SIDDABARUN CORONAVIRUS A NIJERIYA

*SIDDABARUN CORONAVIRUS A NAJERIYA*
Ta Najeriya, ta Daban ce.
Ita Coronovirus din Najeriya, 'yar rainin hankali ce. Tana da kebantattun ranakun da take kamu. A jihar Kaduna, Coronovirus ta yiwa jama'ar jihar Afuwa. Ba za ta kama su ba a ranakun Talata da Laraba ba.
Ta ce, duk dan jihar Kaduna, ya fita a wadannan ranaku ya yi cudanya yadda ya ga dama. Ba za ta kama shi ba.
'Yan Jihar Kaduna na godiya gareki CoronoVirus, da ki ke ba su dama sau biyu a sati.
A jihar Kano ma, CoronaVirus ta raina mutanen jihar. Ta zaunar da su a gida tsawon kwanaki. To, amma ta yi musu afuwa a ranar Alhamis da ta gabata, ta ce kowa ya fita a yi turmutsumutsu, a yi cudanya yadda ya kamata, ba za ta kama su ba. An yi cunkoso sosai, amma fa ba ta kama kowa ba.
Kanawa na godiya gareki CoronoVirus, da ki ka ba su dama a ranar Alhamis.
Kusan duk jihohin nan, CoronaVirus kan yi musu afuwa su fito a lokaci bayan lokaci.
Amma ita Coronovirus, duk da amincewa da take a cakudu a wasu ranaku, ta ce ba ta yarda da Sallah da sauran ibadoji ba a cakude ba. Ta ce, duk wanda ya fito sallah, za ta kama shi.
Kai, gaskiya Coronovirus din Najeriya ta daban ce, kuma Shu'uma ce.
SHAWARA: Akwai Waliyin CoronoVirus, Malam Nasir El-Rufa'i. Corona ta je har gida ta kama shi. Da ya yi mata walittaka irin tasa, kawai sai ya warke.
Ku garzaya Kaduna ku samo sirrin CoronaVirus wajen El-Rufa'i.

Post a Comment (0)