*AKWAI ZAKKA A CIKIN HAJAR KASUWANCI !*
*Tambaya*
Assalamu alaikum. Malam, Na karbi loan a Ja'iz Bank shekaru uku da suka wuce, na kuma shiga harkar gina gidaje, a yanzu na gama biyan kudin a wannan January 2020.
Gidajen da na gina a Millinion City 2 & 3 bedroom flats ne, amma fa suna kasuwa.
1.Tambaya ta ita ce, shin akwai Zakkah a cikin wannan, idan akwai, yaushe ya kamata a fitar?
Saboda a yanzu shekara daya kenan gidajen na kasuwa ba'a riga an sayar ba.
2. Tambaya ta biyu.
Mai dakina tana sana'ar kayan Kitchen yau shekara Ukku, Kuma Allah yasa Albarka a cikin sana'ar, yaushe ya kamata ta fidda Zakkah? saboda, wasu kudin suna hannun mutane a matsayin bashi, wasu hajane watau (kayan kitchen) ba'a riga an sayar ba.
Sannan akwai kudi a banki, amma basu isa Zakkah ba.
Shin Yaya za'a fitar da Zakkah a wannan halin? saboda idan aka hada kudin dake banki, da hajar dake kasa da kudaden dake hannun mutane na bashi, kudin sun kai Nisabin Zakkah.
Na gode, Allah Ya saka da Alheri, amin.
*Amsa*
Wa alaikum assalam
Gidajan da aka yi don siye da siyarwa ana fitar musu da Zakka in sun Shekara kuma sun kai nisabi, saboda sun zama kayan Kasuwanci, kayan Kasuwanci kuma ana fitar musu da Zakka kamar yadda Ibnu Abi-zaid Alkairawany ya yi bayani a Risala shafi na (66).
Mutumin da yake Kasuwanci, ya wajaba duk Shekara ya kaddara hajarsa da kuma kudin da suke hannunsa da kuma na banki, mutukar jumalarsu sun kai Nisabi kuma sun Shekara, zai fitar da Zakka.
Ana kasa jumlarsu ne gida Arba'in, sai a bada kashi guda.
Allah ne Mafi sani
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
08/04/2020
Don kasancewa damu a telegram sai a danna link din dake kasa 👇
https://t.me/joinchat/M_XPUBckMpCl_dPC-2MrVA
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```