Sharhi akan film din "Mere Jeevan Saathi"..... Lifemate....Abokin Rayuwa..........
WhatsApp group Labaran Bollywood......
Admin....Ammar Haruna Muhammad......
Admin maman Fatee...hajiya Aisha....
Admin....Misbahu Ibrahim (RAWY)....
Admin.....Abdul Sham khan.....
Ina farawa da sunan ubangiji madaukakin sarki mai komai da kowa.....Allah ya dafa mana tare da gafara......zanyi sharhin film din " Mere Jeevan Saathi" amma bai zama lalai sharhin nawa ya tafi kamar yarda yazo a film ba.....dole zan mance wasu gurare a matsayina na Dan adam mai mantuwa.......don haka nake bada hakuri ga Wanda ya kalla baiga na saku wasu guraren ba...hakan ya faru bisa mantuwa.....sannan bazan yi amfanin da sunayensu na film ba zanyi amfani dana Asali ne.......
A farko.........................
Zaune take a cikin office nata tayi jigum ga dukkan alamu dai tayi nesa a cikin tunani.....
Karishma kapoor kenan wacce tayi nesa a kaunar wani matashi Wanda bai san tana yiba...
Mawakin Akhshye Kumar mawaki ne da yake tashe a wannan lokacin Wanda yake da masoya masu taren yawa...yaka samun masoya ne bayan fitar sabuwar wakarsa mai take...."Mere Jeevan Saathi "...Wanda ya wake abar kaunarsa (Amesha Patel)...Wanda sun jima a cikin kaunar juna kuma tana kara karfafa masa guiwa a ko wani lokacin....
Bayan ya kammala yin show ne ya fara samun Appointment daga manya company's akan zasu rika sayan wakokinsa....Wanda har ya amince da wani company jimma kadan kuma sai ya samun wata babban dama a wani shahararen company dake American akan zasu rika sayan wakokinsa....Wanda a wannan lokacin ya shirya domin tafiya can American Wanda da fara sam yake Aminta domin a tunaninsa yin hakan kamar can amanar wance company da ya karbi contract nasu ne....a dayan bangaren kuma baya son yayi nesa da abun kaunarsa Anjali(Amesha Patel)... Wanda iyayensa da ita budurwarsa suka dauki nauyin sasantawa da wadancan company na farko....
Bayan tafiyarsa American ne ya hadu da shugabar company ba wata bace face....Natasha...(Karishma kapoor) ya samun karramawa sosai Wanda har yayi mamaki ganin pictures NASA a office din ita Natasha... Wanda har yakai ga tambayarta ita kuma ta labarta masa ai ita tana daga cikin fans NASA tana jin dadin wakokinsa...Wanda a take ya nuna jin dadinsa......
Bayan ya samun Hutu ne ta aikon masa da sakon. Zasu fita zuwan wajen taro.....Wanda a lokacin da suke tafiya a jirgi ne Anjali ta kirasa a waya Wanda a lokacin yake bata hakuri tare da uzurin da yasa bayan isarsa American bai kirata ba....inda ta nuna masa babu komai....Wanda har ya bukaci akan su gaisa da shugabarsa...Natasha Wanda ya baiyana mata ai ga budurwarsa su gaisa....Wanda a take fuskar Natasha ya canja....sun gaisa ba tare da ranta yaso ba inda tayi ta amsa gaisuwar bacin rai....Wanda ita kuma anjali sai nuna farin ciki take da haduwa da ita Natasha.......
Can bangaren Anjali kuma mahaifiyarta ta nuna mata ita fa tana tsoron anya har zasu iya yin aure da Rohit....saboda a yanzo ya zama superstar shi kuma superstar zaiyi ta haduwa da yan mata kalala Wanda har ta nuna tsoron kar ya guje ma diyarta inda ita kuma Anjali ta nuna ai babu komai tasan Rohit bazai guje mata ba...domin babu cin Amana a tsakaninsu......
A kwana a tashi Natasha ta fara nuna ma Rohit irin son da take masa...Wanda shi kuma sai sai yayi kamar mai bai san tanayi ba.....Wanda wata rana ta bukaci daya zo ya tayata murnar zagayowan ranar haihuwarta.....bayan yazo ne sukayi farin ciki sosai....wanda ita Natasha tayi ta kissa tare da salo har dai taja hankalinsa wanda har shaidan ya kawu musu ziyara suka aikata masha'a....
Wanda bayan faruwan hakan ne Rohit yayi matukar nadama da bakin cikin abunda ya gudana a Daren jiya....wanda a tunaninsa ai yaci amanar Anjali.....
Wanda ita kuma Natasha sai ma farin ciki tayi da abun da ya faru....wanda har take ikararen bata taba samun farin ciki ba kamar na Daren jiya......wanda a lokacin ya bata hakuri akan kuskuren da ya faru a Daren jiya....ita kuma sai ta nuna ai hakan ba komai bane sai ma matakin soyayya har take baiyana masa ai ta jima tana kaunarsa....shi kuma a take ya baiyana mata ai yana da wacce yayi ma Alkawarin aure.....
Daga nan ne matsaloli sukayi ta faruwa tsakaninsa da Natasha wanda ta dage sai ya sota....shi kuma yaki.....
Bayan lokacin komowarsa India tayi ne....ya sanarda ita inda itama ta nuna lalai sai ta bisa....domin a can ma.zata bude babban company domin ta kara daukaka stardom NASA....wanda badon yaso ba ta biyosa....Wanda ya bayan sun sauka a India ne ta hadu da anjali wanda anjali tayi farin ciki ganin Natasha har take cewa.... "Muryar ki akwai dadi.... Amma dai kyawunki mai yawa ne da daukar hankali...." Wanda a take ita Natasha tace" ai duk mace da tasan ita mai kyau ce da aji ba ta yabon kyawun wata mace yar uwarta"....wanda maganar ta ba anjali da Rohit mamaki har anjali take cewa" kamar ya? Bangane ba....
Sai Natasha tace " inji masu hikima" ta fada fuskarta a daure... Wanda take anjali da Rohit sukayi murmushi naji wata hikima anan......
Toh fa daga nan ne Natasha ta konna wuta kan sai ta raba Rohit da Anjali....wanda ta sanya Rohit yana ta karyar Alkawarin da ya dauka ma Anjali akan zasu fita tare ko kuma zasuyi dining tare....wanda sai ta bukaci daya zo gidanta shi kuma sai yaki wanda har kiran Anjali take ita kuma anjali sai ta tursasa Rohit tare da roko akan yaje har take ce masa" karka manta Natasha bakowarmun ce bai kamata kana mata haka ba...karka manta ita tayi sanadin daukakarka har wakarka ta zagaye duniya...ka girmamata don mu ta dawo India " da kalamai makamanta hakan take sa Rohit yaje gidan Natasha.......,
Can bangaren Natasha kuma tana yawan samun matsala da ma'aikatan company dinta domin a cewarsu tana kashe masu riba na yarda take sayar da casete na wakar Rohit da sauki maimakon da tsada yarda zasu sami riba sosai ..wanda ita kuma ta nuna masu ita ba ruwanta da wata riba burinta kawai kowa ya saya wakar Rohit ya zama anji wakar sosai ta zauna kuma a zukatan jama'a burinta Rohit ya daukaka koda zata talauce bata damu ba.....
Toh bayan Rohit yaje gidan Natasha ne ta nemi da lalai shima ya nuna mata soyayya wanda a take ya fara fada mata shifa ya gaji da abun da takeyi masa shi bazai taba kaunarta ba....kawai dai yana girmamata ne amma babu zance soyayya....wanda ita kuma har ta bukaci lalai ya zama dole ya rabuda Anjali yaso ta ita kadai....shima ya dage lalai baya kaunarta yana girmamata ne kawai..... Wanda bayan magana tayi zafi ne Rohit yace....ta fita a rayuwarsa shi ya hakura ma da neman daukakar ta barsa yayi rayuwa mai kyau da Anjali Wanda har takai da ya Turo Natasha akan kujera.....Wanda abun ya mata zafi.....cikin bacin rai take cewa....dole ya sota ko yana so ko baya so.....Wanda a take yace mata shi yi soyayya da ita ba....in ta yarda dai zasu iya zama abokai....Wanda bayan taki yarda ne ya bukaci da ta fita a rayuwar sa kuma ta manta dashi kawai....ita kuma tace har abada bazata daina kaunarsa ba kuma bazata manta dashi ba....Wanda a lokacin ta basa labarin cewa tun. Suna makatantar secondary take kaunarsa tare da sauraron wakokinsa Wanda a lokacin in yayi waka a makaranta jar jefansa akeyi da takalmi...ita kuma tana jin zafin haka wanda har ta dauki aniyar taimakonsa tare da baiyana masa yarda yake kaunarsa da begensa......Wanda a lokacin da take shirin fada masa tana kaunarsa ne ta sami labarin mahaifinta yayi hatsari ya mota....Wanda tayi bakin cikin matuka domin mahaifinta shine komai NATA...wanda tilas ta sanya ta koma American da zama domin kula da company's na mahaifinta Wanda ya zama NATA tare da aniyar daukaka Rohit a duniya.....
Bayan ta gama basa labari ne shi kuma yanuna mata sam hakan bai damesa ba....shi dai kawai bazai iya soyayya da ita ba.....wanda a take tace masa inda kuwa bazai aureta ba tabbas itama Anjali bazata aureshi ba kuma sai tayi abunda bazai taba mantawa da ita ba.....
Bayan wucewar lokacin ne, da dare ta tafi gidansu...Anjali bayan anjali ta bude mata kofa ne...ta shiga har take ma Anjali wani tambaya mai ban mamaki take ce mata shin "Kina kaunar Rohit sosai?" Cikin mamaki Anjali tace "ehh amma mai yasa zaki min wannnan tambayar?"... Cikin daurewar fuska da fusata Natasha tace" nima INA matukar kaunarsa kuma na Dade INA kaunarsa.... Don haka yau zan kashe ki tunda ya Nuna ke yake kauna bani ba" wanda a take ta cika mata wako a ciki....."... 🤔🤔🤔🤔🤔(wajen dai kaman tunani ne don akwai mamaki an nuna ta kashe anjali amma a cigaban film din sai a nuna kamar babu abunda ya faru ma da anjali....Don haka mu dauki gun a matsayin tunani🤔🤔🤔🙏),
Toh a dayan bangaren kuma dama company da suka fara ba Rohit contract har ya dawo masundashi abun ya masu zafi inda suka dauki aniyar ganin bayansa......wanda har suka sami Natasha akan ta taimaka masu su kashe Rohit tunda ya nuna baya kaunarta. Ita kuma sai ta amince...da hakan don haka suka shirya sanya masa bom a kasannmoto....haka kuwa ayi suka sanya masa bom a mota bayan yaje wajen yin training wanda a gun ma yayi ta tunani maganar da Natasha ta fada masa....bayan ya shiga motor ne sai su makiyansa suka kiransa suna fada masa cewa yanzo zai bar duniya wanda romot na hannunsu na tada bom din haka kuwa ayi suka tayar da bom din wani abun mamaki ashe bom din a kasar motarsu Natasha ta sanya....bayan ya tashi ne Rohit yayi mamaki kwarai wanda a take Natasha ta kira take shaida masa ita ta kashesu da bom.din har take ce masa ai babu abunda zai sanya ta kashe masoyinta kuma sai ta kashe makiyansa gaba daya.....hakan dai abubuwasu sukayi ta faruwa......wanda har wata rana Natasha ta yanka hannunta kan soyayyar Rohit wanda ya kaita asibiti kuma a ranar yayi ma Anjali akan zasu hadu....wanda bayan ya kai Natasha asibiti ne yaje gunta wanda har ya samu ta fara yin barci.....anan ya bata uzurinsa ta nuna masa babu komai.........
Kumin afwan zan cigaba zuwa anjima......🙏🙏🙏🙏 banda lokacin ....amma yayi kuji sharhi fatan zakuyi hakuri da yanayin sharhi kasancewa na farko farko....daga Ammar haruna Muhammad🙏🙏🙏🙏na gode sai naji daga gareku mai zaku iya cewa game da film din Mere Jeevan Saathi
......