Tambaya
:
Malam Mecece Hikimar da ta sa rabon gadon Namiji yafi na Mace yawa??
:
AMSA:
:
Da farko dai babban abin da ake buƙata awajen Musulmi Mumini shi ne yayi Imani da dukkan wani Hukunci da yazo daga wajen Allαн(ﷻ) ko Mαnzonsa(ﷺ), domin a matsayinsa na bawa anaso ne kaitsaye yaji zuciyarsa ta Sallama da wannan hukunci, kuma yaji a ransa cewa hakan shi ne ƙarshen adalci da Allαн(ﷻ) yayi, Shin ya gano hikimar da tasa Allαн(ﷻ) yayi hakan ko kuma bai gano ba, domin Allαн(ﷻ) yana yin abin da yaga dama ne akan bayinsa kuma duk abin da yayi adalci ne babu Zalunci aciki, domin Allαн(ﷻ) yana cewa:
:
"وما كان لمؤمن ولا مؤمنة إذا قضي الله ورسوله أمرا أن يكون لهم الخيرة من أمرهم"
(سورة الأحزاب/الآية36)
MA'ANA:
Bai kasance (bai kamataba) ga Mumini (Namiji) da kuma Mumina (Mace) idan Allαн(ﷻ) da Mαnzonsa(ﷺ) suka zartar da hukunci cikin wani al'amari ya kasance (Muminai) suna da wani zaɓi acikin al'amarinsu
:
Danhaka Sallamawa da miƙa wuya shi ake buƙata ga Mumini.
Alal-Haƙiƙa Malamai sun faɗi irin hikimar da tasa Allαн(ﷻ) ya fifita rabon gadon "Ɗa Namiji" akan na "Ƴa Mace" daga cikin Waɗannan hikimomi sukace:
:
(1)-Shi dai Namiji dama Allαн(ﷻ) Ya ɗora masa wani nauyi a kansa irin wanda ba a ɗorawa Mace shi ba:
:
(2)-Namij ine zai biya sadaƙi yaje ya auro Mace:
:
(3)-Shi ne zai nema mata muhallin da zata zauna:
:
(4)-Shi ne zai ciyar da ita:
:
(5)-Shi ne zai ciyar da dukkan 'Ya'yan da ta Haifa masa:
(6)-Shi ne zai Ɗauki dukkan wani nauyi da yake da alaƙa dasu:
:
_Ammafa ita mace babu wani nauyi da aka Ɗora mata a cikin waɗancan abubuwan da a ka ambata, domin ita mace asali kafin ayi mata aure tana zaune ne a gidansu kuma Iyayenta Musamman Uba shi ne yake ci da ita kuma yake ɗaukan dukkan ɗawainiyarta, ko kuma ya kasance dan'uwanta ne Namiji (Brother) yake ɗaukan dukkan nauyinta, Sannan kuma Idan tayi aure tofa dukkan nauyinta ya koma kan Mijinta ne:
:
Sannan kuma Misali: Sau dayawa idan a ka raba gado tsakanin mace da Namiji sai aga rabon gadon shi Namijin ya ƙare ya bar na Macen, domin dama ita nata rabon ba taɓashi a ke ba, kuma watakilama bata da kowa sai wannan Ɗan'uwan nata da aka raba musu gadon tare, gashi kuma yanzu nauyinta yana kansa kenan, kuma dole da dukiyarsa zai riƙa ɗaukan nauyinta har kafin tayi aure:
:
Sannan kuma abin lura anan shine, ba fa a kowan ne irin hali na rabon gado ba ne Namiji yake ɗaukan kaso biyun Mace ba, a'a akwai gurare da yawa na rabon gado inda Namiji da Mace rabonsu yake zuwa daidai a tsakaninsu, Sannan kuma akwai yanayin da rabon gadon Mace yake fin na Namiji yawa, akwai kuma wajen da Mace take iya cin gado amma shi kuma Namiji bai ci ba, Misalin inda rabonsu yake zuwa daidai shi ne,
:
Mutum ne ya mutu yana da "Uwa" da kuma "Uba" Sannan kuma yana da "Ɗa", to anan rabon da za a bawa Uwa da Uba daidai suke ba fifiko, domin kowa a cikinsu za a bashi kaso Ɗaya bisa shida (1/6)ne na dukiyar, shi kuma Ɗan sai ya kwashe sauran.
:
Misalin wajen da gadon Mace yake fin na Namiji shi ne, Mace ta mutu tana da Miji da kuma 'Yarta guda Ɗaya, to a nan za a bawa ita 'Yar rabin dukiyane, yayinda shi kuma Miji za a bashi kaso daya bisa huɗu (1/4)ne, sannan kuma abinda ya rage na dukiyar za a bawa ita wannan 'Yar ne duk ta haɗa ta riƙe,
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/