BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 06


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA

Fitowa ta 006

Ci gaba da Bayani daga inda Muka: KHUL'I; Khu'il Saki ne Wanda babu kome a cikin sa, ko da ba a Ambaci maganar Saki a cikin sa ba, Khul'i Shine, idan Matar mutum ba ta shi wani Abu wanda yayi mata Khul'i da shi, wato ya tube igiyar Aurensa daga wuyanta.
     Wanda yace da Matarsa ke Sakakkiya ce Saki batti, toh Saki uku ne, ko ya sadu da ita ko bai Sadu da ita ba, idan ya furta mata haka, toh Saki uku kenan, sannan idan yace da matarsa, ai ke kubatacciya ce, ko igiyar Aurenki ma tana wuyanki, toh duk wannan Saki uku ne in dai ya Sadu da ita, idan kuwa bai Sadu da ita ba sai a nemi bayaninsa, wato Saki nawa yake nufi? matar da aka saki kafin a Sadu da ita lallai ne a ba ta Rabin Sadakin ta, sai dai idan ta yi masa rangwame ita da kanta, toh shikenan, amma idan batayi mai rangwame ba dolen shi ya bata Rabin Sadakin ta,

Idan bazawara ce, ko kuwa Budurwa ce, toh wannan lamarin yana Hannun babanta, haka nan Ubangida ga kuyangarsa.
    Wanda duk yayi Saki, toh yakamata yayiwa matar 'Yar kyauta ta jin dadi, haka yadace da Shari'a, yakamata ace indai ka Saki matar ka, a kalla in baka bata kyautar kudi ba, ka dauko 10,000/20,000 ka bata kyauta, idan Kai Mai Arziki ne ma yakamata ka bata kyautar gida da abin hawa, da kudi, haka Shari'a yace, idan baka da karfi kuma, ko 5,000/2,000 da abinci ka dauko ka bata ka bata hakuri, amma a wannan Zamanin wai Auren So da kauna akayi, amma idan an zo Rabuwa kaman Wuta da Auduga, za'a rabu kace nace cikin bacin rai kowa najin haushin kowa, wani yana ce ya Saki Matarsa, to da Asar da bakaken magana zai kore ta daga gidan shi, ko tausayi babu, Addini bai yadda da haka ba. Wajibi ne Mazaje a gyara saboda wannan halayya ce irinta Jihilai Wanda basu san Addini ba. amma kuma shi kyautawa Mace idan ka Saketa ba za a tilasta masa ace dole sai yayi ba, amma dai idan kayi hakan yanada kyau kuma yin haka zai kare muku wani dankon do da kauna ce. wadda bai Sadu da ita ba kuwa kuma ya riga ya yanke Sadakin da za a ba ta, toh babu Mutu'a a gareta, 

Haka nan ma Wadda aka yi Khul'i da ita, ita ma babu Mutu'a gareta, idan mutum ya mutu ya bar matar da bai yanka mata Sadaki ba, kuma baiyi khul'i da ita ba, toh tana da gado, amma babu Sadaki gareta, idan kuwa yayi Khul'i da ita, toh za a bata Sadakin ta daidai da matsayinta, idan ta yarda da wani Abu da aka kayyade mata_____

Ku biyo mu a fitowa ta gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Zuwa Ga WhatsApp Number Namu
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)