SADUWA DA MACE TANA SHAYARWA YARONTA NONO


SADUWA DA MACE TANA SHAYARWA YARONTA NONO 

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum
mlm tambayata itace,mlm idan miji ya sadu da matarsa kuma tana shayarwa yaronta ya tashi a Bacci to mlm sai tayi wanka data bashi nono ko zata iya bashi haka,sannan kuma wani lokaci idan tana bashi nonon mijin yana amfani da gabanta ta baya hakan babu matsala.Allah ya sakawa mlm da alkhairi.

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

 Al-imamul A'imma Maliku Ibn Anas Yace, Bai Kamata ga Mace ta shayar da danta Nono Alhalin Akwai Janaba a Jikinta ba. Sabida Wannan yaron zai sha Wannan Nonon Nata tare da Shaidani. Shaidani yana Kusantar Mutumin da yake da Janaba a Jikinsa. Wanda kuma idan Shaidan ya sha Wani Abu Ko ya Ci Wani Abu tare da Mutum, Zai cutar da shi. Musamman Yaro. Shiyasa Manzon Allah saw Yace idan dayanku zai Ci Abinci yayi Bismillah a farkon Farawarsa, idan ya manta Baiyi Bismillah a Farcin Laumarsa ba, to ko da a ta Karshe ne ya yi Bismillah. Sakamakon Rashin Yin Bismillah, yana Ci da Shaidani. Idan Yayi Bismillahi. Wannan Shaidanin zai Amayar da Abinda ya ci tare da Wannan Mutumin da Baiyi Bismillah a karon farko wajen cin Abinci sa ba. Ko dai yaron nan ya Hadu da wata Jinya, ko kuma ya dabi'antu da Dabi'u irin Na Kangarewar Shaidani da Sauransu.
 Sabida haka Kenan sai dai tayi Wanka Ko tayi Alwala kafin ta shayar da wannan yaron.
  Zama Da Janaba haka Kawai ba shi da Amfani. Amma dai ba Lefi bane a shari'ah Mutum ya dan Zauna da Janaba kafin ya samu yayi Wanka na dan Wani Lokaci.
 Sabida wani Lokaci Manzon Allah saw Ya Hadu da Abdurrahman Ibn Sakarin Addausiy Al-yamaniy, shine Abihuraira a wata hanya. Sai Abu Huraira bai zo ya gaisa da Manzon Allah saw ba. Ashe ya tafi ne yayi Wanka wanda a wannan Lokacin Akwai Janaba a jikinsa. Sai da ya dawo sai manzon Allah saw Yace ina ka shiga ya Abuhuraira? Sai Abuhuraira Yace, Akwai Janaba ne a Jikina, shine na kyamaci Gaisawa da kai ina Cikin halin janaba. Sai manzon Allah saw Yace SUBHANALLAH AE MUMINI BA YA ZAMA NAJASA.
  Duk da Cewar ManzonAllah saw ba ya gaisawa da Mutane, ba ya Maida Sallama kuma ba ya yiwa kowa sallah idan da janaba a jikinsa. Har sai yayi Wanka.
 Sannann Kuma Yana Cewa, Mala'iku ba sa Shiga Gidan da ya ke da Mai Janaba a Jikinsa.
  
Allah Shine Masani.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)