🍜🍝 *MUKOMA KITCHEN MATA🍉🍑🍕*
🌶🥖 _SPICY FANKE_ 🥖🌶
*Kayan Hadi:*
Filawa Kofi 2
Yeast Rabin cokali
Attaruhu 4
Albasa babba 1
Maggie 2
Gishiri Rabin cokali
Mai
*Yadda Akeyi*
Zaki tankade flour a kwano Mai zurfi ki hada da yeast da Maggi da gishiri ki juya saiki ajiye agefe batareda kin kwabata ba. Ki wanke Attaruhu da Albasa ki yanka qanana ko kina iya jajjaga Attaruhun Amma ita Albasar saiki yankata. Saiki zuba su acikin hadin flour ki juya ki dauka ruwan dumi ki kwaba kamar kwabin fanke Mai sikari(yadanyi ruwa ruwa yadinga kama hannu) ki rufe ki barshi yatashi aWa 1 zuwa 2.
Ki soya Mai da Albasa ki DINGA diba kina soyawa. #yana da Shan mai#
*Wohoho dadi* 😋😋😋
_Sister saikin gwada Zaki gane me nake nufi._
✍🏻 *MRS KABEER*
( _Mommyn Nasreen)_
