KWAƊAITARWA WAJEN YIN SALLAR DARE



*MAKARANTAR AZUMI 015*//

📌 ```KWAƊAITARWA WAJEN YIN SALLAR DARE``` 

Manzon Allah Ya kasance Yana ƙwaɗaitar da Sahabban Sa gameda yin tsayuwar Ramadana, kuma ya kwaɗaitar da Al’umma gaba-ɗayan ta akan haka, saboda faɗar Sa a Hadisin Abu Hurairah (RA) yace: Manzon Allah ﷺ Ya ce: “ *Duk wanda yayi tsayuwar Ramadana yana mai Imani kuma yana mai neman Lada a wajen Allah, an gafarta masa abinda ya gabata na Zunuban sa* ”. [Bukhaariy da Muslim suka riwaito shi].

Don haka ya kamata ga mai Azumi yayi kwaɗayin yin Sallar Dare, kada ya bari wannan alkhairi ya kuɓuce masa, musamman a cikin wannan Watan akwai Daren Lailatul Kadri, kuma yafi watanni dubu alkhairi.

Kuma ita wannan Sallah, raka’o’in ta basa wuce raka’o’i goma sha-ɗaya, Annabi baya ƙarawa akan haka; saboda abunda Ummuna Aishah ta faɗa (RA) tace: *Manzon Allah (SAW) Ya kasance baya ƙara sama da Raka’a goma sha-ɗaya a Ramadan ko ba a Ramadana ba* . [Bukhaariy da Muslim suka riwaito shi].

Duk da yake ya halasta Mutum yayi ƙasa da hakan saboda aikin Manzon Allah (SAW) da ya aikata hakan, a yayin da yace: “ *Sallar Wutiri dai haƙƙi ce akan kowani Musulmi, duk wanda yake so yayi Wutiri da Raka’o’i biyar yana iya aikata hakan, kuma duk wanda yake so yayi Wutiri da Raka’o’i Uku yana iya aikata hakan, hakama wanda yake so yayi Wutiri da Raka’a daya ma yana iya aikata hakan* ”   [Abu Dawuda ne ya ruwaito shi daga Sahabi Abu Ayyub].

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)