YADDA AKE KUNUN ALKAMA DA KUMA AMFANINSA GA JIKIN MACE



*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*



*_Yadda Ake Kunun Alkama Don Amfani A Jikin Mace Wajen Ni'ima Da Gyara Nono_*

Zaki nemi kaya hadi kamar haka;
* Alkama
* Gyada Markadadde
* Kayan kamshi
* Suga
* Nonon shanu ko madara peak
*Bayani;* Zaki kawo garin alkama da wanda ba’a nika ba sai ki wanke alkamarki ki sa a tukunya ki dora a wuta sai ki dauko gyadarki ki dama ki tace ki ajiye a gefe, sai ki duba idan ya yi sai ki sauke ki juye sannan ki dora ruwan gyada a wuta, idan ya tafasa sai ki dauko dafeffen alkamarki ki zuba ki barshi ya kara nuna, sai ki dama garin alkamarki kadan ki sa kayan kamshi, idan ya yi sai ki sauke ki zuba damammen garinki ki juya sosai, idan ya yi sai ki zuba suga da nono ki juya sosai ki sawa mai gida da yara.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*


*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a shiga ta wannan link din* 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/GqtP5PUubzCHPlL92GDFT1
Post a Comment (0)