MUSULUNCI BAYA YUYUWA SAI DA KARATU!
Addinin musulunci addini ne da baya yuyuwa sai da karatu, shiyasa duk wanda ya zauna baya karatu bai da mai koya masa karatu to yayi asarar duniya, kuma ba zai san yayi asara ba sai san da ya wayi gari a gaban Ubangijinsa. An masa tambaya daga gidanka zuwa inda ake karatu Mill nawa ne? Sannan zai gane yayi asara. Wani ma a kofar gidansa ake karatun, wanda Manzon Allah cewa yayi *'ka je ka nemi ilimi ko da a birnin sin ne'* lokacin da babu jirgi, babu mota, babu keke, babu babur babu komai amma a tafi har birnin sin, amma kai yanxu a unguwarku ana karatu kafi karfin kaje, sai dai ka zauna a majalisa kayi ta hira, ko ka zauna kayi ta charting, ko kallo, ko ka tafi yawon banzanka! To wallahi mutum bazai gane kuransa ba, sai lokacin da yayi arba da Ubangijinsa Madaukaki idan bai gyara ba.
Domin baka da wani uzuri a wajen Allah madaukakin sarki, saboda yanzu idan malamin Qur'ani kake so to, akwai su gasu nan a unguwarka, a kowace unguwa kake a kano ko kauye gasu nan, hatta dalibin da ke jami'a gasu nan akwai su, akwai irin su MSSN da sauransu, haka idan malamin hadisi kake nema, ko na fiqhu, ko sira, duk gasu nan a zube, so suke ma kazo domin su koya maka, sun bada lokacin su domin su karantar din, mutum sai yayi nazarin sama da awa biyar yana bincike sannan ya zo yayi karatun awa 1 domin ya fa'idantar da kai.
Amma kai babu ruwanka kayi zamanka, kaqi zuwa ☹️ kana ji da kai ko ganin kafi karfin zuwa makaranta saboda kana da kudi ko kuma kai dan boko ne, amma da ace ana raba naira dari ko koko da kosai ma, to da kana cikin sahun farko wajen karba, watakila ma kayi wajen awa daya kana jira, haka dalibai a jami'a suma zasu qi zuwa masallaci ko majlisan da ake karatu don su saurara na awa daya kawai, amma zasu ɓata sama da awa 16 suna karatun boko ☹️. To ba laifi bane don kayi awa 16 kana boko ba, amma laifi ne a sanda ka kasa bawa Allah lokacin ka.
Kuma babban takacin ma shine yanzu idan ka mutu mai xaka cewa ALLAH❓ idan yau abun duniya ne ko nemanta ka fi kowa garaje wajen sai ka samu,amma kana zaune ana karatun addini kaki zuwa, kaga wannan babban tashin hankali ne?!
Allah ya bamu ikon gyarawa baki daya, ya bamu ilimi mai amfani
🗣️Khudbar Juma'a: *Dr Abdulmdallib*
*📝Abou Khadeejatu Assalafeey*