WAƘAR FAUZIYYA D. SULAIMAN

JINJINA DA YABO GAREKI, BISA AIYUKKA NA JINƘAI, 
ALLAH ƘARA RIƘO DA HANNUNKI FAUZIYYA D. SULAIMAN. 



Ya mafi iya saka khairi,
Ka yi sakamakonKa tari,
Kariya daga dukka sharri,
Ɗaukaka da rufin asiri,
Ƙara yi wa Fauziyyar nan.


Allah Baiwarka ga ta,
Fauziyyar Marubuta,
Mai jinΖ™an mabuΖ™ata, da
Garkuwar yara da mata,
Inuwa ta shiga su huta,
Yi jibintar lamuranta,
Har ma da gidauniyarta,
Ƙarfafa guiwa gareta,
Yi daΙ—in buΙ—i, wadata,
Ƙara yauΖ™aΖ™a arziΖ™inta,
DaΙ—a tsarkake zuciyarta,
Ya Allah Ka tsare ta,
Ga duk sharrin magauta,
Da shiga komar macuta,
Kar sui nasara a gun ta
Janye sheΙ—anu jikinta,
Ka tsaya mata kai-da-fata,
A cikin duk lamuranta,
Masu son su ga tawayarta,
Ko Ι“acin ayyukanta,
Kar sui nasara a kan ta,
Yi daΙ—in shiriya a gunta,
Ta fi Ζ™arfin zuciyarta,
Darajarta ka Ι—aukakata,
Ƙara albarka gareta,
Kyawun Ζ™arshe Ka bata,
Da shahada Ι—auki ranta,
Aljanna ciki ka sa ta,
Ka yi jinΖ™an walidanta,
Albarkaci zuri'arta,
Bayanta ka kyautata ta,
DaΙ—a kyakkyawar fahimta,
Da uban 'ya'ya mijinta,
So da Ζ™auna ka daΙ—e ta,
Da biyayyar Annabinta,
Don isar mulkinKa Amin.
Post a Comment (0)