Tambaya:
Wani ne sukayi soyayya da wata yarinya, hasali baidae Yi Zina da ita ba Amma sun rinka soyayya wadda ta saba ma shari'a, Karshe sun rabu, Shi ya Zama bawan Allah nagari, salihi, Amma ita daganan ta cigaba sosae yanzu haka yarinyar tazama karuwar gida, Shin ya zaiyi, shine ya Zama sanadiyyar fadawar ta ga hakan.
.
*Amsa:*
Bābu wani mutum da zai yi wa wani nuni zuwa ga wani aiki face sai ya samu kamasho na sakamakon wannan aiki duk lokacin da aka aikata.
Wanda ya lalata mace ya ďora ta a hanyar fasiqanci, har ya kasance ta saba da abin, to zai ci gaba da samun kamasho a duk lokacin da ta yi fasiqanci da wani, koda kuwa bayan ya mutu, domin shi ne ya yi sanadiya ko ya fara jefa ta a cikin wannan hali.
Zina tana da wahalar bari ga wanda ta ratsa ruhinsa. Shiyasa Aʟʟαн(ﷻ) Ya ce kada mu kusanci zina, domin Shi Mai ilimine a kan komai, Ya san cewa idan mun kusanci zina za mu iya afka mata, kuma barinta ya fi fara ta wahala. Allah ne Mafi sani.
Duk da cewa shi be aikata zina da ita ba, amma ai shi ne ya ďora ta a hanya, shi ya kusanto da ita zuwa ga zunubin, don haka ba zai tsira daga zunubin da take samu ba.
Tunda shi yanzu ya tuba ya gyara ayyukansa, wajibine ya same ta ya yi mata wa'azi. Kamar yadda be ji kunyar sa6a wa Allah tare da yarinyar ba, kada ya ji kunyar zuwa ya yi mata nasiha. Ya yi iya bakin 'kokarinsa wajen fahimtar da ita hatsarin abin da take aikatawa tare da azabar da Ubangiji Ya tanadar wa mazinata.
Idan ta ji tsoron Allah ta daina, to madalla. Idan kuma ba ta daina ba, Allah Ya ga zuciyarsa, sai ya ci gaba da istigfari da yawaita ayyukan alkhairai, tare da yin ayyuka masu gudana da za su amfanar da shi har bayan mutuwarsa. Tabbas Allah Mai yawan gafara ne.
Wallahu A'lamu.
.
*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*
Telegram: https://t.me/irshadulummah1