka shiga zuba wanda bata san ma suna zuba din ba kawai dumi take ji a sama kuncinta har zuwa kirjinta buɗe idanunta tayi ganin mutum tsaye akanta ya sanyata saurin matsawa tana watsa masa wani matsiyanci kallo mai cike da tsana da kiyayya mai girman gaske kafun ta shiga motsawa laɓɓanta suka shiga motsi hawaye sai faman ambali suke yi.
"Ka sani wannan dariyar da kake yi akwai ranar da za ta zame maka kukan jini, karka yi tunanin wannan rashin imanin da kake nunawa ba ranar da zai zo karshe, karka yi tunanin cin zarafi da keta haddi da kake yi ba zai zo karshe ba, ka sani duniyar ma gabadaya sai ka barta kamar yarda kake zama SILAR AJALI ga wasu to ka tabbata yarda ko wani dan aike yake zuwa ya dawo to ka tabbata kai ma dan aiken ka yana nan dawowa kuma duk abin da kake aiken sa yayo kai ma sai ya zo ya yi akan ka".
Numfashi taja tana jin yarda zuciyarta ke zafi da raÉ—aÉ—i da tashin hankali mai girman gaske.
"Ka kashe mani iyaye na ka rabani da gari na ka keta min haddi ka zaja min UKU BALA'I bala'in da bai taba rabuwa dani ba ka ja zamanin bala'in da ba zai taba canzawa ya koma alheri da yake kamar da ba amma ka sani shi sharri dan aike ne wallahi".
Mikewa ta shiga kokarin amma har lokacin jiri take ji wani fizga taji yayi mata ya watsar da ita kasa ya taka mata ruwan ciki da kafarsa mai dauke da wani kafcecen takalmi wani irin nishi ta saki hawaye suka zubo mata idanuwanta a runtse.
"Ina so ace na mutu amma abu daya zan roki Allah ya banni nayi rayuwa har zuwa lokacin da zan ga karshen ka zan fi kowa farin ciki da murna a filin duniyar nan mutane da yawa na san za suyi farinciki duk da dai baya in ta tafi bata taba dawowa amma ina so ace mutane da ka saka wa ciwon rai ka saka su a BALA'I zan so ace sun ga karshenka Malik".
BuÉ—e idanu tayi tana jin yarda zuciyarta take kara kekeshewa da rashin tsoronsa yinkurawa tayi zata tashi tana mai ture kafarsa daga ruwan cikin ta.
Duban gawarwakin da ake kokarin dauka guda biyu na yan'uwanta tayi kafun ta dube shi fuskarta da murmushi mai ciwo.
" 'Ya'ya Mata kayi wa haka ka sani komin daren dadewa wallahi sai hakkin su ya hanaka sukuni ba ganin ka na shiga rigar mutanan adalci kana nuna kai na Allah ne kana yaudarar mutane ta wannan hayar Uhmm...".
Taja numfashi kafin ta girgiza kai.
"Lokaci ne ba wanda yake hanyar sabawa Allah ya samu nasara komin lokacin kuwa da ya dauka yana cin nasara to akwai RANA DAYA tak! da zata zo ta rushe duk wannan nasarorin da yake zaton ya samu".
Sosai ya har zuƙa jikinsa har rawa yake yi wani wawan cafka ya kai wa wuyanta nan ta shiga kakari idanuwanta sukayo waje sun kaɗa sunyi jajir wani huci ya shiga fetar wa kamar zai ci babu kafin yayi cilli da ita can gefe guda ta hadu da wani katon dutse ta gaban goshinta lokaci guda gun ya tsage ya shiga zubda jini sosai ta ji zafin wajan amma ba ta nuna hakan ba tashi tayi ta sanya hannunta ta na dauke jinin a hankali a ko ina na sashin jikin ta azaba take ji amma jarumar zuciyarta ta kiyin rauni.
"Kisan kai da kakeyi ka dauka kuma aikin yi a filin duniyarka na rantse da Allah wata rana kai ma zaka mutu mutuwa kuwa ta wulakanci sai ka raina kan ka BAR GANIN ALLURA wallahi karfe ce bar ganin abin da kake yi kamar abun burgewa ne wallahi kai ma sai wannan hanyar ta zama silar barinka duniyar nan".
Kallonta yake yi da wani irin yanayi na mamaki tun da yake bai taba gani mace mai taurin rai kamar ta ba tun da yake bai taba ganin an kwaso yan mata an kawo masa ya samu mai taurin rai haka ba har zata iya dubansa ta gaya masa magana son ranta ba tare da fargaba ko tsoro a fuskarta ba gyaÉ—a kai yayi kafin ya bar wajan yana faman dukan iska.
Ita kuwa kuka ta saki mai taba zuciya da soya ruhi sosai ta durkushe hannayenta saman kanta ji take yi kamar ta hadi zuciya ta mutu ta bar wannan duniyar komai na cikin ta ba dadi sai yau ta kara tabbatar da cewa DUNIYA BA ALJANNA BACE ta tabbata bakomai cikin duniyar na sai ta shin hankali da rashin imani kaicon wannan rayuwa kaicon wannan zamani.
*****
Numfashi take ajjewa kyar idanuwanta sun kaɗa sunyi jajir hannunta dafe da cikinta da take jin sa yana ta faman juyawa sosai ta shiga tashin hankali sosai tayi kuka kuka wanda har zuwa yau take yin sa kuma bata san ranar daina shi ba ta shiga kunci da ukuba da bala'i ta sani bata da wata dama da za ta sake zuwa mata ta dadin rayuwa ta sani ita kam rayuwarta ta gama karewa tunda ta fado hannun wadannan azzaluman mutanan maras imani da tausayi maras ganin darajar 'YA MACE ba su dauke ta a bakin komai ba 'Ya'ya Mata sun mai da su kamar Toilet din su na duk lokacin da suƙa bukata za su je su biya bukatar su ko hali ƙaƙa ne ba sa ganin darajar koma waye bata san wasu irin mutane ba ne su bata san wata alkibla suke bi ba har ga Allah zata iya cewa ba musulmai bane domin bata ganin su da suffar ni'imar musulci ba duk da dai suna ikirarin su din haka amma ita kam bata taba yarda ba.
Nisawa ta sake yi Hawaye na kwaranyo daga idanuwanta kamar daga sama taji ana dauke mata su firgigit tayi ta dawo hayyacinta dubansa tayi kafun ta kau da kanta zuciyarta nayi mata zafi da raÉ—aÉ—i ji take yi kamar ta haÉ—iyi zuciya ta mutu da wannan bala'in da take ciki bata son ganinsa ko muryarsa bata son ji domin ganinsa kamar ganin bala'in rayuwa ne.
Murmushi yayi yana sake kai hannunsa bisa kuncinta.
"Ki yarda dani ki zauna dani mu rayu tare dake a filin duniyar nan ki yarda mu zama abu daya har gaban abada ni dake da abin da ke cikin ki".
Wani irin zillo taji cikinta yayi kafun idanuwanta suyo waje sosai fargaba da tsoron da take ji a zuciyarta akan abun da take zargi shi ne ya tabbata tabbas haka ne maganar sa gaskiya ita kanta ta sani akwai abin da ke damunta sosai taji a jikinta komai ya canza sosai take jin motsi a cikin cikinta runtse idanuwa tayi duniyar taji tana juya mata kanta yana komawa kasa kafafuwanta na dawowa sama zuciyarta take ji tana yayyagewa muryarsa da bakaken kalamansa take ji suna ansa kuwwa akan ta da cikin kunnuwanta tartsatsi da rugugi take jin kwanyarta nayi.
"Ban san ta zan sanar dake ba amma ki sani ina cikin yanayi na bukatarki a gareni ina so ki kasance dani har karshen numfashina sosai nake ji a zuciyata sosai da sosai nake jin zuciyata ta baki wani fili mai girma kina rayuwa ki sani ban taba kaunar wata mace ba ban ta taba son wata mace ba iyakata da mace na biya bukatuna da ita domin ni ban dauki mace a abun darajawa ko girmamawa ba amma akan ki ina ji a zuciyata ke ta daban ce".
Numfashi ya ja mai tauri kafun ya kureta da idanuwansa masu firgitar da ita a ko wani lokaci.
Bata san ya zata dauki wannan lamarin ba bata san a wani mizani zata ajje shi ba sosai take cikin wani mataki na rashin nasara a rayuwa sosai ta hango kaifaffan ALKALAMIN ƘADDARA ya daura tsininsa akan rayuwarta yana rubuta rubutun da take gani a matsayin ajalinta a duniyar nan rubutun da take ganin shine sanadin afkawar wannan rayuwar mai cike da tashin hankali da bakin ciki da ukuba sai yau ta kara tabbatar wa bata da sa'a ko daya a duniyar nan bata da sa'a matsayinta na 'ya mace bata da duk wasu ababe da mace zata yi alfahari da shi a duniyarta komai ya ruguje komai ya lalace wai ita ce yau dauke da juna biyu, juna biyun da ba ta hanyar aure ta same shi ba junan biyun da ya kasance ta same shi ta hanyar bala'i da masifa da jafa'i juna biyun da zata iya kiransa da shine ajalin rayuwarta.
'Yaa Zuljalali wal-Ikram'.
Ta ambata a zuciyarta da take ji tana yayyagewa tana fadowa kirjinta da tashin hankali mai girma ga wani abu mai girman gaske da take jinsa tsakanin makoshinta da kirjinta ya tsaya cak!.
Bata san me zata ce ba ita dai ta san rayuwarta ta kare rokon Allah take ya dauki ranta a filin duniyar nan rayuwar take ji gabadaya ta ishe ta bata son ta bata son komai na cikinta komai baki ne take gani bata burin sake maimaita WATA RAYUWA a duniyar nan burinta kawai numfashinta ya dauke a daidai wannan lokacin lokacin da take ji yafi komai zama bala'i a gareta.
Hawaye suka cika gaba da zuba a idanuwanta shi kuwa sai hannu yake kai wa yana dauke mata su.
"Ki ce wani abu ina son abin da yake cikin ki ina kaunarsa har dake kan ki ki yarda mu rayuwa a inuwa daya a tare har zuwa numfashin mu na karshe".
Daga idanu tayi ta dubi sashin da yan uwanta suke gabadaya sun gama mutuwa yawancin su da sunyi musu fyaÉ—e suke kashe su wasu kuma in suka ki yarda da bukatarsu suke kashe su su jefa gawarwakin a ruwa tana kallo bata da damar hanawa a gabanta sun kamo mutane masu yawa suna yin yarda suke so da su tana kallon yarda ake nunawa yan uwanta mata zallar rashin imani da tausayi amma bata san yarda zata yi ba agabanta an kashe har bata san a dadi ba an sha daukar bindiga ana bata ko wuka da sunan ta kashe wani amma bata tunanin zuciyarta zata iya zama mara imani da tausayi har haka yan uwanta musulmai ake kashewa har ake bata damar ta kashe batare da laifin komai ba.
Ruwan hawaye suka zuba mataa ta daga kai can nesa ta hango Baaba BG na kallonta tun da ta zo shi kadai ne mutumin da take kallo a mutum wanda ba irin su ba tana zaton shima kamar sato shi akayi kamar yarda suma aka sato su bata taba jin yayi magana ba bata taba jin ya buÉ—e baki ya furta kalma daya ba tausayinsa take ji mutum har mutum amma izayar da yake sha in da wahala na kisa da tuni ya mutu sosai ta fuskanci hakan bai son aikin da suke saka shi a lokuta da dama tana kallon yarda Malik yake basu umarnin aiwatar da wani aikin na mugunta amma shi sam ba yayi Malik lokuta da dama ya sha daura masa bindiga da sunan zai harbeshi amma sai ya fasa amma fa izaya ya na shanta ko yanzu da yake cikin razana tsaye sai faman gumi yake yi idanuwansa a sama yana kallon ranar da ta kyalla sosai idanuwansa sai faman zubda hawaye suke yi.
Malik ya sanya shi akan idonta yake bashi wannan azabar don kawai yaki yin mubaya'a akan abin da ya saka shi...
Karar albushirin da yaketo cikin dajin ne ya firgita su da sauri Malik ya mike yana kai kawo a tsakiyar wajan ita kuwa gabadaya ta firgice tashima ya gagare ta.
Yaran Malik ne taga suna ketowa kan baburansu a guje kamar za su tashi sama gabadaya wajan ya kaure da karar albushiri sosai da sosai Malik ya nufi cikin Tamfol din sa cikin hanzari lokaci guda kuma ya fito jikinsa da wata riga baka wulik mai kauri ga wasu igiyoyi da suke barbaje a jikinta da hanzari ya keta hanyar da ya ga yaransa na shigowa gudu yake yi kamar zai tashi sama can nesa ya hango bataliyar sojoji sun tun karo wajen bindigogin sa kirar Ak47 ya ya cilla sama tare da caɓe su a hannayesa ya shiga gudu yana sakin wuta ko ta ina cikin dajin sai da yayi tafiya sosai yana zubda sojojin da suka tunkaro alkaryar tasa albushiri ko ta ina amma shi ko a jikinsa domin albushiri da ta fado kansa yake watsewa kasa batare da ya bula jikinsa ba sai dai rigarsa ta dau hayaki a daidai inda albushirin ya sauka sosai ya cigaba da tafiya yana kallon yarda ake ta kashe masa yara hakan ya kara harzuka shi matuka lokaci guda zuciyarsa ta shiga tururi fuskarsa na kara hautsinewa idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir a daidai lokacin da ya tun kari inda yake hango bataliyar sojojin adaidai kuma lokacin albushirin bindigun nasa suka kare watsar da su yayi tare da yin wata uwar sufa ya yi kasa ya tura hannayenssa cikin ciyayin da ke wajan lokaci guda ya dago wata bingida mai saffurin mai jigida ya cilla sama kafin ya sake mai da hannunsa cikin ciyayin ya fizgo albushiri mai matukar tsayin gaske ya mike kan kafafuwansa da wani irin karfi gaske domin inda yayi tsalle ya dire sai da ciyayin wajan suka yi sama bindigarsa da ta shilla sama a daidai lokacin tayo kasa da hannu daya ya caɓe ta tare da zura mata albushirin nan ya shiga sakin wuta ko ta ina yana faman juyi kamar wanda yake amfani da wani maganakisun majajjawa.
Abin da Malik bai sani ba shine sojojin sosai suka shirya domin kuwa ƙawayansu kayi wa dajin can bangaren alkaryar tashi tuni sojojin sun isa cikin ta suka shiga sakin wuta ga duk wani yaransa sosai yan matan suka firgita suka shiga ihu saboda sautin tashin albushiri da suke ta faman ji ko ta ina ba su tsinke da lamarin ba sai da suka mazaje na bajewa a kasa matattu Mubeena dake cikin Tamfol din Malik tana kai kawo hannuwanta saman kai sai faman du'a'i take yi da fatan Allah yasa masu CETON RAI ne a garesu.
Wani albushiri ya ratso ta ciki wajan ya gogi kafatarta wani zafi ne mai cike da raɗaɗi ya ziyarce ta kwalla kara tayi da kafin gaske tare da zubewa a kasa ji take yi kamar hannu aka fizge daga jikinta zafin jinsa tayi a ko ina na sashin jikinta kararsa kuwa amsa kuwwa yayi cikin dodon kunnuwanta a hankali ta shiga jan numfashi da take jin sa kamar zai fice daga jikinta saboda tsabar azaba da raɗaɗi runtse idanuwa tayi a daidai lokacin aka banko tamfol din aka shigo sojoji ne guda biyu ko wane dauke da hula irin ta su ta sojoji hannayen su dauke da jibga jibgar bindigogi a resting din ta sukayi lokaci guda cikin cikin raɗaɗi ta buɗe idanuwanta ta kalle su lokaci guda ta mai da ta rufe tana jin suna surutunsu akan ta amma ko motsin arzuki bata iyayi ba daya daga cikin su ne ya lura da kafataɗarta da sauri yayi wa dan'uwansa alamu hakan ya tabbata masu alburushin ya same ta da sauri suka cinciɓe ta sukayo waje da ita gabadaya wajan ya zama fili sai gawarwaki dake baje can gefe kuma yan matan ne aka tare su waje guda sai faman rusar kuka suke yi gabadaya sun gama ficewa daga hayyacin su can suka nufa da Muneeba yan uwan naganinta da sauri su suka taso suka ansheta ganin halin da take ciki ya sanya su kara sautin kukan su kukan nasu ya farfado da ita daga sumar da tayi na wucin gadi a hankali ta shiga buɗe idanuwanta wanda hasken rana ya saito fuskarta komar da su tayi ta rufe kafin ta ciji laɓɓanta ta sake buɗe su sosai cikin karfin hali sosai ta shiga juya idanuwan nata tana kallon yarda sojoji sukayi wa wajan ƙawanya gabadaya numfashi taja mai tauri kafun ta dubi wanda suka riketa ganin yan uwanta ya sanya ta rushewa da wani irin kuka mai tsuma rai sosai da sosai jikinta har karkarwa yake nan suka sake buɗe babin kuka a tsakanin su sojojin sai bin su da kallo suke yi kafin su cigaba da shiga duk wani sashi na wajan.
A bangaren Baaba BG kuwa lokacin da sojojin suka fara sakin alburushin ba zato ba tsammani yaji saukarsa a hannunsa na hagu da hanzari cikin wahalallen yanayi ya saki wani nishi kamar ransa zai fita ya saukar da kansa daga kallon ranar da yake yi wanda suka gama wahaluwa jijiyoyin kansa sun fito sun burÉ—un-burÉ—un da su kwayar idanuwansa sai faman zubda ruwa suke yi.
Zubewa yayi a kasa yana kai hannun damarsa yana rike da hagun cikin wani irin yanayi mai matukar wahala sosai yaji kansa da duk jikinsa sun ansa da alburushin da ya fasa masa hannu runtse idanunsa yayi sosai kafun ya bude su dishi-dishi yake gani duban hannunsa yayi da yake ta faman zubda jini dafe wajan yayi sosai amma hakan bai hana jinin cigaba da zuba ba da hanzari ya shiga kokarin mikewa jiri na dibarsa sautin albushiri ne kawai yake ji ta ko ina zuciyarsa yaji ta kawo masa wani karfi mai girma gaske da hanzari ya tashi yana tangaÉ—i ko gani sosai bai yayi ya yanki daji yana jan jikin sa zafin raÉ—aÉ—i sai kara hauhawa yake yi tafiya ya yanka sosai sai yayi ta har kafafuwansa na kokarin kasa daukarsa amma zuciyarsa bata yi rauni ba karfi yake ji yana kara zuwa masa tun yana cijewa har ya fara gudu yana yankar daji numfashin sa na sama da kasa tafiya mai nisa yayi cikin wannan matsanancin halin har sai da sautin alburushirin dake tashi ya ragu yana jiyo sa daga can nesa bai ankara ba ya gashin gaban wani tafkeken kogi dake gudu cak! ya tsaya da tafiyar da yake yi yana mai da numfashi kafin ya zube kasa yana mai lumshe idanuwansa ko ina na jikinsa yake ji yana masa wani irin ansawa da ciwo mai tsanani buÉ—e idanuwansa yayi ya kalli hannun nasa da yake digar da jini ganin jinin ya fara bushewa hakan ya tabbatar masa ba karamar tafiya yayi ba ga hannunsa ya kumbura sosai ko ya ya taba shi zafi da radaÉ—i yake jin suna ansawa a jikinsa.
A hankali ya tashi yana tangadi ya tunkari kogin sosai idanuwansa suna lumshewa bai san lokacin da ya isa bakin kogin ba har ya tsoma kafafuwansa kawai ji yayi ruwan ya fizgeshi da wani irin karfi ya antayashi ciki gudu kogin ya shiga yi dashi ba k'ank'autawa shi kansa bai sam ba a wani hali yake ba sosai ya mika dashi hanyar da kogin yake bi yana faman sama da kasa dashi.
A bangaren su Malik kuwa abu ya kacame fada sosai ake yi ba abin da ke tashi sai sautin albushiri gawarwaki kawai zaka ke gani ko ta ina ta sojoji da ta alkaryar Malik wanda suka rage kalilan ne wuta kawai Malik yake tafiya yana yi idanuwansa a rufe ba zato ba tsammani yaji saukar wani katoton abu ya daki goshinsa ya cilla dashi can gefe ya bugu ta wata katuwar bishiya mai matukar girma kafin ya sake cilla wa wani wajan can daban ya fada cikin ciyayi har sai da ya shiga cikinta sosai da sosai runtse idanuwansa yayi kafun ya bude su sun kaÉ—a sun yi jajir yinkurin mikewa yayi amma ina bayansa yaji yayi wani irin amsawa kamar an karya bushesshen ice da sauri ya koma ya kwanta yana mai sakin numfashi ga wasu hawaye da suka shiga zubo masa a fuska ba kankautawa.
hannayensa duk biyun ya cusa cikin ciyayin wajan ya damka kana jin sautin yardda suke rumurmushewa da yake sun bushe wani bakin ciki yaji ya tokare masa kirji ga wani abu mai girma ya tsaya masa a makoshi da k'yar yake jan numfashi komai.
A karo na biyu ya sake buɗe idanuwansa jin motsi ta ko ina sojoji akansa sun yi masa ƙawanya sosai da sosai ko wannan su hannunsa dauke da bindiga sun saita shi wani takaici ne ya sake kume shi ya kurma wani irin razanan nan ihu da ya ansa sauti sosai cikin dajin...


*_KAMALA MINNA_*😘😘😘😘
Post a Comment (0)