SALLOLIN TARAWIHI DA SALLAR TAHAJJUD (16)
Romon Azumi Ramadam da Falalarsa da Bargonsa duk ya Ta'allaka ga abubuwa 3
(1) TAFSIRIN Ramadam (2) Tarawihi (3)
Sallolin Tahajjud. Bana wannan rubutu da
farin ciki kasancewar an hana mutane yin sallolin cikin Masallaci da Majalisun mutane.
Jinjina da yabawa ga H.E. Gwannan Jahar
Kebbi Alh. Atiku Abubakar Bagudo sabada na
Sami wayoyi daban daban ga al'ummomin da ke Jahar Kebbi cewa wallahi su ba a tauye su da ko abu daya ba a Jahar dukkan Salloli Kuma
Babu doka a Jahar koda ta mintuna 10 ce ta ha na zarga - zarga dukkan kananan hukumomin.
SALLAR ASHAM DA TAHAJJUD
Jam'in Sallolin Tarawihi sunna ce
a Kan Hadisin Nana Aishatu (R.A)
Ta ce " Manzon ALLAH (S.A.W) ya
fito a wani tsakkiyar dare ya yi salla
a masallacinsa mutane suka bibiya
ga Sallarsa (Suna binsa Sallah) da
Safiya ta waye sai labari ya watsu ga
Mutane cewa (Sunyi Sallah da shi )!!
Dare na biyu sai mutane suka karu
fiye da na Jiya Manzon ALLAH ya yi
sallolin ta re da su.. Dare na ukku suka
Kara taruwa sosai ya fito ya yi Sallah su
Ka bi shi sallah. Lokacin da dare na hudu
ya yi suka taru har duk Masallaci ya cika
har waje sai Manzon ALLAH (S.A.W) bai
fito ba' suka yi ta jiransa bai fito ba sai da
lokacin Asuba ta yi ya fito. Lokacin da kare
sallar Asuba sai ya fuskanto mutane
ya yi Khudubatul Khaja sa'a nan ya ce
"Yaku Jama'ar Musulmi Ina sane da ku
(Kuna jiran fitowata) ba bu abinda ya hana
mini fitowa fa ce Ina jin tsoron kada a maida
muku ita (KiyamulLailu) ta zama farillah a Kan
ku ku kasa yin ta nan gaba"!!
Manzon ALLAH (S.A.W) ya rasu al'amari ya gudana kowa ya na zowa Masallaci ya na yin
sallarsa shi kadai ta Tarawihi ko Tahajjud
Lokacin da Manzon ALLAH (S.A.W) ya kar6a
kiran Ubangijinsa tsoron a farlantata ya kau sai
Khalifa Rashid Umar bin Khaddabi ya zo ya ga
Mutane cikin Masllaci su na Sallah daban daban sai ya ce "Lalle da na hade wadannan
mutanen sunyi wannan sallolin da limancin
Mutum daya da zaifi muhimmanci"! Sai ya nada
musu Ubayyu Bin Ka'abu ya jagoranci sallolin.
Lokacin da Umar bin Khaddabi ya ziyarce su
wani dare ya same su suna Sallah a kan kira'ar
mutum guda sai ya ce "Kai Madalla da wannan
Bidiah"!! Ya ambace ta Bidia saboda tawali'u irin nasa (R.A.) Kasancewar Manzon ALLAH
ya jagoranceta har sau ukku ya ki fitowa rana
ta hudu saboda tsoron kada a farlantata... Sayyidina Umar ya sake raya sunnar ne bayan
mutuwarta "Duk wanda ya raya Sunnah bayan
mutuwarta zai sami lada irin duk wadanda suka yi aiki da ita (Sunnar) !!
Imman Bukhari ya ruwaito shi M/4/S/ 218
Zamu ci gaba Insha Allahu gobe.
Umar Faruk Sulaiman
( Abumaisara)
Lahadi 10/5/2020
11:58 AM.
08036789142.
