TANA DA AURE AMMA TANA SON WANI



TAMBAYA
=========
👇
Mlm inada tambaya
Menene hukuncin macen da takeda aure Amman ta kasance cikin so da kaunana wani mutum na daban,shi wannan bawan Allah da ya nemeta sai Allah baiyi Aurensuba
Amman daga Baya taji shine take so da kauna na har abada,ta gagara control din kanta akan haka
Kuma tana gudun fadawa cikin fishin Allah akan haka
Kuma ta kasance bata amincewa da mijinta,saka makon yawan sabani a tsakani,kuma inhar tanason taji dadi saita ga hoton shi wancan din
Toh Mlm acikin wannan wali in ta nemi mijinta ya saketa saboda batason taci amanan shi ko gudun cutar dashi tayi kuskure koko?
Ngd.

AMSA
=====
👇
Shi SO Halitta ne. Kamar yadda Allah ya Ambata Mana a cikin Alqur'ani Mai Girma a wurare Mabanbanta.
 Inda zaka Tabbatar da Cewar So Halitta ne. Bai Kamata Mace take son wanda baya sonta ba. Haka bai Kamata Namiji Yana Son Wadda bata son Shi ba. Amma sabida Halitta ne ba yadda zaiyi.
 Haka zalika. Sabida Shi So Halitta Ne Yana Iya shiga Tsakanin Wa da kanwarsa ko da yayarsa ko da wata Matar da Babu Aure a Tsakanin su. Duk da Cewar sai dai ka Danne Abin a Zuciyarka. Ba zai Yiwu Ka Bayyana Ba. Sabida Ba zai Yiwu ba.
  Sabida So Halitta ne. Yakan Shiga Tsakanin Matar Aure da wanda ba Matar Aure ba. Duk da cewar ba Gaya Masa zatayi cewar tana son shi ba. Sai dai ta danne Abin a Zuciyarsa. Sabida babu yadda zatayi. Haka zalika shima sai dai ya danne idan har yana son wata Matar Auren. Domin shi ya san ba yadda zaiyi da wannan soyayyar. Kasancewarta matar wani. Haka Itama ba yadda Zatayi da wannan soyayyar da take yiwa wani din. Kasancewarta na Matar Wani.
 Kinga kenan. Duk da Kina son Wani a Ranki. Kuma Allah bai Kaddara Mijinki bane. Dole zakiyi Hakuri. Ki Rike wanda Allah ya Kaddara Aurenki da shi. Kiyi masa Biyayya Domin samun Aljannarki. Sabida Rashin Yimasa Biyayya Wai Don Soyayyar wani. Alhalin kuma ba Auren Kiyayya Kukayi ba. Wannan Rashin Yimasa biyayyar Zai Iya gadar Miki da shiga Cikin Wuta. Kuma ba Mamaki Idan Kin Fito daga Gidan wannan da yake son ki, da kuke Tare din. Wanda ba kyau son shi din. Ba Lalle Bane Wannan da kike Nacin Son shu ya Aurenki ba. Sabida idan Allah bai Kaddara akwai Aure a Tsananin ki da shi ba. Babu yadda zakiyi. Har Ku bar Duniya Ba za Kuyi Aure ba.
 Sabida haka, Shawara ta Anan shine. Tinda wannan din da kike tare da shi a Matsayin Mijinki, Uban 'yayanki, Tinda ba wani Mummunan Abu yake Yimiki ba. Ki Hakurtar sa Zuciyarki. Ki yiwa Mijinki biyayya. Kiyi Addu'ar Allah ya kawo Muku Yara Na Gari.
 Domin fitowarki daga Gidan Wannan da yake tare da ke. Zaki Iya Samun Jarrabawar Ubangiji. Sabida Allah yana Ganin Yayi miji Ni'ima. Amma kuma Kin Rena. Wannan zai sa Ki sami Jarrabawar da zaki Jefa Kanki Cikin damuwa da Nadama da Dana Sani.
  Sabida Haka dai Ki ci gaba da Addu'ar Allah ya kawo Muku zaman Lafiya Mai Dorewa. Idan Kuma Aurenki dashi babu Alkairi. Allah ya Chanja Miki Shi wannan din.
 Amma dai Sai Muna Hakurtar da zuciyoyin mu da kuma Addu'a Akan Allah ya zaba Mana Abinda Shine Yafi Zama Alkairi a Rayuwar Mu. Sannan zamu ke yin Wadannan Addu'o'i ne tin kafin Muyi Auren. Idan Kuma Munyi Addu'a kuma Munyi Auren, to fa wannan shine Alkairi a gare Mu. Bq abinda zuciyarmu take so ba.
 Sabida Fadin Allah Madaukakin Sarki da yake cewar. DA SANNU ZAKU KE SON WANI ABU, ALHALIN KUMA BA ALKAIRI BANE A GARE KU, SANNAN DA SANNU ZAKU KE KI KO KYAMATAR WANI ABU, ALHALIN KUMA SHINE ALKAIRI A GARE KU.
 Sabida haka Mu Kiyaye. Sabida Gudun Da Na Sani a Rayuwar Mu.
  
Allah Shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797
Post a Comment (0)