_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(12)
SHARADAN INGANCIN I’ITIKAFI,
DA KUMA MEKE BATASHI!!!
Hakika, li’itikafi yana da sharadan inganci guda bakwai:
1. Musulunci:
Li’itikafi ba ya inganta ga kafiri.
2. Balaga: Ba ya inganta ga yaron da bai balaga ba, ko mahaukaci.
3. Tsarki: Ba ya ingantaga mai janaba ko haila ko nifasi.
4. Masallaci:
Li’itikafi ba ya inganta a cikin gida ko daki ko Masallacin da ba a sallar jam’i a cikinsa.
5. Azumi:
Li’itikafi ba ya inganta ba tare da Azumi ba.
6. Barin runguma ko sunbatar mace da daddare ko da rana.
وَلاَ تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنْتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ. (سورة البقرة: آية 178)
Allah (S.W.T) ya ce: “Kar ku rungume su (mata),
lokacin da kuke li’itikafi a cikin Masallaci.” (Suratul Bakara: aya ta 178).
7. Neman iznin miji: Li’itikafin mace ba ya inganta idan mijinta bai yi mata izini ba.
ABINDA KE BATA SHI,
ME KE BATA I’ITIKAFI
Li’itikafi yana baci don aikata babban laifi,
kamar:
Zina da shan giya da karya da kazafi.
Haka nan yana baci don yin jima’i da sumba da daddare ko da rana bisa sha’awa.
Haka nan yana baci da zuwan haila, haka nan yana baci da cin abinci ko shan ruwa da rana,
haka nan yana baci in an fita daga Masallaci ba don neman abinci ko wata bukatar dan’adam ba.
_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_
_*USAINI AMFANIMA BABAN AMEENA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248