AZUMIN RANAR ARFA DA FALALARSA
*A-Azumin ranar Arfa*
Yin azumin ranar Arfa yana da falala mai girma kuma sunnane na Manzon Allah s.a.w.
Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kasance yana yin Azumin *ranar Tara ga watan Zul-hijjah,da ranar Ashura da kwanaki ukku a kowane wata*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﺑﺮﻗﻢ 2106.
*Falalar Azumin ranar Arfa ga wanda baije aikin Hajji ba*
i-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805.
ii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335.
iii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta...........)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3853.
Allah ne mafi sani.