💌 *Wasika daga Zuciya:*
✍ Mansur Sokoto
17 Ramadhan 1441H (10/05/2020)
*Abinda ke damu na:*
1. Duk inda na buga waya labarin mutuwa ake ba ni.
2. Idan na buda Facebook labaran mutuwa ne a ko ina.
*Fatawa:*
Kowa ka tambaya cewa yake yi: Ba Corona ce ba.
*Dalili:*
Masu mutuwar duk masu hawan jini ne da ciwon Sugar, sai kuma tsofaffi.
*Wata Tambaya*:
Tun yaushe ne suke dauke da wannan ciwon? Ko a satin nan ne tsufansu ya kama?
*Tambaya Ta 3:*
A duk duniya ana ta mace-mace, kuma an yarda Corona ce musabbabi. Me ya sa tamu mutuwa ta bambanta?
*Abin lura:*
Idan mun yarda da matsala mun kama hanyar maganin ta. Idan ba mu yarda ba to, mun dauki matakin ci gabanta.
*Laifin wa ye?*
1. Wadanda ke da alhakin wayar da kan jama'a har yanzu akwai aiki babba a kan su.
2. Masu kutsawa a cikin abinda ba su sani ba suna daukar wa kansu nauyin da za su yi da-na-sani a kan sa.
*Babbar Matsala:*
Babu yarda a tsakaninmu da Jagororinmu na mulki da na addini.
*Addu'ata:*
Idan wannan ibtila'in shi ne ajalinmu, Allah ya karbi uzurinmu ya sa mutuwar shahada ce a gare mu.
*_Wassalam_*
