𝗠𝗨𝗧𝗨𝗪𝗔 Ƙ𝗔𝗗𝗗𝗔𝗥𝗔𝗥𝗥𝗘𝗡 𝗟𝗔𝗠𝗔𝗥𝗜 𝗡𝗘



𝗠𝗨𝗧𝗨𝗪𝗔 Ƙ𝗔𝗗𝗗𝗔𝗥𝗔𝗥𝗥𝗘𝗡 𝗟𝗔𝗠𝗔𝗥𝗜 𝗡𝗘.
-
"Zaka mutu, zan mutu, zata mutu, zai mutu, zasu mutu, kowa zai mutu yaje ya tarar da ubangijinsa Allah maɗaukakin sarki a ranar ƙiyamah"
-
"Wane irin kyakkyawan tanadi ka yiwa kanka wanda zaka amfane shi a ranar lahira ta hanyar kusancinka ga Allah? Kada ka yarda ka zamto daga cikin irin asararrun bayin nan da suke nesanta kansu daga ubangijinsu Allah a wannan duniyar"
-
"Ita mutuwa hukuncin ubangiji ne zartacce wanda babu mai iya kuɓuce mata, idan baka mutu yau ba, to tabbas gobe ko jibi zaka mutu, anyi al'umma da yawa a gabanin ka amma duk sun shuɗe, to haka wataran kaima zaka zamto tarihi ga ƴan bayan ka, wato kaima wataran zaka mutu kabar duniya, sabida haka ka kawar da dukkanin wani girman kai da jiji da kanka ka dawo kabi Allah, domin haƙiƙa gareshi kake komawa bayan mutuwarka"
-
Facebook page
https://mobile.facebook.com/Hausa-Islamic-Pictures-Quotes-304897013359792/?ref=opera_speed_dial_freefb
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
Post a Comment (0)