🍁 *RAYUWA SAI DA LURA {05}*🍁
Idan har zaka fita daga gida, karika yabawa matarka tare da yimata godiyar abisa aikace-aikacen da takeyi acikin gidan, idan kadawo ma haka, saboda mata suna matukar son irin haka
Ke kuma idan yashigo gida, kitarbeshi da sanyayan kalamai da tattausan lafazi, saboda bakisan irin yanayin da yake ciki ba, bakisan me yatarar a waje ba,
Kar kuma kema kikara gumamasa wani haushin, sai shaidan yasamu kofar shigowa tsakninku.
Rayuwar Aure sai da lura, sanyayan kalamanku zasu iya yin tasiri wajan fatattakar shaidanin da yake fusata ku domin wargaje alakar rayuwar ku.
Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana imaninmu.
✍🏻Rubutawa
*Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com