BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 05


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 005

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya: LI'ANI. Wanda duk yayi Li'ani da Matarsa to ba za ta sake Halatta Gare shi ba har Abada, haka nan Wanda ya Auri Mace a cikin Idda kuma ya riga ya Sadu da ita a cikin Iddar wani, toh ta haramta Gare shi. Idan an Saki Mace ganta kaji kana sonta, toh kada kayi magana da ita cewa kana sonta kai tsaye, saidai zaka iya cewa idan fa tagama kana ciki, sai kabarta haka, kada kullum idan kun hadu a hanya tana Iddanta kayi ta Kawo mata maganar soyayya kana nuna cewa kana sonta, Haramun ne. Saboda haka idan ka fada mata tun farko kai kana ciki idan ta gama. Toh bai halatta ka sake wani zance nuna kana sonta ba sai lokacin da ta gama Iddarra.
    Babu Aure ga Bawa ko kuyanga sai da Izinin shugabansu. Mace ko Bawa ko Wanda ba Musulmi ba, ba sa daura wa Wata Mace aure, bai halatta ba ga mutum ya auri Mace don ya halatta ta ga Wanda ya yi mata Saki uku, kuma ma ko an yi irin wannan Auren bai halatta ta ga Mijinta na farkon nan Wanda yayi Saki uku a kanta.

Auren Mai Harama da Hajji hakan Bai halatta ba, Haka nan bai halatta ba Gare shi ya 'daurawa kansa aure ko ya 'daurawa Wani aure duk bai halatta ba.
   Auren mara lafiya bai halatta ba, Ana warware wannan auren koda an daura shi, idan kuwa ya Sadu da Ita, toh lallai ne a ba ta Sadakinta daga cikin Sulusin Dukiyarsa a fitar da shi da farko, amma ba na cikin gado ba. Idan mara lafiya ya Saki Matarsa, toh Sakin ya tabbata, kuma tana da Gado in dai ya Mutu a cikin wannan halin rashin lafiyar. Wanda ya Saki matarsa Saki uku ba ta sake halatta gareshi ba, ta hanyar mallaka ko Aure har sai ta Auri namijin ba shi ba, kuma zama waje guda ne misali zaka yi tafiya sai ka zo ka shiga moto sai ka ga matar ka a cikin moton itama zatayi tafiya, toh bai halatta kai ka shiga moton kuyi tafiyar tare ba sai dai ka chanja wani moton, wallahi akwai aiki babba gare ku masu yin Saki uku, wani zai saki Matar shi daya daya har uku, amma kullum suna tare zaka ce Ma'aura ne, wannan Haramun ne haramun ne babba, idan ba da wani Uzuri mai karfi Wanda Shari'a ta yadda cewa ya 'kebe da ita ba, haka kawai don yana jin son ta ko tana jin Son shi sai su hadu a wani waje guda domin yin zance, hakan ya sabawa fadin Allah da Manzon Allah______

Ku biyo a Fitowa na gaba In Allah yakaimu. Zamuyi magana akan Saki a kalma guda shin yaya Auren nasu yake akwai gyara ko babu, ku biyo mu

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar ku Ta WhatsApp Mai Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)