LADUBBAN MUSULUNCI A LOKACIN ANNOBA(CORONAVIRUS)


*LADUBBAN MUSULUNCI DA SUKA SHAFI ANNOBA (CORONA VIRUS)*

*Daga: ✍ Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria (Abu Sumayyah).*

*1.* Kowa ya kame bakinsa kar wanda yayi magana akan mas'alar sai masana- Ulul Amri( Malamai da Likitoci). 

*2.* Annobar Corona azabace mai gargadi ba abar wasa ba. Saboda haka a kiyaye wasa da ita.

*3.* Tuba cikakkiya zuwaga Allah (At-Taubatun Nasuh) da mayar da haƙƙi ga wanda aka zalunta.

*4.* Yawaita addu'a, istigfari da tasbihi (Allahumma inni auzu bikia minal Juzhami, wal junuuni, wal barasi, wa sayyi'il asÆ™aam). 

*5.* Kyautatawa Allah zato. Duk abinda ya same mu to akwai hikimar da Allah ya barwa kansa sa ni.

*6.* Haƙuri da rashin raaki, kuyatu da surutai akan mas'alar.

*7.* Katange marasa lafiya don karsu cutar da masu lafiya.

*8.* Sauraron shawarwarin likitoci gameda yadda za ayi mu'amala ga wanda cutar ta bayyana a gareshi.

*9.* Komawa zuwaga malaman addini gameda hukunce-hukuncen shari'ah akan mas'alar. Kamar sallah, gaisawa da mutane, zuwa gaida wanda ya kamu da cutar d.s. 

*10.* Kame baki da rashin yaɗa jita-jita akan mas'alar. Domin yanzu ana cutar da mutane da tsoratar dasu fiye da haƙiƙanin yadda cutar ta ke.

In sha'a Allah za'a ci gaba da bayanai.

*Zauren Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria Hafizahullah.*
+2348062169629
+2348143646953
Post a Comment (0)