*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 27```
.
2) YI AMFANI DA DAMARKA A LOKACINTA
Da yawanmu ba mu san mahimmancin lokaci ba, inda za ka lura da masu wasan tseren dauka-sauke za ka ga kowa nasara yake son ya ci, amma dole ya san me zai yi, kuma cikin minti nawa? Dole ya yi qoqarin kammala duk zagayennan a cikin 'yan mintocin da yake da su, in ba haka ba komai qoqarinsa a banza ne yake yi, ma'ana ya riga ya saki hanyan nasara kenan, a addini ma za ka ji ana cewa yi kaza kafin kaza ya same ka, shi ya sa a darussan baya muka ce 'yan siyasammu da za su yi shekaru qasa da hudu su sauka, me suka iya yi wa jama'a wanda zai lamunta musu dawowarsu?
.
In kuma wadanda dawowar da ma da wahala kamar kansiloli me suka yi wanda zai lamunta musu damar shiga takarar shugaban qaramar hukuma? In kuma mai koyon sana'ar hannu ne shekara nawa kake zaton za ka yi? Shin wadannan shekarun sun isheka ka gwanance? Ka fara samun wadanda in ka bar wannan wurin za su biyo ka duk inda kake saboda jin dadin aikinka? In ba haka ba ne to ka sake lissafi, kai za ka qiyasta lokacin da kake son ka yi, sai in asali dama yanayin sana'ar a qiyasce lokacinta yake, ko kuma sai maigidanka ya sallame ka.
.
Har da haka, kana da damar da za ka diba wa kanka shekarun da kake buqatar ka zama wani abu a fagen, yadda wasu masu buqatar aikin da kuke yi ba sa iya sakewa da kowa sai kai, mutumin da nasara ke gabansa zancen hutu kowani lokaci ba nasa ba ne gaskiya, shi ma yana cikin tsarin da ya diba wa kansa, lokacin aiki daga kaza suwa kaza, zumunta lokaci kaza, abokai lokaci kaza, in bai yi aure ba qila yana da lokaci kaza don wace zai aura, in kuma ya yi to iyalin nasa na buqatar lokaci kaza, sai an hada da haka don zomo ba ya kamuwa daga zaune, in dai ba za ka shigar da hutu lokacin aiki ba, to bai dace aiki ya riqa shiga lojacin hutu ba, tsari yana da amfani.
.
Mukan ce wane dan boko ne, amma za ka taras ya fi kowa jin dadin rayuwarsa saboda irin tsarin da ya yi, kasuwanci ko aikin ofis ko na masana'anta ko ma'aikata ko wata sana'ar hannu duk suna buqatar lokaci, in kana koyon aiki ka cire qyuya ko gani-gani, ka sanya haquri banda sauri, komai lokacinsa na zuwa.
3) ME KAKE HANGOWA? Ka ga dai sana'ar da kake yi za ka taka ka hango nasara, kai ka samo ta ka gina ta daidai tsawon da kake ganin za ta isheka, kai ka hango inda take kafin ka dauki hanyarta, bai dace ba a ce ka yarda wanda bai da irin wannan tsaunin da ka taka wai shi ne zai hango nasaraka ya gaya maka ga hanyar da za ka bi.
.
To in kuma shi ma ita yake nema fa? Ba laifi ka saurari mutum, amma ka san irin shawarar da yake ba ka, in mai kyau ce ka amsa in kuma ka san ba ta da kyau duk da haka ka biye musu ka saki hanyar da ka tabbatar da ingancinta a qarshe za ka fahimci cewa hanyar kwana ta yi da kai ta dawo da kai baya, kana buqatar hankali da natsuwa da jajurcewa da samun qarfin gwiwa, sai dai duk wayonka ka yi qoqarin tattaunawa da masu ruwa tsaki a cikin harkar, ko ka abokance su ka sanya ido a irin yadda suke gudanar da tafiyarsu.
.
4) Banda yanke qauna, ka yi zaton cewa wannan sana'ar ba za ta kawo maka abinda kake so ba, bayan ba ka jima da shiga ba, na ga wanda ya shiga soja, ko wata hudu kyawawa bai yi ba ya gudu, wai wahala kawai ake ci ga wasa da rayuwa, na ga wani tela da ya fara gwanancewa, shi ma ya watsar da sana'ar, ya raina abinda yake samu, kuma bai ajiye wata ba, na ga wace karantarwa take yi ta watsar da aikin wai ayyuka sun yi mata yawa, sai ta koma sana'ar da ba ta kai koyarwar daraja ba.
.
A kullum mutum ya sani cewa ba sana'arka ce nasarar ba, amma ita ce za ka taka wurin hango ta, iya bisanta iya inda za ka iya hangowa, sai ka san irin ginin da za ka yi mata, da kuma qarfinsa da bisansa, ka shirya kenan, amma in ka gaya wa kanka cewa tana da nisa ba za ka iya hango ta daganan ba, zai yi wuya ka yarda ka gina don ka san wahalar banza za ka yi, anan ka yanke qauna akan abinda ba ka tabbatar ba ya sa ka sha wahala a banza kenan.
5) Kar ka riqa nuna wa mutane fuskar rashin cin nasara a kullum, ba laifi ba ne in ka sha wahala ka gaya musu, kamar yadda ba na ganin duk dadi za ka sha sai ka kwashe ka gaya wa mutane.
.
Amma fa wadanda suke qarqashinaka su riqa sanin abinda kake ciki, ba wai ka gaya musu ba, su ji a jikinsu cewa tabbas an sami alkhairi, dan gutsura ka ba su don qarfafa gwiya, kai ka san irin abinda zai dace da su, kudi ne ko sutura da abinci, ko wasu kayan qyale-qyale? Da haka za su fahimce ka in ka yi musu bayanin halin qunci da kamfani ya shiga, don kana yi din in aka samu, in ba ka yi ba kowa zai san cewa tabbas ba ka samu din ne ba, ka yi qoqarin maida komai ga Allah, samu ko rashi, in ba haka ba wasu lokutan za ka yawaita samun sabani da jama'a.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```