MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 15


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(15)

NISABIN MA’ADANAI : 

Game da nisabin Ma’adanai kuwa, a wajen Imamu Malik da Shafi’i da Ahmad, ba za a fitar da Zakkar ma’adanai ba sai sun kai nisabi.

A nan ana nufin nisabin Dinare ko Azurfa.

Game da abin da za a fitar kuwa sai Malikiyya da Hambaliyya suka ce,

 a fitar da daya bisa arba’in. Wato kamar na Zakkar kudi.
Illa dai malikiyya sun ce idan ba a wahala ba wajen fitarwar sai a bayar da daya bisa biyar, 

su kuma Hanafiyya sai suka kasu uku: Na daya: Masu cewa a kasa arba’in a fitar da daya, 
kamar Zakkar kudi. 

Na biyu: masu cewa a kasa biyar a fitar da daya,
kamar Zakkar Rikaz.

Na uku: masu cewa, idan ba a wahala ba a kasa biyar, idan kuwa aka wahala to sai a kasa arba’in.
Za a fitar da zakkarsu ne a sanda aka fitar da su. Ba sai sun shekara ba.

 *( Duba Zakatul Ma’adini na Mukhtar bin Umar Al-Husaini As-shankidi sh: na 45 - 61.)*

 Game da ajiyar mutan da kuwa,
ana nufin dukiyar da aka samu ta mutanen da.
Mafi yawan malamai sun ce ba sai ta kai nisabi ba za a fitar mata da Zakka.

Haka kuma ba sai ta shekara a wajen wanda ya samu ba. Sai kawai ya kasa biyar ya bayar da kashi daya.

Amma shin za a sarrafa abin da aka fitar ga masu cin zakka ne kamar yadda Imamus Shafi’i ya nuna? 

Ko kuwa ga masu cin fai’u, kamar yadda Imam Malik da Abu Hanifa da Ahmad suka ce?

*( Duba Zakatul Ma’adini na Mukhtar bin Umar Al-Husaini As-shankidi sh: na 67 - 76.)*

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)