*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambayata 6,606:*
=
Dun ALLAH menene hukuncin wasu daga cikin mutane da sukaga su gaskiya basu iya yin hakuri akan rashin samun sallar Jumu'a har wasu daga gungun mutane wadanda yawansu sunfi dari suke hawa kan mashin wasu kuma mota suyi tafiyar kusan 80Kilomters zuwa wani garin idan aka gama sallar Jumu'a sai su dawo garinsu.
Sannan mukuma munada abin hawa kuma munada ikon binsu Amman bama binsu saboda muna tsoron kada mu sabama dokar da government ta saka a jihar mu
=
=
Amsa
=
_Toh ai wadannan kaga su shanune bawai cikakkun mutane bane, domin shi jahili ko acikin mutane toh mutum mutumine shi bawai cikakken mutum bane. Amma banda abunsu wanene yagaya musu cewa zuwa sallar jam'i wajibine?? Amma kaf malaman duniya sun yarda cewa bin umarnin shugaba wajibine, kaga kenan wannan abunda sukeyi shima nau'ine na tawaye idan da ace ajali ze samesu ahanyar zuwa jam'in kuma ace babu uzirin jahilci toh in mutum ya mutu a wannan hanyar yayi irin mutuwar mutanen jahiliyya. Abunda zebaka haushi da irin wadannan mutanen da ace za,a tarasu ace kowa seya fadi yawan sharuddanda se mutum ya cikasu sannan zeyi sallah Allah ya amsa toh kaf dinsu zeyi wahala asamu wanda ze iya gaya maka. Toh mutuminda ko sharadin ingancin sallar be saniba shine dan yayi wannan haukan semuce yana kaunar sallarne da gaske? Ai abunda kakeso toh zuwa kake ka karanceshi, yanzu da sukeson kudi bakaga suna zuwa kasuwaba? Toh zuwa makaranta sukoyi sallar yafi muhimmanci akan zuwansu masallaci suyi sallarma. Kuma abun dadi duk wannan wahalarda sukeyi toh mutuminda ya zauna agida yayi sallah wallahi yafisu lada domin shine yadacece da sunnah kuma shine wanda baya son yakawo rabuwar kai acikin al'uma. Wani kuma abun karin takaicinma toh baccin me ilimi yafi wannan sallar tasu lada inji Malamai*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
°
Yau
15-08-1441
09-04-2020
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
Domin samun shafinmu a Telegram
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
°
Kuna iya samun tsoffin darussanmu kai tsaye ta cikin wannan shafin
http://www.zaurenkitabuwassunna.blogspot.com
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika