HALLAKAR MANYAN KAFIRAN MAKKAH
Imamul Bukhariy da Muslim da Abu Dawud da Nisa'iy sun ruwaito hadisi daga Sayyiduna Abdullahi 'dan Mas'ud (ra) yana cewa :
"Watarana Annabi ο·Ί yayi sujadah (a Harami kusa da dakin Ka'abah) sai tsinannen kafirin nan mai suna Uqbatu bn Abi Mu'ait ya dauko mahaifar raqumi ya jefa akan wuyan Annabi ο·Ί sannan ya koma gefe cikin sauran 'yan uwansa kafirai suna kallo suna ta dariya.
Annabi ο·Ί yaci gaba da sujadarsa bai cira kansa ba, har sai da Nana Fatimah tazo ta dauke masa, sannan ta wanke masa jikinsa Kuma tayi addu'a akan wadanda suka aikata masa wannan (amincin Allah da yardarsa su tabbata gareta da mahaifinta).
Annabi ο·Ί yana dago kansa daga sujadar sai yayi addu'a yace : "Ya Allah kayi mun maganin dattijan Quraishawan nan. Ya Allah gaka nan ga Abu jahal bn Hisham, da 'Utbatu bn Rabee'ah, da Shaibatu bn Rabee'ah, da Uqbatu bn Abi Mu'ayt, da Umayyah bn Khalaf, da Ubayyu bn Khalaf".
Acikin wata riwayar aka ce yayin da suka ji ya fara ambaton sunayensu acikin addu'arsa sai tsoro ya kamasu, sukayi tsit, suka dena dariyar.
Abdullahi bn Mas'ud yace "Wallahi duk sai da na gansu an karkashesu aranar yaqin badar, aka jefa gawarwakinsu acikin rijiyar nan ta badar. In banda Umayyatu da Ubayyu, (shi umayyatu akan hanyar komawa gida ya mutu) shi kuwa Ubayyu da shike Qato ne rugujeje, Kuma Takubban Sahabbai sunyi aiki sosai akansa, an fara janyo gawarsa kafin a kawo bakin ramin har gabobinsa sun wargaje.
Shi kuwa Uqbatu bn Abi Mu'ayt ahannu aka kamoshi, Sayyiduna Aliyu (ra) ya fille kansa agaban Manzon Allah ο·Ί.
- SAHIHUL BUKHARIY (hadisi na 3185)
- Sahihu Muslim (hadisi na 1794).
- Anwarul Muhammadiyyah.
Hakika Allah ya cika dukkan alkawarin da ya yiwa Annabinsa ο·Ί Kuma ya bashi gagarumar nasara akan makiyansa. Wadanda aka nufesu da alkhairi sun musulunta bayan an fafata dasu. Wadanda kuma kalmar hallaka ta tabbata akansu, Sun mace akarkashin kaifin takubban Sahabbansa ο·Ί.
Salati da amincin Allah su tabbata bisa Fiyayyen Annabawa da Manzanni, Mai babban ceto aranar babban taro, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya da dukkan Salihan bayin Allah har zuwa ranar sakamako.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (25/11/1442 05/07/2021)