ME YASA MAZA BASA GANIN KYAN MATANSU?
Akwai wani mutum daya samu daya cikin mashahuran malaman musulunci km mai hikima yakai masa korafi kamar haka:
"A lokacin dana fara haduwa d matata y kasance itace abu mafi soyuwa km mafi kyawu a idona daga dukkan halittun ubangiji"
Yaci gaba da cewa "A lokacin d muka fara soyayya har muke shirin aure, sai n fara ganin wasu matan wadanda suka kaita a kyau"
Bayan km n aureta sai nake ganin mafiya yawan mata sun fita kyau.
Bayan mun dauki shekaru, sai nake ganin dukkan matan duniya *sun fita kyau, aji d km birgewa*"
Sai malamin yace "bana fada maka abinda yafi wannan d'aci b?
Sai mutumin yace "fadamin mana"
Malam: "Da ace xaka auri dukkan matan duniyan nan, toh d xakaga Kare wadda yake gararamba a titi sai kaji yafi birgeka akan su matan naka"
Mutumin: Meyasa kace haka malam?
Malam: "Saboda matsalar bata matarka bace, matukar mutum yanada budurwar xuciya, kuma yana yawan kallace kallace toh babu abinda xai wadaceshi face kasar kabarinsa. Matsalarka itace baka rintse idanuwanka daga kallon abinda Allah swa Y hana ka. Shin kanaso kaga matarka kyakkyawa kmr yadda kake ganinta kafin k aureta?
Mutumin: Eh inaso
Malam: Ka rintse ganinka sbd fadin Allah SWA "Km k fada muminai maza su saukar d idanunsu kasa, km su kare al'aurarsu. Wannan shi yafi tsarki a garesu, km Allah Shine mafi sani akan abinda suke aikatawa" Suratul Nur
Hakika yanada daga dabi'ar mutum: abinda b nasa b yafi 'Kayatar dashi, amma a lokacin daka samu abin sai kaga y tashi daga *something special* to *something ordinary*
K kasance mai godiya d km wadatar xuci daga abinda Allah Y baka. Bin dokokin Allah shine abinda yafi alkhairi. Sannan k dinga yawan addu'a akan *Allah Y sanya k dinga ganin kyanta, Y s k kaunaceta d km tausaya mata a koyaushe".
Copied and translated to Hausa from ISLAMICREMINDER