HIJABI NA MUMINAI MATA NE


*🧕HIJJABI NA MUMMUNAI MATA NE 01🧕*

*🧕GABATARWA:* Da sunan Allah Mai rahma Mai jin ƙai, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, wanda Ya halicci samai bakwai da ƙassai bakwai, Ubangijin Aljannatai, Mai rahma Mai jin ƙai, Mai Yalwan Rahama da Ni'ima ga bayin Sa, wanda ya yi bushara da wa'adi wa mummunai maza da mummunai mata. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu da Alayensa da Sahabban sa. 

    *🧕TAMBAYA AKAN HIJJABI🧕*

🧕“Me ya sa mata suke rufe jikinsu?” wannan tambaya ce wacce musulmai da wanda ba su ba su ke tambaya akai.

🧕Amsar wannan tambayar tana da sauƙi sosai wacce ita ce: Mata musulmai su na saka hijjabi (rufe jikinsu daga kai har ƙafafu) saboda Allah ya umarce su da yin hakan. Allah ya ce:

*🧕يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِىُّ قُل لِّأَزْوَٰجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَآءِ ٱلْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَٰبِيبِهِنَّ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰٓ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ ۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا*

🧕Ya kai Annabi! Ka ce wa matan aurenka da 'ya'yanka da matan muminai su kusantar da ƙasa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai Jin ƙai. [Suratul Ahzab ayata 59].

*✍Rubutawa: Abdullah A Abdullah Abu Khadijat (أنصار السنة)*
15/05/1440.
20/01/2019.


Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)