*MAKARANTAR AZUMI 017* //
📌 _CIKA AZUMI ZUWA DARE_
Idan dare ya gabato daga ɓangaren Gabas kuma yini ya juya baya daga ɓangaren Yamma, sannan Rana ta fadi to sai mai Azumi yayi buɗa-baki, kamar yadda aka karɓo daga Umar Ibn Khaɗɗab – Allah ya ƙara mishi yarda – yace: Manzon Allah (SAW) Ya ce: “Idan Dare ya gabato daga nan (yayi nuni zuwa Gabas), Yini kuma ya juya baya daga nan (yayi nuni zuwa Yamma), kuma Rana ta faɗi, to haƙiƙa lokacin buɗa-baki ya yi”.
Wannan al’amari ne da yake tabbatuwa bayan faɗuwar wainar (kaskon) Rana kai-tsaye, koda kuwa ana ganin haskenta a zahiri, domin tabbas ya kasance daga cikin shiriyar Annabi (SAW) idan ya kasance yana Azumi, yana umurtar wani ya hau kan wani abu ya dubo masa faduwar rana, idan har yace Ranar ta fadi, sai Annabi yayi buɗa-baki.
Sai dai kuma an samu wasu Mutane suna tunanin cewa lallai Dare baya tabbatuwa da zarar Rana ta fadi, har sai bayan Duhu ya yadu a ko’ina Gabas da Yamma, irin haka ta taba faruwa ga wani Sahabin Annabi (SAW) sai aka fahimtar dashi cewa farkon duhu ta bangaren Gabas da zaran kaskon rana ya boye ya isa.
✍ *ANNASIHA TV*
