YA KASHE KANSA DA MATARSA SABODA JARUMI HRITHIK ROSHAN

YA KASHE MATARSA SHIMA YA KASHE KANSA DUK SABODA TANA NUNA SOYAYYAR JARUMI HRITHIK ROSHAN:

Rahoto Daga Shafin NEW YORK DAILY Sun Shaida Wani Miji Da Ake Tsargi Me Suna Dineshwar Budhidat Me Kimanin Shekaru 33 Wanda Yake Rayuwa a UK, Ya Soke Matarsa Da Hakan ya zama Sanadin Mutuwar ta Matar Tasa Me Suna Donne Dojoy Me Kimanin Shekaru 27 Wadda Take Aiki Ma'aikatar Nan ta Mashaya Saboda Kasancewar Tana Nuna Mugun So Ga Jarumin Kasar India Watau HRITHIK ROSHAN Wanda a Kwanan Nan Akace Shine Jarumin da yafi kowanne Kyau.

Anyi Magana da Wasu Kawayen ta Inda Duk Suma Suka Nuna Cewa Gaskiyane Yayi Wannan Aika-Aikar ne a Sanadin Soyayyar da takewa Jarumin Shi Kuma Yana da Kishi Sosai Domin a lokacin da take Kallon Wasu Fina-Finai da Sauraran Wasu Waqoqi Ya Ne mi ta Kashe Su Saboda Kishi da Yake Akanta.
 Hakan ya Ya Taba Faruwa Tun Makonni kadan da yin Auren su Inda Ya Mareta Wanda Tana da Ikon Kaishi Kotu Ayi Maganinsa Kuma Daman Yasha Dukanta da Zagi da Cin mutumci da Tsoratarwa Har da Barazanar Kisa Amma Bata taba Daukar Abin Serious ba.
Yan Uwanda Da Dama Sun Shaida Cewa Sudai Sun San Yarinya ce Me Kyau da Hankali da da Sanin Yakamata Kuma Tana Aikinta Shiyasa Suke Ganin Dole yayi Kishi Akanta Inda Kuma aka tabbatar Cewa Duk Suna Son Junan su Sosai.
Yanzu dai a karshe Bayan ya Soke ta mutu Shima yaje Ya Rataye Kansa a jikin Bishiya Shima Ya Mutu.

By #AbbaIndiaDala

Post a Comment (0)