HUKUNCIN WANDA YA KARYA AZUMI DA GANGAN



*MAKARANTAR AZUMI 014*//

📌 HUKUNCIN WANDA ```YA KARYA AZUMI DA GANGAN``` 

Wanda duk yaci abinci ko yasha abun sha ko yayi Jima’i da Rana tsaka da gangan ba da mantuwa ba, kuma ba rashin Lafiya ko Tafiya bace suka sashi ya karya Azumin ba, to akwai Zunubi mai girma akan shi, kamar yadda Hadisi yazo daga Abu Umamatal Baahiliy – Allah ya kara masa yarda – yace: na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “watarana ina cikin Bacci sai wadansu Mutane biyu suka zo waje na, suka kama damtse na, suka kai ni wani Dutse mai wuyar hawa, suka ce da ni hau, sai nace ba zan iya hawa ba, sai suka ce za mu taimaka maka, sai na hau, sai dana zo kan Dutsen sai naji waÉ—ansu sautuka masu tsananin Æ™ara. Sai nace: waÉ—annan sautukan fa? Sai suka ce wannan kukan Æ´an Wuta kenan, sannan aka tafi da Ni sai na ga waÉ—ansu Mutane da aka rataye su da jijiyoyin agarar su aka tsattsaga leÉ“an su, leÉ“an nasu suna ta zubar da jini, yace: sai nace: su wane ne waÉ—annan? Sai yace waÉ—annan sune waÉ—anda suke karya Azumin su”. [Hakim ya ruwaito shi kuma ingantacce ne].

Amma kuma an ruwaito wani Hadisi wai Annabi yace: “duk wanda ya karya Azumi a watarana daga cikin Ramadana da gangan to ko da zai yi Azumin shekara daya ne bazai isar mishi ba”.

To wannan Hadisi ne wanda yake mai rauni bai tabbata daga Manzon Allah (SAW) ba❗️

Wanda yayi Jima’i da gangan a rana tsaka, shi kadai ne ramuwa ta tabbata akanshi tare da Kaffara, amma wanda yaci abinci ko yasha abun sha to Azumin su ya karye kuma babu ramuwa akan su ballantana Kaffara, sai dai suji tsoron Allah su tuba tun anan duniya, idan ba haka ba to su sani akwai Azabar Allah mai tsanani da take jiran su a ranar Gobe Al-Kiyamah, Allah ya tsare mu, Amin.

✍ *ANNASIHA TV* 

Telegram 👇
https://t.me/AnnasihaTvChannel
Post a Comment (0)