GIRKIN ƘODA


*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*


*GIRKIN KODA*

Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka koda. Akwai hanyoyi da dama wadanda mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin daban yake. Don haka yana da kyau a kasance an karanta wannan shafin domin gano sirrin girki da kuma canza salon girki a kodayaushe, domin yara su rage kwadayi a makwafta.

*Abubuwan da za a bukata*

· koda
· Albasa
· Tumatir
· Garin tafarnuwa
· Magi kori
· Garin citta
· Attarugu
· Man gyada
· Koren tattasai

*Yadda ake haɗawa*

A wanke koda ta fita tas. Sannan a yayyankata kanana, sai a sanyata a cikin tukunya tare da zuba mata ruwa kadan. Sannan a rufe. Idan ya fara nuna sai a yayyanka albasa da yawa a ciki da zuba yankakken tumatir da magi da garin tafarnuwa da kuma garin citta kadan sosai. Sannan a rage wuta sai a shiga gaurayawa. A zuba man gyada kadan sai a cigaba da juyawa har sai albasa da tumatar da kuma attarugu sun nuna. Sannan a kwashe a sanya a kwano. 

Sai a yayyanka danyen albasa da koren tattasai a zuba a kan kodar domin kawata girkin. Za a iya cin wannan girkin da dafadukar shinkafa ko kuma farar shinkafa da jus din lemun zaki. A ci dadi lafiya.


*✍Written by admins*
        *Sumayya &*
        *Fauziyya*

*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
      *WhatsApp Group*
      *0814 899 2840*
      *0818 900 7071*
Post a Comment (0)