MIJI NAGARI 01


( MIJI NAGARI 01. )

4th/Muharram/1443AH-13th/August/2021

1. Miji na gari shi ne mutum mai
ilimin addini kuma yake
kwatanta aiki da iliminsa kuma
ga shi da É—abi’u masu kyau.
Lallai babu shakka wanda duk
Allah Yayi masa baiwar haÉ—a
waÉ—annan siffofi da É—abi’u, Allah
Yayi masa babbar kyauta, kuma
wannan shi ne ake ƙira miji
nagari.

2. Miji nagari shi ne wanda ya haÉ—a
wasu siffofi guda goma (10)
waÉ—anda Allaah Rabbul Izza ya ambata
a cikin sura ta 33 aya ta 35 inda
Allaah (S.W.T.) Ya ambaci maza da mata
nagari. Kuma shi ne wanda
manzon Allaah (S.A.W.) da kansa
yace idan ya nemi mace da
nufin aure to lallai a bashi.
Domin hana irin waÉ—annan
mazaje aure a lokacin da suka
nema na iya sa iyayen yarinyar
da ita kanta yarinyar su faÉ—a a
cikin wata irin fitina da kuma
É“arna a bayan kasa, haka
fiyayyen halitta Annabin rahma
(S.A.W.) ya faÉ—a acikin ma’anar
hadisinsa ingantacce.
Abin lura a cikin wannan
Magana ta manzon Allaah (S.A.W)
shi ne mutum baya zama nagari
saboda tarin iliminsa kawai
amma babu É—abi’a, haka kuma
mutum baya zama nagari
saboda kyawawan É—abi’unsa
kawai amma babu ilimi mai
amfani. Wanda kawai yake zama
nagari shi ne wanda ya hada
wadannan abubuwa guda biyu,
wato ilimin da ake aiki dashi da
kuma kyawawan É—abi’u.

3. Wata hanya ta gaba kuma na
gane mutum nagari itace wajen
alkhairinsa ga iyalansa da kuma
yawan kyautata musu. A wani
hadisi manzon Allaah (S.A.W) yace:
mafi alkahirinku shi ne mafi
alkahiri ga iyalansa, kuma nine
mafi alkhairinku ga iyalaina”.

4. Miji nagari shi ne mai
kyautata ma matansa mai
tausayinsu mai girmama iyayen
matansa.

5. Miji nagari shi ne kuma mai
kulawa da haƙƙokinsu da Allah
Ya É—ora akansa gwargwadon
ikonsa.

6. Miji nagari shi ne kuma mai yalwata
kuÉ—in cefane dana kwalliya
domin a sami abinci mai daÉ—i
kuma ta samu kuÉ—in gyara masa
jikinta.

7. Miji nagari shi ne wanda yake
yabawa da kwalliyar da matarsa
ke yi masa, kuma yake yabon
abincinta a duk sanda yaci. Idan
kuma an sami wani kuskure
wajen dafa masa abincin, to
yakan sanar da matarsa a cikin
hikima da lafazi mai daÉ—i.

8. Miji nagari shine mai ƙoƙarin danne zuciyarsa yayinda iyalinsa taimasa laifi, kuma baya yiwa matarsa fada a gaban yaranta gudun karsu rainata.

9. Miji nagari shine mai kishin
matarsa, domin manzon Allah
SAW yace: Duk mutumin da
baya kishin matarsa ba zai shiga
aljanna ba.

10. Miji nagari shi ne
wanda yake son matarsa bayan
ya aureta fiye da yanda yake
sonta kafin ya aureta, shi ne
wanda son matarsa baya fita a
zuciyarsa har bayan mutuwarta.
Domin manzon Allah (S.A.W) an
kawo masa sarkar Nana
Khadijah bayan rasuwarta, yana
ganin sarkar sai kawai aka ga
hawaye na zubowa a fuskarsa,
sai yace an tunamasa da
matarsa Khadijah, saboda
tsananin son da yake mata.

Allaah YahaÉ—amu da mata nagari, suma kuma yahaÉ—asu da mazaje nagari, Aameen Yaa Rabbissamaawaati.

Zamuci Gaba Inshaa Allaah.

Daga ÆŠan uwanku a Musulunci,

(Ustadh_Abulfawzhaan)

Post a Comment (0)