RAYUWA SAI DA LURA 3


🍁 *RAYUWA SAI DA LURA {03}*🍁

 Yana daga cikin abinda bazai taba yiwuwa a RAYUWA ba shine kaga waninka ya tafi da rabon da Allah yarubuta zai sameka . 

Idan har kaga baka samu abinda Kake da muradi ba, to katabbata haka Allah yarubuta cewa ba rabonka bane, kuma duk hanyar da zaka bi bazaka taba iya samun abinda Allah bai rubuta zaka same shi ba. 

 Hanyar nan ta HARAM da kabi har kasamu abinda kakeso, da ace ka yi Hakuri ka bi hanyar HALAL zaka sameshi, saboda rabonka ne Allah yarubuta zaka sameshi. 

 Ka nutsu kuma kayarda da Allah saboda waninka bazai taba mallakar rabonka ba, rabonka zai sameka komai daren dadewa cikin yardar Allah .

 Imam Shafi'ey (Allah yayi masa rahama) yana cewa : Ni na san wanina bazai taba tafiya da rabona ba, shiyasa na nutsu (ba na tayar da hankali na akan abinda ba nawa bane sbd na San ba Rabona bane.) "

_*"Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana imaninmu"*_

✍🏻Rubutawa 
*Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com
Post a Comment (0)