🍁 *RAYUWA SAI DA LURA {01}* 🍁
بسم الله والصلاة والسلام على رسول الله وآله وأصحابه أجمعين.
Abinda kake da shi a yanzu har kake rainawa, shine wani yake ta burin samu tun tsawon rayuwarsa, kuma har yanzu bai samu ba.
Ba lallaine RAYUWA ta tafi daidai yadda kai kakeson tatafi ba, dole ne asamu wani yafi ka, kuma kai ka fi wani, Kayi Imani tare da hakuri da hukuncin Allah domin hakanne daidai,
Allah baya kuskure, komai yayi daidai ne, kai dai rika yiwa kowa fatan Alkhairi sai kaga ka tsinci kanka a koda yaushe cikin farin ciki da walwala kuma hankalinka yakwanta.
_*Allah yakara tsare mana imaninmu kuma yasa mugama da duniya lafiya."*_
✍🏻Rubutawa
*Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com