TAMBAYA TA 63

*ANA YIN WA'AZI NE, INDA WA'AZIN ZAI YI AMFANI !*

*Tambaya*

Assalamu alaikum
Dr. tambayata ita ce mutum yana tare da abokansa suna yin shaye shaye kuma yana da damar da zai iya dauke kayan da suke yin shaye shayen, amma ba za su san shi ne ya dauka ba, to zai iya daukewa ya kone su ?

Amsa

Wa alaikum assalam, za ka yin hakan In har ba fitinar da za ta faru, saboda wannan aiki ne na hukuma, ko wanda yake da iko a hannunsa !

Amma in za'a samu sabani, ka tsaya a wa'azi shi ne wajibin ka, saboda fadin Annabi (SAW) "Wanda ya ga mummuna a cikinku to ya canza shi da hannunsa, in ba zai iya ba ya canza shi da harshensa (ta hanyar wa'azi), in ba shi da dama to ya ki abin abin a zuciyarsa".
A cikin Suratu A'alah, Allah ya yi bayani cewa: Ana yin wa'azi ne, idan wa'azi zai yi amfani.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

12/04/2020

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

Don kasancewa damu a telegram sai a danna link din dake kasa👇

https://t.me/joinchat/M_XPUBckMpCl_dPC-2MrVA

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)