💵 *_MUNE TUSHEN MATSALOLIN MU_*💵
A kullum mukan yita zagi da aibunta shugabanninmu wanda kuma hakan babban kure ne kuma illace babba a gare mu. A kodayaushe mukan canja shugaba muce bai tsinana mana komai ba, to amma fa har yau matsalarmu bata sauya ba jiya i yau. Babban dalili shine mun ki sauya kawunan mu i zuwa na kwarai balle Allah ya tausaya mana ya kawo mana canji na kwarai.
Ka na matsayin talaka zakuyi aikin wahala a biya ku kudin aikin amma a cikinku sai an samu wani ya zalinci wani, to ina kuma ga wanda kudin ku zasu biyo hannunsa ta takarda?
A matsayinka na mai gida a tsakanin iyalanka baka musu adalci ka zalinci daya ka kyautatawa daya sam basu jin dadin yadda kake gudanar da gidan, to amma har kanada bakin zagin wanda ke shugabanta kasa ko jaha guda akan wani abunda bai kai ya kawo ba. Anya in kaine a wajensa abun zai yiwu kuwa?
Yadda muka kasance haka Allah ya bamu shuwagabanni daidai damu, munsa algus da karya da son zuciya gami da yaudara a lamuranmu shiyasa duk mafi yawan shugabanninmu ma suka zama haka. Babu yadda za ayi niban kyara ba ban canja ba kaima kuma haka muyi tunanin zamu samu sauyi a rayuwan mu sai dai sauyin wuri amma bana zuciya ba, ba kuma na gaskiya gaba daya ba
Allah muke roko ya kyara mana wannan al'umma yasa kuma mu wanye da duniya lafiya. Ameen
