MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 10


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(10)

ZAKKAR RAKUMA: 

Malamai sun hadu a kan cewa nisabin raKuma yana farawa ne daga biyar. 
Amma fa zakkar zata
riKa bambanta 
har sai sun kai dari da ashirin,
 kamar haka:

NISABINSU :

Daga raKumi 5-9
sai a bada Akuya 1

Daga raKumi 10-14 sai a bada Awaki 2

Daga raKumi 14-19 sai a bada Awaki 3

Daga raKumi 20-24 sai a bada Awaki 4

Daga raKumi 25-35 sai a bada RaKuma wadda ta shiga shekara ta biyu (2)

Daga raKumi 36-45 sai a bada RaKuma wadda ta shiga shekara ta uku (3)

Daga raKumi 46-60 sai a bada RaKuma wadda ta shiga shekara ta hudu (4)

Daga raKumi 61-75 sai a bada RaKuma wadda ta shiga shekara ta biyar (5)

Daga raKumi 76-90 sai a bada RaKuma mata biyu ‘yan shekara uku-uku

Daga raKumi 91-120 sai a bada RaKuma mata biyu ‘yan shekara hur-hurdu.

 Idan suka haura 120 sai a koma Kirgen hamsin ko arba’in. kowace 50 a ba da raKuma ‘yar shekara hudu (4). 

Ko kuma Kowace 40 kuma a ba da raKuma ‘yar shekara uku (3).

Wan nan Shine NISABIN RaKuma Wallahu A'alam.

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)