*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambayata 6.037:*
=
Azumin da akace anayi tundaga 1-10 da watan ZULHAJJI ,menene ingancin yinshi tafannin shari'a?
=
=
Amsa
=
_Babu wani hadisi ko daya wanda yazo kuma ya inganta daga Annabi (s.a.w) cewa ana yin wasu azumomi na musamman a wadannan kwanakin in banda ranar arfa, itace kawai hadisi yazo akanta amma duk sauran ranekun babu dalili akan azumtarsu. Amma dai yin azumin acikinsu ba lefi bane domin hadisi ya tabbata cewa babu wasu kwanaki wadanda ake samun falala idan aka aikata alheri acikinsu samada wadannan kwanakin, to kuma azumi shima dayane daga cikin dubban ayyukan alheri, dan haka bawai azumi kadai akeyiba Aa duk wani aikin alheri kamar sallar nafila da sadaka da ciyarwa ko taimakon marayu duk wadannan suma ayyukan alherine sannan kuma wanda yaga cewa ze iya azumtar ranekun tara baki daya shima babu lefi amma dai yasani babu wani hadisinda yace yayi, sedai kawai yayi tunda ba haramun bane kuma ansamu cewa Annabi (s.a.w) shima ya taba azumtar ranekun tara kamar yadda yazo acikin hadisin Ummu salama sedai akwai sa6anin malamai akan wannan matsalar kamar yadda muka fadada bayaninta cikin wata lekcarmu me taken watan zulhijja****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
°
Yau
26-11-1440
29-07-2019
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
Domin samun shafinmu a Telegram
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
°
Kuna iya samun tsoffin darussanmu kai tsaye ta cikin wannan shafin
http://www.zaurenkitabuwassunna.blogspot.com
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaikait