ANNABI DA SAHABBANSA // 008 .



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

         ANNABI DA SAHABBANSA // 008
.
_Ko Ka San Waye Abdulmuttalib? To Shi Ne Dai Wancan Shaiban Da Muka Ce An Haife Shi A Madina, Da Ma Tuni An Miqa Ragamar Kula Da Dakin Allah Da Kuma Mahajjata A Hannun Dan Uwansa Wato Muttalib Bn Hashim Bn Abdi-manaf, Shi Muttalib Babban Mutum Ne Kuma Karimi, Mutane Ma Kiransa Suke Da Kyauta, Yayin Da Shaiba Ya Kawo Qarfi Sai Muttalib Ya Sami Labarinsa, Ya Kuwa Fita Nemansa Allah Ya Yi Masa Gam-da-katar Ya Sadu Da Shi._
.
_Haka Dai Ya Rungume Shi Ya Yi Ta Kuka, Kuma Ya Nemi Ya Bi Shi Su Koma Makka, Shaiba Ya Qi Wai Sai Ya Nemi Izinin Mamansa, Ita Kuma Ta Nuna Sam Ba Za Ta Ba Da Hadin Kai Ba, Amma Da Muttalib Ya Yi Mata Bayanin Cewa Zai Je Ga Mulkin Tsohonsa Ne, Ya Riqe Dakin Allah Mai Girma Sai Ta Yarda, Ya Goyo Qaninsa A Bayan Raqumi Har Makka, Ko Da Mutane Suka Gan Shi Da Wani Mutum A Baya Sai Suka Zaci Bawansa Ne, Amma Karamcinsa Da Sauqin Halinsa Suka Sa Ya Goyo Shi, Shi Kuma Yana Cewa Ba Bawa Na Ba Ne, Qanina Ne Dan Hashim, Amma Sunan Ya Bi Shi Abdulmuttalib._
.
_Haka Aka Ci Gaba Da Kiransa Abdulmuttalib Har Shi Yayan Nasa Muttalib Ya Rasu, Qaninsa Abdulmuttalib Ya Zarce Da Shugabanci, Sai Dai Hakan Ba Ta Faru Ba Sai Da Naufal Ya Yi Qoqarin Qwace Shugabancin Tukun Daga Hannun Abdulmuttalib, Sai Ya Nemi Quraishawa Su Sa Hannu Amma Suka Yi Qemadagas Suka Ce Ba Ruwansu, Shi Da Baffansa Ne Su Qarata Can._
.
_Wannan Ya Sa Abdulmuttalib Ya Nemi Taimakon Kawunnansa Daga Madina Wato Banul Najjar, Sai Kawunsa Abu Sa'ad Bn Adiy Ya Surfafo Makka, Abdulmuttalib Ya Tarbe Su A Abtah Ya Nemi Su Wace Masauki, Amma Abu Sa'ad Ya Qi Ya Wuce Wurin Naufal A Sannan Yana Tare Da Quraishawa, Naufal Fa Ya Ji Yaqi Za A Yi Sai Ya Ba Da Mulkin, Daga Nan Ne Abu Sa'ad Ya Yi Umura Ya Zauna A Wurin Abdulmuttalib Na Tsawon Kwana 3 Ya Koma Madina._
.
_Dalilin Hadin Gwiwar Khuza'a Da Banu Hashim Wanda Za Mu Ambato A Fathu Makka In Sha Allah Shi Ne, Wannan Abin Da Ya Faru Ya Sa Naufal Ya Yi Hadin Gwiwa Da Banu Abdisshams Kan Banu Hashim, To Da Khuza'a Suka Ga Taimakon Da Banun Najjar Suka Yi Wa Abdulmuttalib Sai Suka Ce "Ai Mu Ma Dammu Ne" Daga Nan Suka Mara Wa Banu Hashim._
.
_Akwai Abubuwa Guda Biyu Da Za A Iya Cewa Sun Gudana A Lokacin Abdulmuttalib Na Farko Dai Sake Gina Rijiyar Zamzam Da Jurhum Suka Turbude Wasu Kayayyaki A Ciki, Tabbas Ya Tono Rijiyar Kuma Ya Hankatso Kayayyakin, Daga Ciki Akwai Takubba, Da Sulkoki Da Wasu Kayan Alatu Na Zinare, Sai Dai Kuma Quraishawa Sun Nemi Ya Raba Aikin Da Su, Da Bai Yi Ba Sai Suka Kai Qararsa Wurin Manyan Banu Sa'ad, Har Dai A Qarshe Suka Gamsu Da Cewa Tabbas Shi Din Ne Ya Kebanta Da Rijiyar, Wannan Ya Sa Ya Yi Alwashin In Ya Sami 'ya'ya Goma Zai Yi Hadaya Da Na Goman._
.
_Na Biyu Kuma Abrahata Dake Yaman Ya Fahimci Cewa Larabawan Dake Wani Babban Coci A San'a Suna Zuwa Aikin Hajji, Sai Ya Yi Qoqarin Ya Hana Su, Ya Tsayar Da Su A Nan, Da Wani Balaraben Kinana Ya Ji Sai Ya Yi Sakko Ya Shafe Gaban Cocin Da Kashi, Wannan Ya Sa Abrahta Ya Fusata, Ya Dibi Sojoji Kusan Dubu Sittin Gami Da Giwaye Tara Zuwa 13 Ya Nufi Makka, Haka Ya Yi Zango A Hanya Ya Dada Gyara Sojojinsa Ya Yi Shiri Na Gaskiya._
.
_Lokacin Da Ya Qariso Muhassar, Wani Babban Wuri Ne A Tsakanin Muzdalifa Da Mina, Nan Ne Giwayen Duk Suka Guggurfana Suka Kasa Yin Gaba, In Dai Za A Yi Kudu Ko Arewa Ko Gabas Suna Iya Zuwa A Guje Kuwa, Amma Yamma Inda Dakin Allah Yake Sun Kafe Sun Qi, Har Dai Allah Sw Ya Turo Musu Tsintsaye Suka Yi Ta Jifansu Da Tsakwankwanin Wuta Kamar Yadda Muka Gani A Suratul Fil, Su Kuwa Quraishawa Dama Can Sun Fita Sun Bar Wa Rundunar Wurin, Sai Da Allah Sw Ya Yi Ikonsa Sannan Suka Dawo._

_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
Post a Comment (0)