RAYUWA SAI DA LURA 2


🍁 *RAYUWA SAI DA LURA {02}*🍁

RAYUWA zatayi ta nuna miki cewa : Duk kawayenki sunyi aure ke kadaice yarage a unguwa sai kannen bayanki, mutane sudameki akan kinki yin aure. 

Yer uwa kedai ki kyautatawa Allah zaton cewa bai manta da ke ba , saboda komai yana da lokacin da ALLAH yaqaddara masa, babu abinda yataba faruwa lokacin sa baiyiba,

Kar hakan tasanya ki kidamu, ko ki matsawa RAYUWRKI akan dole sai kinyi abinda wasu sukayi ko sukeyi domin surutun mutane. 

Hakan zai iya kaiki ga daukar kara da kiyashi ko kuma zabin tumun dare. 

Kiyi hakuri, ki tsare mutuncinki kuma ki kiyaye dokokin Allah daidai gwargwado, kina neman Allah yazaba miki mafi Alkhairi a rayuwarki. 

Jarabawa ce kuma kowa da nau'i na jarabawar da Allah yakeyi masa. Allah yabamu ikon cinye jarabawar mu.


✍🏻 Rubutawa 
*Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com
Post a Comment (0)