KASUWANCI NA GASKIYA



KASUWANCI NA GASKIYA

An ruwaito daga Hakeem bn Hizaam ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: "Masu cinikayya biyu suna da za6i matukar ba su rabu ba, ko ya ce: har sai sun rabu(idan suka gama kulla cinikayya har suka rabu to cinikayya ta riga ta kullu), idan su ka yi gaskiya suka bayyana(mai kaya ya yi bayanin gaskiya in ma kayan yana da wata illa ko aibu ya fada, shi ma mai siya ya siyeshi a kudin da ya dace da kayan) sai a sanya musu albarka a cikin kasuwancinsu, (shi mai siyarwa kudin suyi masa albarka, shi ma mai siya a sama abin da ya siya albarka) idan suka 6oye suka yi karya, sai a shafe albarka daga cinikinsu". 
Bukhary da Muslim 

Allah kabamu ikon halantacce kasuwanci. Ameen 🤲🏼


https://chat.whatsapp.com/IP2nTIEClBfGwdcRnXk9hS

@zauran salafiyyah abuja__
Post a Comment (0)