KUNDIN MA'AURATA // 03

KUNDIN MA'AURATA // 03


FAHIMTAR BAMBANCI
Idan ya kasance ko yaushe maza ne a gaba, dole sai abin da suka ce a gida shi ne za a yi, abin da suka kawo kuma in ba a karba ba ya zama matsala, sannan mace ba ta isa ta yi aiki ba sai sun yarda, in ma suka ga dama sai ka ga sun han ta, tanan za a iya cewa sun yi kaka-gida sun qwace wa mace haqqinta, masamman in ya kasance alqalin da zai yanke hukuncin bai da basira, domin in muka koma baya za mu ga hatta wajen neman aurennan mace na jira ne sai an furta ana son ta, sannan namijin ya riqa zuwa gidanta zance ba ita ta zabo shi take zuwa zance in sun gama ta kamfato kudi ta bashi ba, hidimomin da ake yi har zuwa ranar daura aure duk ba ruwanta da su.
.
Macen duk da ta dauki nauyin wannan har zuwa daura auren, kuma ta ci gaba da daukar nauyin gidan ka je ka leqo abin dake faruwa, ka ga wanda yake da haqqin yanke hukunci a gidan, asali matsalolin da muke fama da su a yau, ba sa rasa nasaba da qoqarin da muke yi na tsallake wajibin da yake kammu zuwa karbe na abokin zamammu, in haka ne kuwa to zai yi matuqar wahala a zauna lafiya, kenan mace ta san wajibobinta, shi ma namijin ya san inda ya kamata ya tsaya da inda zai wuce, kar ka yi mamaki wata macen ta ce maka maigidanta yana yawan fushi kuma ba ta san dalili ba, don ba ta sami cikakken lokacin da za ta zauna da shi ba bare ta karance shi, amma wace duk take aiki a wani wuri ta san oganta da kyau da duk abubuwan dake damunsa don tana da cikakken lokacin karantarsa.
.
Anan ba cewa nake yi kar mace ta je aiki ba, ina qoqarin cewa ne ba ta sami cikakkakken lokacin da za ta karanci gidanta sosai ba, galibin maza abin da ya sa suke ta samun taho mu gama kenan da iyalinsu ba wai tsabar kishin ba ne, ina koyarwa a wata makaranta wani mutum ya janye matarsa, mun ji zafin hakan gaskiya don tana da hazaqa matuqa, ga zuwa makaranta a kan kari, koda wasu ba su zo ba ita za ka riske ta a cikin aji, dalilin wannan sai hukumar makaranta ta yi qoqarin sanin ko an yi masa laifi ne wanda ya sa ya yi yunqurin janye ta, amma sai ya ce ba ya samun kulawar da ta dace ne, kullum tana waje, kafin ya farka barci har ta fita, in ta dawo kuma sai ta mai da hankali kan ayyukan da aka ba ta a makantar, a taqaice dai sai da ta sauko ta yarda ta gyara wasu abubuwa sannan aka daidaita.
.
YADDA MUKE GANIN JUNANMU 
Farkon kokawar da mace za ta yi ita ce: Namiji bai son yawan koke-koke, in ma ya tsaya ya saurara din sai ka ga abin da zai yi kawai shi ne ya gama sauraron matsalolin ya fara fadin hanyoyin da za a warware su" ita mace abin da take so shi ne a nuna damuwa da halin da take ciki, kuma a ba da cikakkiyar kulawa, sannan a fahimci cewa lallai matsalar da suke fadinnan fa tabbas matsala ce, to shi gogan duk bai yi haka ba ya fara binciken warware matsala amma ba ta hanyar da ta dace ba, a qarshe ba za a iya warware matsalar ba.
.
A irin wannan halin za ka riski wasu matan sun fita harkarsa, wanda a qarshe su ma sai su fara wasu dabi'u da gangan don tura masa haushi, wata kuwa takan dage ne sai ta nuna masa abin da take so, wanda yin haka shi yake kawo hayaniya a tsakaninsu koda yaushe, haka za su yi har su gama ba tare da wani ya fahimci dan uwansa ba, a qarshe dai akan fi liqa wa namijin ne laifi, masamman in ya kasance masu kallon abubuwan dake faruwa mata ne, ta bangaren namijin kuwa za ka taras galibin abin da suke fara kokawa a kai shi ne: Ita mace kullum qoqarinta sai ta canza masa rayuwa qarfi da yaji, kamar irin bai san abin da yake yi ba ne ita za ta nuna masa ya-kamata, wato dai tana nuna cewa ita ce a gabansa ta fi shi hankali da tunani, ita za ta ce masa ya yi kaza ko ya bar kaza, ciki har da zumuntarsa.
.
Duk da cewa shi yana ganin ya gaya mata ba sau daya ba ba sau biyu ba ba ya son irin surutan da take yi, amma abin ya ci tura, ita tana ganin taimaka masa take yi, shi kuma a fahimtarsa kullum qoqarin mallake shi da maishe shi saiwar sala take yi, to da wahala su fahimci junansu, amma gaskiyar maganar tana baya, shi kullum yana waje, tunaninsa yadda za a maida naira daya ta zama biyu, da yadda za a warware duk matsalolin cikin gida, don haka tunaninsa da tsantsar abin dake faruwa a cikin gidan kadan ne, ita kuwa mai dakinsa da take gida ba ta da wani abu sai shi din, dole ta fi shi sanin abin dake faruwa a gidan, da ma alaqarsa da 'yan uwansa, da sauran abubuwan da suka shafi zumunta, da za mu yarda mu karanci juna ba shakka za mu warware matsaloli da daman gaske.
.
YADDA NAMIJI YAKE JIN KANSA
Namiji kamar yadda aka san shi yana da qoqarin hangen nesa, da jajircewa wurin isa ga abin da yake so, wasu mazan ba sa so ma a san abin da suke ciki bare wani ya yi qoqarin amshe musu abin da suke nema, ko kuma su ce sun isa gare shi ne da guminsu, ba tare da wani ya sanya musu hannu ba, to ko a gida ma irin wannan yakan faru tsakanin mutum da iyalinsa, wani yakan yi mata iyaka ya hana ta shiga lamarin 'yan uwansa, ko kasuwancinta ko wasu abubuwan da yake ganin ba su shafe ta ba, in ya zama haka to zai yi wahala ka ga ya zauna da ita ana tattauna wasu abubuwan da yake ganin shi kadai suka shafa banda ita, amma kuma da a ce ita matar za ta nemi shawararsa a irin wadannan matsalalolin za ka ga yana qoqarin nuna mata cewa kaza ya kamata, kaza kuskure ne, ashe ba wai yarda ya yi da cewa irin wadannan maganganun sun shafi mutum ne shi kadai ba, gani yake yi ba zai bari ta shugo masa ba.
.
A irin wannan yanayin shi yana gani tausayawa ce da qauna za ta sa ya ba ta shawara, amma ba zai yarda ita ta nuna tausayawa da qaunar ta wannan bangaren ba, wasu kenan daga cikinsu ba duka ba, babban abin kula a ciki shi ne, in fa ya ba ta shawara dole ta karba ta yi aiki da ita ba za ta yi gardama ba, don yin hakan rashin girmamawa ne da ba shi matsayin da yake ganin ya kai, to in muka lura da wannan sai mu gane cewa ashe babban dalilin tunkude shawarwarinta ya raina tunaninta ne, ko guje wa yin kafada da kafada da ita kan shugabancin gida, in muka koma farko, mace tana qoqarin fadin matsalolin da ta sami kanta ne a ciki, tana son a saurare ta a ba ta shawara a sanyaya mata rai, shi kuma sai ya yanke ta ya fara ba ta mafita, ko ma ya nuna mata cewa sakacinta ne, a nan dole ta yi fushi.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)