BUDURCI NA 20


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{20}

Adarasin mu nabaya munji yada wata baiwar Allah ta koka ko take Jan hankalin iyaye da suyiwa Allah sukula da matsalolin yayansu musanman mata, toh wan nan jan hankali nata yasa naga yadace da wan nan Darasi muka gaba tar dashi kamar yadda tabukata ko saqon zai isa ga iyayen mu,

Toh wan nan yasa nikuma naga kawo wata kadiyya da tafaru akasar larabawa wan wani babban Malami daga cikin malaman kasar Makka garin *(manzon Allah Sallallahu Alayhi wasallam)*

Shide wan nan malamin yarubuta littafine kan wan nan al'amarin da yafaru ga wata yarinya balarabiya da kuma babanta, kuma yaja hankali iyaye kan sukula da haqqi da amanar da Allah ya Dan ka musu na yayan da suka Haifa Musanman mata,

Malamin yabada labarin yace akwai wani dattijo acikin garin maka ya kasance yanada wata "ya guda daya kyakkyawa balarabiya kuma gata da kokari wajen karatu. Lokacin data gama karatun secondary takai munzalin aure se Manema aurenta suka fara bayyana suna zuwa Neman aurenta Amma uban se yace karatu zatayi yanxu,

Ahaka ahaka har ta gama jami'a university masu zuwa Neman aurenta suna ci gaba da zuwa se yace aiki zatayi ba aureba, tasamu aiki mai kyau tana kawo masa albashin ta yana Jin dadi yana ta kashewa har wataran ta kwanta rashin lafiya,

Jiki yayi tsanani taga alama mutuwa zatayi setacewa mahaifinta tanaso ya gayyato mata manyan Malamai haka kuwa akayi ciki harda shi wan nan malamin da yake bamu labari cikin littafinsa, 

Yace tana kwance kan gadon asibiti ga malamai ga mahaifinta setace baba zanyi addu'a kace ameen ku kuma kushaida sukace sun shaida harda shide wan nan malamin tasake cewa baba kace ameen yace Ameen tasake Addu'a tace baba kace ameen yace Ameen,

Toh anan ne tace baba kasan menace cikin Addu'a ta? Yace A'a tace masa baba cewa nayi yadda ka yadda kangeni agida kahanani shiga gidan aure toh kaima Allah yakangeka yahanaka shiga gidan aljanah,

Yadda ka kuntatamin kahanani aure kaima Allah yakuntata maka ranar Alqiyama,
Yadda ka hanani Jin dadin aure kaima Allah ya hanaka abinda kakeso Ranar Alqiyama,

Tana gama wan nan bayani se Allah yadauki rayuwarta, toh babban tashin hankali shine ta mutu bare yanemi yafiyarta tayafe masa ,


Shine wan nan malamin yayi rubutu akai da tambayoyi ga dukkan iyaye na duniya,
Shin wan nan Addu'a tata takarbu agurin Allah?
Shin ko uba yanada haqqin yahana yayansa aure Dan Neman abin duniya?
Dade sauran tambayoyi wanda kaima me karatu zaka yiwa kanka Allah yasa mu dace Allahumma Ameen yãhayyu-yãQayyum 

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)