TAMBAYA TA 59

Tambaya
:
Mutum ne yake so ya saki Matarsa, har ma ya rubuta takarda dauke da saki uku aciki, amma daga baya sai ya fasa bata takardar, Shin yanzu ta saku kenan ko ba ta saku ba??
:
Amsa:
:
Abin da Ma'abota Ilimi sukace dangane da wannan Mas'ala shine: idan Miji ya rubutawa Matarsa takardar saki, to hukunci yana komawa ne zuwa ga niyyar sa a lokacin da yake yin rubutun, idan dama a lokacin yayi hakane da niyyar saki to ko shakka babu cewa Matarsa ta saku ko ya bata takardar ko bai bata ba, amma idan a lokacin da yake rubutun ba niyyarsa ya saketa ba, saidai yayi ne kawai saboda da nufin idan nan gaba zai sake ta basai ya sake rubutawa ba, ko kuma ya rubuta ne da nufin ya baƙanta mata rai ko dan ya tsoratar da ita saboda ta dena aikata wani abu da take yi maras kyau, amma bawai yayi ne da kudurin nufin ya saketa ba, dadai wasu abubuwa makamancin hakan, Malamai suka ce a irin wannan yanayi Matarsa tana nan bata saku ba, domin Manzon Allah(ﷺ) Yace:
:
"إنما الأعمال بالنيات......"
MA'ANA:
Haƙiƙa Dukkan ayyuka (na ibada) ana yinsu ne da niyya..........
:
Kuma wannan itace fatawar waɗannan Malamai kamar haka:
①-Imamu Malik,
②-Imamu Abu-Hanifa,
③-Imamush-Sha'abiy,
④-Imamun-Nakh'iy,
⑤-Imamuz-Zuhriy,
⑥-Imamush-Shafi'iy,
Da Sauran Mafi yawa daga cikin Ma'abota Ilimi, sukace shi dai rubutu hukuncinsa kamar kinaya ce, ita kuma kinaya ba a tabbatar da saki da ita sai in da niyya, abisa ga zancen da yafi inganci, amma inda zai fito fili ƙarara ya furta da bakinsa yace na sakeki to ko shakka babu anan Matarsa tasaku,
:
Danhaka kenan idan Miji ya rubutawa Matarsa takardar saki mai ɗauke da lafazin da ya ɗauki Ma'anar saki a fili, kuma ya rubuta hakan da niyyar ya saketa din shikenan Matarsa ta saku, amma idan saki biyu ne ya rubuta ko kuma saki uku magana mafi inganci za a ɗauke shi ne amatsayin saki ɗaya kawai, duk da cewa Mazhabin MALIKIYYA sun tafi ne a kan cewa idan mutum ya saki mace saki uku a lokaci ɗaya to kawai ta saku, amma magana mafi inganci za a ɗauke shi ne amatsayin saki ɗaya kamar yadda Malamai da yawa suka yi bayani akan haka.
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

Post a Comment (0)