ZAN IYA AUREN MAZINACIYA?

TAMBAYA ========= 👇 Aslm malam allahyasaka da alkairi Tambayat itace Wata buduruwace take harkar zinace zinace sai nakemata nasiha akan bbu keu Allah yahana sai tacemin in aureta ita tarasa Wanda zai auretane shiyasa takeyi amma inzan iyani in auret tayi alkawari zatadena Toh nikuma inada wace nakesoh in aura sannan kuma inasauraron wazin wanimalami hamd tijjani yusf yakecewa duk mecenda take zuna toh dazaran anzubamata maniiyin zina amahaifart toh duk danda yakownt awannan mahaifar zaifitu baya tausayin kowa toh wanan abun yatsoratni akan aurent Memafita malam abani shawara. AMSA ===== 👇 Maganar Gaskiya, mazinaciya sai mazinaci dan uwanta. Domin fadin Allahu Subhanahu wata'alainda yake cewa, MAZINACIYA BABU MAI AURENTA SAI MAZINACI DAN UWANTA, HAKA MAZINACI BABU MAI AURENSA SAI MAZINACIYA YAR UWARSA, AN HARAMTA HAKAN AKAN MUMINAI. Wato indai kasan baka yin zina, bai kamata ka aureta ba, sai dai da da'awar taka zata mike, sai ka kawo mata wani wanda yake mazinaci ne dan uwanta, sannan ka biya masa sadakin aurenta din, sabida mazinaci ba lalle ka sami kudi a wurinsa ba. Allah shine masani ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)